← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 158

Sashe 26

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kadaiyi haquri” Dadan ta sake fada kafin su kayi sallama. Ransa a bace ya shiga dakinsa ya kwanta se kuma ya ja wayar ya kira Asma’u dan yau duk basuyi waya ba.

“Ran Alhaji Bashir Baban Ali ya dade” ta fada cike da nishadi dan hirar sa suke yi da Yaya Bilki ya kira. Murmushin da beyi niyya bane ya kwace masa kamar wanda ake watsawa ruwan sanyi yaji zuciyar sa na huce wa, muryarta kadai ta wanke masa bacin ran Naman suna seya gyara kwanciya yana cewa

“Ba wani nan bayan kunyi tafiyar ku ma kin manta dani inaga sena biyo ku sannan zaku dawo”

“Haba dai kwatakwata fa kwanan mu biyar yau cikin weekend muke saka ran dawowa ai” Asma’u ta fada.

“Shikenan ma kinga da kun dawo se mu wuce kawai, na gaji da zaman gwauranta kan nan”.

Dariya tayi kafin tace “oh kana Gombe kenan”

“Eh na shigo dazu, an sallamo Fatima yanzu tana gida”.
“Masha Allah Allah ya raya mata ya bata lafiya, ashe Addah aka saka”.
Da “Amin” ya amsa ya share tambayar ta ta. To me take so yace mata in dai ba son tada zaune tsaye kuma ba.

Yaran ya tambayeta tace sunyi bacci suka dan taba hira kafin sukayi sallama bayan sun gaisa da Yaya Bilkisu.

“Kinji mutuminki nace ashe Addah aka saka yayi kamar beji ba” Asma’u ta fada bayan ta ajiye wayar.

“Kema da neman magana kike wallahi me kike so to yace miki?” Cewar Yaya Bilki
“Me kuwa zece daman kinga ai ta ta uwar tafi tawa a gunsa shiyasa ya saka mata sunanta”.

“To da be saka ba dama Addini ne yace dole ayi ko kuwa da ze zama laifi” cewar Goggo da shigowarta kenan. Muqus Asma’u tayi, dan tasan idan ta tofa wata fada ne zata sha ita kam se taga kamar Goggo tafi son Bashir a kanta ma wani lokacin, bargo taja ta rufe har kanta hankali tacewa Yaya Bilki “idan ta fita ki gaya mun” jin Goggo ta ci gaba da magana.

Seda Goggon ta fita kuwa ta bude tana cewa “Ita Goggo bata san takaicin da ake qullawa mutum ba tayi ta rufeshi da fada, wai fa kinji ma cewa yake idan mun koma se mu bishi mu tafi ni nama fasa tafiya Sunday din sena tabbatar ya koma tukunna. Sati uku mukayi dashi munci biyu se na qarasa sati na wallahi dan har Bauchi nake so Naje wa Alawa sannan naje Jos ma”.

“Ai kuwa da ba kwana zakiyi a Bauchin ba nima da naje Alawiyya har tayi mitar ta gaji ban taba zuwa ba” inji Yaya Bilkisu

“Kai haba dai amma baki kyauta ba wallahi ina Gombe ina Bauch” cewar Asma’u

“Ba haka bane kinsan yawan ci abin zuwan haihuwa ce to kusan tare muke haihuwa kota rigani kona rigata amma daya baya Arba’in to sedai mu hadu a gida”.

“Eh to hakane”. Hira suka ci gaba dayi kafin sukayi bacci.

A Gombe kuwa washe gari Bashir ga haushin cinye masa nama gana tambayar kudi da Amirah tazo ta fara masa da sassafe, buyagin gaske yai mata ya faffada mata maganganu son ransa qarshe ta fita tana kuka da dana sanin zuwan daman Qawarta Husna ce ta tsara mata yanda zataje ta same shi gashi babu biyan buqata se baqin ciki ta kwaso tana shiga dakin ta kuma ta tarar da Addah ta cika baho da ruwan zafi ta tube Iman tana shirin tsumbulata tai mata wanka.

Da mugun gudu Amirah ta tare ta hannun ta ya shiga cikin ruwan da sauri ta cire jin zafin ruwan ta yayimi towel ta nade Iman tana kallon Addah data saki baki da Hanci tana kallonta itama.

“Dan ubanki saboda zan mata wanka shine kika buga wannan tsallen kamar wata yar ball kika kwace ta? So kike a bar ya mace ba wanka kusan sati biyu da haihuwa tayi warin qashi To wallahi ba da ni ba dole a wanke mata dattin mahaifa”.

Ita dai Amira bata kula ta ba, se jijjiga Iman da ke dan kukan da ko muryar ba’aji dakyau take dan ta firgita, jin Addah bazatayi shiri ba yasa tace “wai Addah baki ji me likita yace bane gaskiya idan ba zaki mata irin yanda yace ayi ba ki bar wankan kawai zan nunawa Inna Gaji ta ringa mata. Haka kawai idan wani abun ya sameta ai nice da Asara kuma ji ruwan da kika saka kamar wanda zaki fige kaza”.

Salati Addah ta debo ta dire kafin ta shiga auno mata ashar tana cewa “kiji mun yar banza ni kike shatawa layi akan wannan magen dan bazance mutum ba to kinyi da yar halak in na sake taba ta kice shegiya nake” ta mike tana gyara zani tana ci gaba da banbaminta.

Inna Gaji da shigowarta kenan ta tambayi ba’asi Amiran ta mayar mata seta dubi Addah tace

“Wallahi Fatu kin fiya tada zaune tsaye in ba haka tunda ga abinda likita yace se kibi na dan lokaci ne ko cewa akayi zata dawwama ba wankan ne se ki mata yanda suka ce.

Yanzu kizo ki zunduma musu ya a ruwa bayan naji ance tana da munoniya wani abu ya faru kinsan dai wannan sirikin naki manta komai zeyi wallahi har ni nan da babu ruwa na qila se yayi qarar mu ai wannan ruwan yayi yawa...kaii” maganar ta katse bayan data tsumbula hannu a ruwan, seta kalli Addah ido waje tace

Fatu kice kisan kai kika shirya wannan ruwan ko uwarta bata wanka da me zafinsa shine zaki jefa wannan tatsitsiyar yar a ciki? To nidai inaga watan tafiyata gida ya kama dan bazan iya zuwa polisteshan bada sutotimen ba”.

Addah da tayi tsilli tsilli dakyar tace “nifa ji nayi jikin ba kwari shine nake so na gasata jikinta ya hade amma tunda banyi abin kirki ba shikenan kuda kuka iya se ku mata” fuu tayi waje.
Wunin ranar haka ta yini mita duk wanda yazo seta gaya masa abinda Amirah tayi mata kuma dai kowa ita yake bawa laifi.

Ganin dai dagaske Bashir baze bada kudin taro ba Addah ta shiga ta fita da abinda Baban Amirah da yan uwanta suka hada da bashin Jama’a duk ta ganganda za’ayi bikin suna. Kayan abinci dama ba matsala bane sunyi akan na Store dinta za’a diba ayi komai.

Kaji kawai zasu siya se ruwa da lemo da kayan snacks se kuma kayan rabo da Amirah ta nace se tayi dan har ta kira me hoto yazo ya dauki Baby wanda za’a saka ajikin Jaka da Memo. Duk shirin nan basu gayawa Dada ba tunda tace bada yawunta ba balle Bashir da ya rantse ya kuma rantsewa baza’ayi ba shiyasa ma suka tsaida ranar Laraba bayan ya tafi litinan sannan zasuyi sunan.

Allah kaimu ranar suna lafiya 😂😂😂🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 17

Ranar Litinin Bashir ya tafi a ranar kuma Asma’u ta dawo dan ta tabbatar daman kafin su iso ya tafi. Da wuri suka taso dan haka sun sauka da wuri.

Gaba daya ranar baccin gajiya sukayi har zuwa washe gari talata sannan suka wartsake. Da yamma ta shirya dan tana so ta fita harta kunna motar ta amma taqi tashi tayi duk abinda zata iya amma taqiyi dole ta haqura ta kira Naziru ya zo da bakanike suka dubata yace dole seya tafi da ita gareji haka suka lallaba suka tafi se fasa fitar tayi.

Seda aka yi Sallar Isha tayi order Bolt, itada yaran suka fita, Shagonta na siyar da kayan yara sukaje dan tana so ta siyowa Baby Iman riguna, basu bata lokaci ba ta zabi masu kyau yan turkey guda uku se Shawl shima me kyau daya sannan tacewa yaran kowa ya dauki abu daya da ze kaiwa Baby Iman.

A leda aka zuba musu kowa aka bashi nasa suka juyo zuwa gida, seda ta dakko Atamfar data ajiye da zata hada musu da ita ta saka da qaramar Barimar Gold da tun cikin su Ahmad ta siyeta da aka ce mata mace ce qarshe se gashi ta haifi yan Biyu duk Maza tama manta da ita se zuwan nan ta ganta shine ta dakko ta hada musu da ita.

Yan uwan Amiran Suna zaune a palour sun baje kayan rabo ana zuzzubawa ita kuma tana daga gefe tana duba dinkunan ta ga gadon Iman a kusa da ita Asma’u sukayi sallama ita da yaran gaba daya.

A sake suka amsa musu, Amirah ta ajiye Kayan hannunta tana kallonsu, hada ido sukayi da Ma’u, seda ta murguda baki ta juya ido sannan ta gaisheta ita ko Ma’u data na ankare da duk abinda takeyi murmushi tayi kawai ta amsa mata a ranta tace “zaki gane kurenki yarinya Allah sa kiyi kuskuren zagina wata rana”.

Addah da tajiyo muryar Asma’u tai wuf ta fito daga daki, bakin kaman ze tsage saboda fara’a suka gaisa tana satar kallon Ledojin da suka shigo dasu.

“Miqo musu Yar mana Amirah kina zaune” Addah ta fada tana yiwa Amiran signa da ido, se Amiran ta daga ido ta kalleta fuskarta na nuna alamun “kin san me kike cewa kuwa” Ma’u da duk tana kallonsu tayi saurin cewa”Aa barta ma kawai bari mu qaraso mu ganta kar a jagwalgwalata”.

“Wane irin magana ne haka ke gafara da Allah ki gani se ayita wani saka ya a ke ji kamar kaza tunda tazo duniya ai dole a dauketa a haka zata saba” ta kwashe Net ta ciro Iman ta miqawa Ma’u.

Bakinta dauke da Bismillah ta karbeta cike da taka tsan tsan, masha Allah kuwa ga kamannin Farida nan a Fuskarta koda yake ai duk yaran da Bashir suke kama saboda ita macece shiyasa kamar ta da Farida tafi fitowa. Tana hannunta duk yaran suka leqata har Ahmad yana kama dan hannunta ya riqe.

“Mami muna son ta mu tafi da ita Lagos” ya fada yana wasa da hannun yarinyar, se Ma’u tayi murmushi kafin ta amsa shi Addah tayi caraf tace “Da ita zaku tafi ai Malam Amadu ko kuma in kunyi gaba zata biyo daga baya”.
Chapter 26 · 0% Book details