← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 158

Sashe 30

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Qulululu cikinta ya bada sauti tareda murdawa kamar zawo ze kece mata taji lokacin da tayi Arba da yar jaririyar da ke kwance idanunta na qaqqafewa kamar me suma ga qirjinta na sama da qasa da sauri har wani wahalallen tari take saki a shaqe ba’a maji sosai Amirah na gefenta tuni Goggoro yayi ta kansa kwalliya ta jagale tana rusar kuka hannu aka.

Habiba Kishiyar Addah ce tayi qarfin halin cewa a dauki yarinyar a kai Asibiti mana se a sannan ma tunanin su ya kawo nan da nan Ummi ta shiga kiran wayar Naziru tunda shine wakilin Bashir din amma se aka ce mata call waiting, bata haqura ba taci gaba da kiran wayar amma be daga ba.

LAGOS Nigeria
Wato ranar bayan Bashir ya tashi daga aiki se yabi wani abokinsa gidan sa saboda koya dawo gidan baya masa dadi. Suna zaune suna cin abincin da sukayiwo take away a hanya dan shi abokin bashi da Aure suna yan hirarrakinsu. Bayan sun gama Bashir ya dauki remote yana chanza tasha kafin lokacin sallar Magriba yayi su fita shikuma abokin wayarsa ya dauka ya shiga Tiktok dan shi ma’abocin duba Tiktok ne.

Bashir na daga gefe lokaci lokaci ya daga kai ya kalleshi jin yanda yake dariya shikadai, sedai ya girgiza kai kawai yana mamaki besan me mutane suke ji ko gani a wannan Tiktok dinba. Yana yawan ganin Abokanan sa suna shiga suyi kallace kallacensu har Ma’u ma yana ganin tana shiga ta kalli video Girke Girke amma shi a shirme yake daukansa. Dukda sunce akwai abubuwan amfani amma gani yake rashin Amfanin yafi amfanin yawa ai.

“Mata da bidi’a abarsu kawai yanzu suna ma ya zama biki kenan ji wannan ai wallahi bama ko wanne biki ba” Abokin Bashir din Musa ya fada yana nunawa Bashir video bayan yayi joining Live din da wata friend dinsa takeyi. Kallo daya Bashir yayi musu “yace Allah ya sawwaqa” ganin mata nata tiqar rawa abinsu.

“Masha Allah amma mejegon tayi kyau nima fa mutumina Gomben nan zanzo ka bani wata yar fara haka na aura wallahi” Musa ya sake fada. Haka kawai se ya samu kansa da juyawa ya sake kallon wayar karaf idonsa ya sauka kan mejego Amirah tana kwaso shoki.

Murza idonsa ya sakeyi dan ya tabbatar ita dince ko kama ce ya miqa hannu ya karbi wayar daga hannun musan daidai Live Video ya katse.

“Musa bude mun page din yarinyar nan na gani” Bashir din ya fada. Se Musa ya saka dariya yana cewa
“Kai mutumina biyu ne fa dakai tsalatsala ka barmu dai mu zero mu nema amma banda kai” ya qarasa yana miqa masa bayan ya budo masa page din Nabila Dikko qawar Amirah.

Videon farko da tayi uploading kadai ya kalla ransa yai qololuwar baci, videon da aka mata ne bayan an gama mata makeup da Baby Iman a hannunta. Wayar ya miqawa Musan kawai ya zaro tasa Musa kuma ya bishi da ido ganin yanda fuskarsa ta nuna bacin rai qarara.

Number Naziru ya kira ringing biyu ya daga.
“Naziru me yake faruwa a gidan nan?” Ya tambayeshi. Naziru da daman yake shirin kiran Yayan nasa dan dawowarsa daga makaranta kenan Dada take gaya masa ana can ana taron sunan, ze kira Bashir din kuma ta hana dan haka ya karkace ya fara jero masa yanda akayi

“Wallahi yaya taron suna sukeyi gida ya cika da mata harda me kida suka dakko tun daga Kano wai Feli sunansa kowa nadai manta sunacan dai sunayi wallahi ga sanyi ya kankama a Gombe kuma.....”

“Kanaji ko, kaje gidan ka kulle qofar ta waje kayi tafiyarka kawai kabarsu” Bashir din ya katse Naziru jin zancen nasa yaqi qarewa.
“Yes” Nazirun ya fada ransa qal dan dama yasan Indai Bashir ne ya san takan Tsiya aikuwa Kwado ze siyo qundumeme ya garqame su kuma baze bude ba se irin sha biyun daren nan gobe ma su sake zuwa suna.

Be fadawa Dada yanda sukayi ba haka be bi takan Kiran da Ummi takeyi masa ba dan daidai lokacin ne suna waya Bashir. Machine ya hau dan yafi sauri bayan ya siyi garqamemen kwadonsa kamar me kulle kurkuku ya nufi gidan.

A gidan suna kuwa bangaren su Ma’u sun sha hirarsu sosai har Magrib sannan driver Zahra yazo, sallama sukayi kamar karsu rabu Sannan Ma’u da Rahma suka rakota kallon matan da sukayi cirko cirko a tsakar gidan sukayi dan duk budirin nan basu san me yake faruwa ba suna sama abinsu kuma da yake sun rufe windows yasa basa jin qarar kidan sosai koda aka kashe ma abun be dame su ba.

Rabawa sukayi suka nufi Get dan bama wanda hankalin yakai kansu Asma’u ta saka key din hannunta ta budewa Zahra a ranta tana mamakin ganin an garqame qofa harda kwado Zahra na saka qafarta waje Naziru na dira ai harda gudu ya hado har yana tsorata su Zahra tayi Waje Ma’u tai ciki da sauri ganin yana neman datse mata hannu abinda ya ankarar da matan dake tsaye kenan suka yo Get din da gudu amma ina kafin suzo tuni ya danna Kwado ya bame.

Baki bude Rahma da Ma’u suke kallonsu,
“Kiyiwa Allah Hajia ki bude mana mu tafi dare yanayi haka kawai an kullemu kamar wasu barayi” wata mata ta fada. Kiran sunan Naziru Ma’u ta shigayi gaba daya kanta ya kulle se ya amsa mata yana cewa

“Anty kije kawai zan kiraki a waya in miki bayani”. Seta juya ita da Rahma sunajin matan wasu na magiyar a bude wasu na zage zage.

A palourn qasan suka zauna ta dannawa Naziru kira.

“Baba Naziru wai ya akayi ne meya faru aka garqame mana gida” ta tambayeshi bayan ya daga wayar. Seda yai dariya san ransa dannan yace

“Wallahi Anty ina zaune Yaya ya kirani yace na siyi kwado nazo na kulle gidan nan da duk jama’ar ciki inyi tafiyata ze kirani sanda ya kamata nazo na bude”.

“Ikon Allah, me akayi toh” ta tambayeshi.
“Oho inaga dai daman besan da zasuyi taron nan ba shine dalili qilan” cewar Nazirun.

“Toh Allah ya rufa asiri nidai yayana suna waje daman yanzu nake shirin naje na dakko su tunda gaka taimaka ai kasan gidan Su Qawar Amna Amina ka debo munsu”

“Ba case Anty Bari naje” sukayi sallama ta ajiye wayar.

“Kinji me gidan ne yace a kulle masa gidansa” Ma’u ta gayawa Rahma.

“Amma naji dadi dan fa sanda Abban Ilham ya kawoni yaga taron nan tambayata yakeyi meya faru nace nima ban sani ba nadai yi hasashen suna ake, yace aikuwa dakyar idan yaya bashir ya sani toh Allah dai yasa atashi lafiya nace Amin
Yanzu kuwa naga alamar kamar ba lafiya ba dan banga iyayen bikin ba a gurin”.

“Koma meye susuka sani dai, muje muyi Isha naji an fara kira” Asma’u ta fada suka miqe suka shiga dakinta na qasa dan yin sallar.

Dakin Mejego kuwa kiran duniya Naziru be dauki waya ba haka suka tasa ya a gaba suna kuka ita se qaqqafewa take Su kuma suna aukij kuka Amirah kamar itama zata shide babu wanda fasahar kaita wani Asibitin tazo masa a cikinsu.

“Ina Fatun, wallahi tun da sauran mutunta juna tsakaninmu kizo ki bude mu mu fita idan ba haka ba wallahi bazaki so abinda zan aikata a gidan nan ba” Hajia Mariya datafi kowa shiga tashin hankali dan kamar Mijin na jira ta gane an sace mota se gashi ya kirata akan yana Airport za’azo a karbi key din motar a dakko shi, seda wanda ya tura yaje aka ce masa bata nan ya kirashi gashi yanzu se kiranta yake yana Zazzage mata kwandon rashin mutunchi yace ta kuma tattaro dik inda take karya rigata zuwa gida in ma ita bata dawo ba to motarsa ta rigashi isa.

Qaqawara qaqa 🤔🤔🤔🤔🤔🤔

Ayi qara haquri dai yanayin se a hankali 🙏🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 19

Tunda Bashir ya qulla tsiya ya kuma tabbatar Naziru ya kulle gidan dan sun sake yin waya ya gaya masa ya je dakko su Amna a gidan qawarsu a sannan ce masa yayi ya wuce ya kaisu gidan Bilkisu yayar Asma’u kawai dan idan yace gidan Dada zata zargi wani abu kuma baya so labarin ya isar mata da wuri.

kashe wayarsa yayi dan karma wani dayake ganin mutunchi ya kirashi ya roqeshi. Beko qara minti goma a gidan Musa ba ya tafi yana tuqi a ransa yana wassafa irin hukuncin da ze dauka akan Amirah tunda har ta take dokarsa ta nuna bata jin maganarsa tabbas ze nuna mata shima ba kanwar lasa bane.

Daya isa gida shikadai ya ringa safa da marwa a cikin palour yana kwafa tabbas se ya hukunta yarinyar nan hukunci me tsanani, tunanin halinda Baby Iman take ciki yake yana fatan Allah yasa yarinyar tana lafiya wani abu be sameta ba hakan ze dan rangwanta wa Amirah hukuncin da zeyi mata amma ya rantse tabbas wani abu ya sami yarinyar nan se kansa besan me ze mata ba. Yana so ya kira Ma’u amma bayaso ya kunna wayar wani kiran ya shiga qarshe haka ya haqura ya zauna jiran lokacin daya diba kafin ya sake kiran Naziru.

Gidan suna kuwa gagarumin ruguntsumi ne ya sake tashi. Ana tsaka da dambaruwar yanda za’ayi a bude qofa, dangi da qawayen Addah sun taru suna mata tijara sun cika palour Amirah taf kaman an sakko daga Idi daidai da iska me kyau babu ta shaqa se kaya kaya akeyi.

Amirah na durqushe se rasgar kuka take har sannan akan yarinyar da harta gaji da komawa da numfashinta ta kwanta laqwas kamar mara rai ita duk wannan hayaniyar ba ganewa take ba, buqatarta a samu me kai mata ya Asibiti dan ta dade da saddaqarwa yau kashi ta ya gama bushewa.
Chapter 30 · 0% Book details