← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 158

Sashe 133

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mun sauka Gombe lafiya lau, daga gidan mu aka zo daukar mu. A cikin dakunan mu na yammatanci da yanzu babu kowa guda dayane Yaya Suwaiba da Mijinta ya mutu ta dawo gida take ciki nan aka gyaramun daya nima na shiga na zauna.

Wani iri na ringaji a zuciyata, ada kai tsaye gidan mijina nake sauka idan munzo se munkwana mun huta kafin nake zuwa gida mu gaisa amma yanzu wai har daki na samu na zawarci Allah kenan.

Saboda rashin ganin wata a daren ranar dole washe gari aka tashi da cikon Azumi na talatin kenan. Har gida aka samo mana me lalle da kitso tazo akayi mana ga yan sannu da zuwa qannena da yayyena suna ta zuwa abin dariya wai duk wadda tazo barka take mun na barin gidan Bashir kamar wadda aka sako daga kurkuku a maimakon su tayani jimami Yah Fati ce kadai ta nuna Alhini da rashin jin dadinta.

Nidai nasan banyi rayuwar qunci a gidan Bashir da har za'a ringa murna haka da rabuwar mu ba.
A daren aka kawo kayan su Jafar na gurin Yusuf, shadda ce yar ubansu kala biyu daya doguwa daya me babbar riga ko wanne da hula da takalmi qafa daya harda Agogo se dogayen riguna Abaya masu kyau na Amnah da Farida.

A daren na kira wayarsa amma a kashe, se na tura masa da saqo kawai nasan in yagani ko zuwa safiya ze kirani.

Washe gari aka sallace, munje sallar Idi mun dawo gurin qarfe sha biyu na saka Aliyu ya hada kan qannensa suka tafi gidan su Bashir suka gaishe su, se bayan Azahar suka dawo tareda Naziru da Yaran Amiru dukkansu da yake suka sunzo sallah harda Dan gidan Fainusa da alama shima bana an kawo mata shi kenan.

Har cikin gida Naziru ya shigo muka gaisa ina tayi masa tsiyar ko a waya ya dena nemana yanzu laifin me mukayi masa.

"Wallahi Anty bansan me zan ce Idan na kiraki ba, Yaya Bashir ya bata komai gaba daya ya saka kunyarki mukeji ko yanzu abinda Yaya Amiru ya gama fada kenan yake Lagos kwanaki amma ya kasa zuwa ku gaisa dan besan da wanne ido ze kalle ki ba"

"Haba Naziru, dan Bashir ya hada mu se kum ace dalilinsa zamu rabu, ni ban qullaci kowa a cikin ku ba wallahi in ma banda abinka shi daya aikata muka ci gaba da gaisawa muna zaune guri daya se ku da bakusan sanda akayi bane zaku ringa ji masa nauyi ai ba'a haka sedai idan kuma daman neman hanya kuke kaga ae ku yanke alaqa dani bawai dan abinda ya faru tsakanina da Bashir ba"

"Haba dai Anty alaqa kuma ai yanzu ma muka qullata kin taba ganin da ya sake uwa ai baze yuwuba, ni yanzu tsoron da nake ma kar ace za'a hanani Yayana ya jawo mun dan dai nasan baki manta alqawarin mu ba" ya fada yana sosa kai.

Dariya nayi sosai ina cewa
"Oh ni Baba Naziru wai kai dagaske kakeyi me zakayi da wannan kwailar ga manyan yammata nan a gari? Nida har ina maka kamun wata ma ashe kai kana nan dagaske kake ashe"

Kallon Amnah data tura baki gaba yayi yace
"Haba Anty wane irin wasa wallahi dagaske nake ni sedai idan kuma baza'abani ba in cire rai amma duk wani lissafina ai kena kinsani Anty tsokana ta kawai kikeyi"

"Babu wanda ze hanaka Naziru indai yarinya ta amince mu kam yan shan biki ne ko Amnah" Zainab data shigo ta tsokaneta ai kuwa ta kwasa da sauri ta bar gurin tana boye fuska.

"Yawwa Anty Zainab inaga qafarki zan kama ki tayani campain tunda naga Anty wasa ta dauki abun, nida ina can na saki baki wai ina da uwa a bakin murhu ashe ita sagegeduwa zatayi mun gara da Allah yasa na sani da wuri" Dariya mukayi gaba daya muka ci gaba da hira shidai jaddadamun yake fa wallahi Yana son Amnah kuma tun tana yarinya damanya gayamun bashida mata se ita nace toh Allahya tabbatar mana da Alkahiri.

Seda aka kira La'asar yayi mana sallama bayan ya rabawa yaran barka da sallah dubu daddaya ina ta masa maganar yayi yawa yayi gana yana cewa

"Bamu samu zama bafa Anty akwai labarai inaga da daddare zan dawo tuna dai an yafe mana laifi"

"Allah ya shiryaka Baba Naziru, ka gaida su Baba zuwa gobe zan shigo nima mu gaisa" munayi sallama ya wuce.

Seda aka kwana uku da sallah kafin ranar da yamma na shirya zuwa gaida Alhajin su Bashir. Ko babu komai darajar qaunar da yake nunamun ya cancanci naje, da La’asar na kwashi Khadija da Alawiyya muka tafi dan ranar gidan mu a cike yake maqil da Jama’a ranar ake zuwa wunin sallah wasu ma sunzo kenan tunda saura kwana uku a fara bikin su Bilal.

Da qafa muka tafi muna zuwa kan kwana daidai gidan su Ibbah na kalli gidan ina cewa
“Oh Allah sarki rayuwa ko ina Ibbah yake oho dan nafi shekara goma sha rabona dana ganshi”

“Wato yanzu har tuno da tsofaffin samarinki kikeyi saboda kin samu yanci, yana nan kamar ma acikin gidan yake zama da yayi aure kin san Mamansu ta rasu da dadewa da ya koma Ingila daga baya ya sake dawowa nan” Alawiyya ta bani amsa.

Seda na harareta ina gyara zaman Gyalen kaina daya zame nace “ke se ana zancen arziqi se ki sako na tsiya meye kuma wasu tsofaffin samari mtsw” haka muka qarasa gidan su Bashir tun daga waje muke jiyo hayaniyar Jama’ar gidan da alama suma yau suka zo ga yaransu nan nata wasa a Gareji muna shiga suka hau gaishe mu.

A tare muka rangada sallama kafin muka cire takalman mu muka shiga Palour Dada inda suke zaune gaba daya suna hirar tun daga kan Anty Amina har zuwa Sadiya autarsu a mata suna ganin mu sukayi shiru kamar ruwa ya cinye su.

Afiya ce tayi qarfin halin farayi mana maraba se Samirah da Sadiya da suke kan Three sitter suka miqe suna ce mana ga guri mu zauna muka samu kujera kuwa muka harde aka shiga gaisawa ina lura da yanda suke qaremun kallo kamar masu neman wani abu a jikina sena sake gyara zamana ta yanda zasuga dinkin doguwar rigar Lashin dana saka ga qafata tasha qunshi haka hannaye na zobuna harda na aro duk na hada na saka.

“Yanzu fa muke cewa zamu shigo gidan ai mu gaisa se gaku kunzo” Anty Amina ta fada tana dariyar yaqe, ban tanka ta ba nayi murmushi ina duba wayata da saqo ya shigo, Yusuf ne yana gayamun sun sauka a Abuja yanzu nayi masa sannu da zuwa da bangajiya.

“Su Asma’u ne lale maraba sannunku da zuwa” Muryar Dada ta katseni se na dago na kalleta yanda take bude mana haqora haka kawai na saki murmushi wanda na zallar takaici ne. Daga inda nake na dan zamo kadan na gaisheta, yanda kasan zata goyani haka ta ringa amsawa ta juya ta koma Kitchen ta kwalawa Fainusa kira se gata ta fito da qaron Try an shaqe shi da kayan lemo ga Kwanon Dambun nama dana Alkaki duka aka hado mana.

“Baba yana ciki ne naga bamu ganshi a qofar gida ba” na fada ina kallon Sadiyah, se Dada daketa faman musha ruwa tayi saurin Amsawa da cewa

“Yana nan, yau din beji dadi bane shiyasa ya zauna a ciki kinsan iskar maraice yanzu seta tado masa da zazzabi. Kusha ruwa bari nayi masa magana” ta juya ta fita.

Juyawa nayi na kalli Alawa da Khadija da suketa muzurai karma Khadija taji labari nace
“Kusha ruwa mana Khadija”

“Alhamdulillahi seda muka qoshi kafin muka fito daga gida” Alawiyyan ta fada tana miqewa, se Khadija ta tashi itama tana cewa

“Muje Anty ku gaisa tunda gurinsa muka zo lokaci yana tafiya”

“Au gurinsa kukazo to ai shikenan, ina namu yayan suke se a turo mana su suzo gurin iyayansu” Samirah da tun asali daman suna yar tsama tsakaninta da Khadija saboda sun taba hada saurayi qarshe kuma ba wadda ta aure shi a cikinsu ta fada, se kuwa ta waiwaya ta galla mata harara kafin tayi magana nayi saurin moqewa ina cewa

“Muje, Anty Amina se anjiman ku Allah bamu Alkahiri”

“Toh Ma’u ku gaida gida se mun shigo daman wallahi bari mukayi mu hadu tare gaba dayan mu se muzo miki jaje kiyi haquri” Anty Amina ta fada tana taka mana.

Alawiyya da har takai qofa ta juyo tace
“Ku mata jaje kuma meya sameki Ma’u da za’azo miki jaje? Indai zancen rabuwarta da Bashir ce kuyi zamanku wallahi ba se kunzo ba abu wata da watanni ai tuni muka gama karbar yan taya murnar base kunzo bama mu yafe muku wallahi”

Gaba daya suka raka mu da ido ina jiyo Fainusa tana cewa
“Kema Anty meye haka dan Allah kina kallon yanda suka shigo suna kallon mutane kamar wasu kashi ai gashi nan kinja sun gayawa mutane magana mtsw”

“Dallah gafara can an jawo din seki dakeni ai nasan kinji haushi” Amina ta fada tana harararta.

“Gaskiya dai Yaya Bashir ya luza ji yanda mata tayi luwai abinta zawarci ya karbeta ba irin wasu ba” Suwaiba data fi kowa iskanci ta fada nan da nan suka fara rigima da Fainusa dan dai ita kadai ce Bazawara a gurin kuma kowa yasan da ita take tunda daman sun ba mudai muka shige Palour Alhajin Su Bashir inda Dada harda qara shimfida mana qatuwar Dadduma akan Carpet din dayake gurin.

Cikin girmamawa muka gaishe shi gaba daya.
“Ki gafarce ni Asma’u wallahi nauyi da kunya ta saka na kasa kiran ki, Bashir be kyautawa kansa ba amma babu komai Allah yasa hakan shiya fiye muku Alkahiri” Baban ya fada daga kwance da alama jikin ya takura masa da gaske.

“Babu komai Baba, nima ai nayi laifi da ban kiraka na gaishe ka ba kayi haquri”
Chapter 133 · 0% Book details