← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 158

Sashe 46

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin Magriba munyi wanka nida yaran munyi kwalliya yanda kasan ranar sallah. Wata Atamfa na saka Batik Maroon da akayiwa dinkin A line me dogon hannu babu ado a jiki se aikin stones da aka mata se walwali takeyi na kashe daurina na baza qamshi duk inda na juya yara se sun ce "kai Mami kinyi kyau wallahi" ni kuwa se jin dadi nakeyi.

Ina tahiyar qarshe a sallah naji waya ta tana qara kafin nayi sallama ta katse. Bayan na idar na janyota dan nasan Bashir ne, ilai kuwa wani kiran nasa ya sake shigowa.

"Ranka ya dade Mijin Ma'u, ka iso nazo na bude maka qofa ne" na fada da yar dariya.
Dariyar shima yayi cikin jin dadin sunan dana kira shi yace

"Mun dawo amma ban qara so gida ba"
"Masha Allah, sannunku da dawowa, muna jiranka nida yara mun shirya maka babbar tarba".

"Dagaske, me kika tanadar mun?" Ya tambaye ni, seda na gyara zama kafin nace
"Duk abinda kake so" na bashi Amsa.

"Ke kadai nake So Ma'una" yayi maganar cikin wani salo da yayi mun dirar mikiya dan har seda naji kamar numfashina ya tsaya na dan lokaci, jikina ya karbi saqon sa dagaske, se na yi qasa da murya kamar me gudun wani yaji abinda zan fada nace

"Na tana dar maka kaina, kai kadai nake jira Farin cikin Ma'u". Na fada sannan muka kashe waya. Cike da zumudi na tashi na mayar da dankali na na sake gyara fuskata sosai na qara turare. Palour na dawo muka zauna motsi kadan mu kalli qofa kowa ya qagara Abbi ya dawo har dai aka kira Isha Malam Bashir shiru.

Tafi tafi fa har qarfe tara babu Bashir gashi yara har sun fara qorafin yunwa suke ji, se na tashi a sanyaye na dibar musu abincin bayan sun shimfida Table mat a qasa dan kar a bata gurin suka zauna suka ci.

Muna zaune goma ta buga zuwa sannan hankalina ya fara tashi anya lafiya kuwa gashi na kira wayar sa har sau biyu bata shiga daga qarshe ma aka ce a kashe take.

Muna tsaye tsuru nida Amna da Aliyu dan ragowar sun kwanta, Aliyu ya kalle ni yace "Mami ko naje na tambayi Baba Audu naga yana gida".

Se a sannan ma tunanin yazo mun da mu gayawa Baban, na dago kai da niyyar bashi amsa wayata dake hannuna tayi qara alamar shigowar message. Number Bashir ce, sena bude da sauri na fara karantawa

"I'm sorry Ma'una, na wuce Gombe" Abinda ya rubuta kenan.

Wani duhu ne ya gifta idona na saki wayar a qasa nayi baya kamar zan fadi Amna da Aliyu suka riqe ni,

"Mami meya faru? Wani abu ya samu Abbin?" Aliyu ya shiga tambayata a rikice, dakyar na iya cewa

"Dauko mun Inhaler" se ya sake ni ya tafi da gudu dakina. Wayata Amna ta dauka ta bude, ina kallon ta bayan ta karanta message din ta goge daidai sanda Aliyu ya dawo yana bani Inhaler ya karbe wayar aga hannunta yana cewa

"Na gani me aka turo" se ya bude ya kalle ta yace "Ni banga komai ba, Mami wai menene?".

Seda naji numfashi na ya daidaita, Ina da Asthma kuma yawan ci baqin cikin Bashir ne yake motsamun ita dan ni da na shiga damuwa ko tashin hankali zanji numfashi shina yana sama sama.

"Ku tashi kuje ku kwanta babu komai, ashe ma basu taho ba" na fada ina qoqarin miqewa. Se Aliyu ya zuba mun ido kamar be yadda da abinda na fada ba, seda na sake maimaitawa sannan suka miqe.

Hannuna ya kama yace "Mami muje ki kwanta toh"

"Aa Aliyu sena kwashe abincin nan karsu lalace" na fada cike da qarfin hali dan na matsu subar gurin ko zan samu damar fashewa da kukan daya tokare mun maqoshi.

Qarfin hali kawai nayi muka kwashe kayan, ina shiga dakina na jingina da qofar na fashe da wani irin kuka na zallar baqin ciki da takaici, wannan wane irin wulaqanci ne, meyasa kwata kwata Bashir baya darajani?

Meyasa ze yaudareni yace yana hanya sannan ya zagaye ya tafi gurin Kishiyata? Idan ya ce mun Gombe ze wuce ai bazan hana shi ba tunda itama matarsa ce amma wannan ai zalunci ne yasa na bata lokaci na na shirya tarar sa sannan ya zagaye ya tafi gurin wata.

Haka na kwana ina kukan baqin ciki idona sunyi luhu luhu ga wani azababben ciwon kai daya kamani, sauqi daya dana samu Amna ba zataje makaranta ba saboda wani satin zasu fara WAEC ita ta shirya yaran ta basu abinci sannan tayi musu order Uber suka tafi.

Ina zaune a gaban mudubi ina shafa mai bayan na samu nayi wanka dakyar ta shigo da Try ta dora Mug din shayi da plate din dankalinda kwai. Akan Coffee table ta ajiye kafin ta zauna akan daya daga cikin kujerun.

"Mami" ta kira suna na, sena waiwayo nayi mata kallo daya na mayar da kaina.

"Mami kiyi haquri dan Allah, wallahi ba laifin Abbi bane kin san su Anty Amirah har gidan bokaye suna zuwa qilan Asiri sukayi masa" ta fada muryarta na rawa alamar kuka zatayi.

Sena juyo na kalleta ina murmushi nace

"Kinsan menene Amna?" Seta girgiza kai alamar Aa, numfashi naja kafin naci gaba da cewa

"Abbin ku be kyauta mun ba, inda ya fadamun ba yau ze dawo ba kinga da ban sha wahalar hada masa abinci ba. Kina kallo fa jiya ko baccin kirki banyi ba ina gasa masa zabo amma duk wannan wahalar ta tashi a banza kuma fa da magriba ma fa seda mukayi waya yace sun dawo yanzu ze taho gida".
Na qarasa ina share hawayen daya zubo ta gefen ido na, gaya matan da nayi se yasa naji wani sanyi sanyi a zuciyata.

"Haka ne Mami, nidai kiyi haquri ki dena damuwa daman abinda suke so kenan"

"Na haqura Amna, kije ki kwanta ki huta toh nima idan na karya bacci zanyi" na fada ina miqewa na bude wardrobe na dakko Doguwar rigar Yadi me laushi na saka. Tura abincin kawai na ringayi dan bakina sam babu dadi. Bayan na gama na sha Paracetamol na kwanta.

Dakyar ya yakice tunanin abinda Bashir yayi mun na samu bacci me nauyi ya dauke ni, gana jiya da banyi ba ga bashin na shekaran jiya.

BASHIR

Tun washe garin da ya sauka a Delta da daddare suna waya da Amirah tana ci gaba da yi masa kukan data ara ta dorawa kanta.

Cikin kukan take cewa "Kowa ya kira ni yayi mun gaisuwa dangi na kusa da na nesa amma banda Anty, ai ko ba komai tsakanina da ita ya kamata ace tayi mun gaisuwa ko su Aliyu ma ai duk ya kamata su kirani ko banza qanwarsu ce" .

"Ma'u bata kira ki ba?" Ya tambayeta da mamaki,

"Bata kirani ba mana inda ta kira ai Zan gaya maka  indai kuma ba murna take da mutuwar Iman ba". Amiran ta bashi amsa. Wannan fushin cewa bata kira Amirah ta mata gaisuwa ba shi ya hana shi kiranta har tsahon kwanakin da yayin.

Ko ranar data kirashi da Amiran suke waya, sanda kiran ya shiga harga Allah yaso ya daga dan yayi missing dinta amma daya gayawa Amirah nan da nan ta rikice ta fara masa kuka, basu kuma gama wayar ba se gurin sha biyu dan haka suna gamawa bacci ya kwashe shi.

Gaba daya yanzu shi tausayin Amirah yake ji. Koshi me Ÿaÿa Shida rasuwar yarinyar nan ta tabashi sosai bare ita me guda daya sannan ga irin wahalar da tasha shiyasa yake biye mata ko zata samu sassaucin abinda take ji.

Rabar laraban kuma da zumudin son ganin Asma'u ya taho, yasan be kyauta mata ba ya kuma bari ne se ya dawo sannan ya goge laifinsa, sanda ya kirata dagaske yana Lagos saukar su kenan amma suna ajiye waya Amirah ta kirashi tana kuka tamkar ranta ze fita.
Akan gashi har anyi sati da rasuwar Iman amma beje ya ganta ba.

"Ni daman nasan baka sona Yaya, baka qaunata farin cikin Anty da Ÿaÿan ta ne kawai matsalar ka baka damu da ni na rayu ko na mutu ba. Karinga tunawa nima matarka ce kamar ita, kuma ina da haqqi akan ka. kuma idan har ban yafe ba kasan Allah babu ruwan sa seya kama ka da haqqina". Tana gama fadar haka ta kashe wayar ta, bugun duniya kuma taqi dagawa.

Gaba daya ji yayi hankalinsa ya tashi, shifa duk abinda za'ayi kar a saka batun Allah ya isa. Ya fito kenan ze taho gida suka hadu da daya daga cikin Directors dinsu shima dan Gombe ne suka gaisa se yake gaya masa Gombe ze tafi yanzu.

"Sir Daman akwai jirgi yau ko a mota zaka tafi" Bashir din ya tambaye shi, se yayi murmushi yace
"Haba Engineer mota kuma a daren nan ai kayi mun fada, a jirgine His excellency yazo wani taro, kasan Abokina ne, toh na samu alfarma za'a rabani Private Jet mu tafi.

"Ai Sir ku manayan mutane ne da zan samu a rabani nima ai dana biku na dana" ya fada yana shafa kai, se Director yace "dagaske kake ko wasa se na kira Protocol naji idan ze samu".

Beyi zaton za'a samu din ba kawai ya amsa, yana kiran protocol din kuwa yace su taho yanzu su akw jira. Babu damar yayi wa Director wasa da hankali dole ya bishi suka tafi dukda shi kansa yasan be aikata daidai ba, amma yasan Asma'u tana da Fahimta, gara ya fara gyarota da Amirah sannan ya dawo kan Ma'un sa dan yasan ita bazata taba yi masa Allah ya isa ba kome zeyi mata.

A Flight mode ya saka wayarsa dan karma ta kirashi besan me zece mata ba, seda ya sauka a Gombe, yana kan hanyar zuwa gidan su ya tura mata da wannan Text din.

Sanda ya isa har sun rufe gida seda ya kira Naziru ya bude masa tukkana. Da mamaki Nazirun yake kallonsa, ya karbar masa Jakar suka shiga ciki kai tsaye ya wuce dakinsu da Jakar shi kuma Bashir ya wuce Dakin Dada dan burinsa yanzu yaga Amirah yaga halin da take ciki.
Chapter 46 · 0% Book details