← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 158

Sashe 10

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“I’m sorry Amirah ranar nayi miki ihu raina ne a bace Wlh ga Ma’una bata da lafiya a lokacin ke kuma kin dame ni da kira”

“Ba komai Yayana ya wuce yanzu ya jikin Antyn? Ban sani ba ai dana kira na mata sannu dukda idan na kirata ma bata amsawa kaga yanzu kosu Aliyu ta hanani magana dasu”

“Qorafi dai qorafi halin daya tsana da Amirah kenan a rayuwarsa” ya ayya a ransa a fili kuwa se yace
“Ta samu sauqi, se zuwa Next week zan shigo insha Allah akwai abinda kike da bugata ne?”

Se Adda ta zungureta tana rada mata tace kudi se tace
“Uhm uhm Ba komai maganar siyayya ne kawai daman se kuma ni Yayana ina so in dawo kusa da kai gaskiya saboda....”

“Amirah I’m looking forward to that ok maganar kudi kuma idan mun gama zan saka miki wani abun kafin End of the month saboda nayi hidimar Asibiti duk na kashe kudaden hannuna yanzu”

“To shikenan amma dai gaskiya Yaya nidai ko wani gidan ne se ka samar min da zan zauna amma irin Na Anty nake so me kyau sannan fa yaya karka manta da zancen canjin kujerun irin natan” ta sake fada dan harga ranta fa ita tunda ta tashi burinta kawai shine ta kamo Asma’u ta ko ina.

“Naji ki gaida su Adda” ya fada yana qoqarin kashe wayar jin tana so ta bata masa rai,
“Bama ta da lafiya bari na bata kayi mata sannu” ta fada kafin ta miqa mata kuwa qit ya kashe wayarsa dan itama Addan haushin ta yake ji dan abu da yawa ita take dora Amiran akai, idan banda bata da tunani kwana nawa basuyi waya ba amma da abinda ya kamata ta tare shi kenan? Bayan haka yanzu fa yake gaya mata bashida kudi amma ita wannan baya gabanta buqatarta ce kawai a gaba. besan dalilin ta na gasa da Ma’u ba komai ta gani a gurinta yunqurinta se itama ta samu, tana mance cewa Asma’u na aiki tana da abin kanta abu dayawa ko beyi mata ba zatawa kanta.

Gudun karta ishe shi ya saka shi yi mata transfer 100k saura 200k kenan kudin siyayyar kayan haihuwa dana fitar suna da tace ya bata, yace sun yi yawa ta ringa masa mita da qorafin bala’i dole ya yarda ze batan kota qyale shi.

shi tunda Asma’u take haihuwa baya tunanin ya taba bata dunqulalliyar dubu Hamsin wai da sunan tayi siyayya shi bata ma taba tambayarsa ba, duk abinda ya dakko ya bata idan yana dashi karba take idan ma bashi dashi haqura take yan uwanta su mata harma ya samu Arziqin shaddar fitar suna shima.

Baze taba manta Haihuwar Abdallah ba da tace ya saka mata sunan Babanta yace mata sedai ta se masa rago hakan kuwa akayi ta siyo raguna har biyu ta kuma cewa Yan uwanta da Nasa shi ya siya har yu har gobe ya kalli yaron se yaji wata kunya da Nauyin sa dana Uwarsa ya kamashi, shi wallahi a duniya in yai wani abun se yaga kamar dai shafar Aljanu yake samu su saka shi yayi abu daga baya yazo yana dana sani (Shafar Aljanu ko iskanci ba 😂😂)

Dakin ya koma Ma’u najinsa tayi shiru kamar me bacci ya gaji da tsayuwa ya qaraso ya mata peck a goshi ya fita yanaso yaje gida ya dan yi bacci tunda yaran basa nan yau shima ya dan huta kafin gobe Monday.

Su Addah kam Kudi na shigowa suka hau Murna “Ke yar nan kinga abu kaman wasa aikin malam ya fara kama Bashir to wannan aka gama aiki kuma ai ban san yanda zamu taka shi ba yanda muke so. Ita waccan shegiyar dama itama ba a zaune take ba dole nata yaqi tasiri amma tunda mun rabu lafiya shikenan, yanzu bari an jima zan kira Malam se ya nada account mu sake tura masa ko kudin biyu ne tunda na bada na biyu ayi a gama aikin nan mu fara shan romon damokaradiyya”

“To Adda amma da mun bari dai akwana biyu a sake samun wani abun wannan mudan rage siyayyar mana” cewar Amira.

“Ke dallacan ba gara a gama ba nasan ko million goma kika ce ya baki kawo wa zeyi”
“Kuma fa haka ne, to ki kira se a tura masa din”

“Allah dai ya kauda bacin rana” Ummi ta fada tana miqewa kafin ta karbi duka ko Ashar daga gurin Adda ai kuwa ta shiga aika mata dasu tana ce mata yar baqin ciki haka zata qare tana gani suna abin arziqi banda ita.

Wai ya Hajia Balaraba ta qare da maganin Malam Wizy ne?? 😂😂😂🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 7

A bangaren Hajia Balaraba kuwa cike da farin ciki ta bude gida ta shiga ganin har sannan Kishiyarta bata dawo daga gurin aiki ba, cikin sauri ta fito da rubutu ta huda leda tareda guntsa ta feshe kofar dakin Amarya tana cewa “Shegiya maza ki dawo ki taka ni Alhaji yaiyo waya daga kasuwar ma yace ya sake ki base ya jira ya dawo ba” ta qulle ragowar gudun kar ya zube ta qarasa qofar ta.

Mayafinta kadai ta ajiye ta shiga kitchen ta hau kicikicin dora girki qarin farin cikinta ita ce da girki dama kai yau koda ba itace da girki ba ai dole tasan yanda za’ayi ta aiwatar da aikin nan tanayi tana tuna irin cin mitunchin da Alhaji yai mata dazu da safe kafin ya fita kuma ta tabbata duk Amarya ce ta zugoshi har yana iqirarin tabar ganin sun tara yaya da jikoki tsaf seya yanka mata tikitin zawarci.

Itadai tunda Malam na kan Tudu ya kwanta dama kamar ya tafi da duk ayyukan da Tayi akan Alhaji ne komai ya karye shekara da shekaru tana cin duniyarta da tsinke se yanzu da tsufa ya kusa cin mata ne zata fara karbar taskun namiji ina bazeyuwu ba ai.

Tsaf ta gama hada lafiyayyar Miyar taushenta kafin ta dakko qaramar tukunya ta sare wata wadda zata ci, nan da nan dakko ragowar rubutun Malam Wizy ta kurbe tas ta kuskuro dattin bakinta da komai ta watsa musu a miya ta sake kurbe ragowar ta zuba ta juyata dakyau ta rage wuta ranta fes dan gani take kamar ma aikin gama ya gama.

Tana cikin malmala tuwan autarta me suna Ruqayya ta shigo ta dawo daga makaranta dan tana shekarar ta ta qarshe ne a GSU da mamaki ta kalli maman tata kafin tace “Hajia kece dakanki yau a kitchen ina Baba Zulai din”

Bata ko dago ta kalleta ba tace “Taje gida Sa’adenta batada lafiya ina ga se gobe zata dawo”

“Kai dukda haka da mamaki ace Hajia kina girki lallai yau zamu kwashi dabge bari nayi sauri nayi wanka nayi Sallah muzo mu kwashi ganima”

“Zaki kwashi ganima dan uwarki duk zan kulle bakinku ai na ga ta inda zaki ringa kaiwa uban naki gulma idan na taba kudinsa” ta fada bayan Ruqayyan ta fita daga kitchen din

Oho bata ma san tanayi ba dakin ta ta nufa a ranta tana ayyana tabbas akwai wata a qasa dan ita dai tafi shekara Goma rabonda taga Hajia tayi girki da kanta Baba Zulai ce take yi musu ko kuma ita idan taba gida. Ita zata iya cewa ma idan kaga Hajia a kitchen to an gama Abinci ne idan harda na Baban zatayi barbade daga baya ma daya gane yai Allah ya isa yama zo kuma ya dena cin abincin kwatakwata se baya bayan nan taga ya dawo yana ci.

Ita kuwa Hajia tana sauke tuwo ruwan Tea ta mayar ta saka lipton dinta da kayan qanshi sannan ta zuba jiqon Wizy, bata matsa ko ina ba seda ta kammala tsaf ta hada komai ta kai kan Dining sannan tashi ga dakinta tai wanka ta fara jero Qara’in salloli.
Seda akayi Isha Alhaji ya shigo, kai tsaye part din Amarya ya shiga dan akwai kayan daya manta da safe da ze tafi kasuwa yana so ya dauka kar gobe ya sake mantawa. da mamaki ya kalleta dan ya zata ta tafi aiki tunda tace masa Night Duty ne da ita. tana ganinsa ta miqe

“Yawwa Alhaji dama kai nake jira tun dazu”
“Lafiya Abida baki tafi aikin ba? Jiran me kike mun?” Ya fada yana kallonta. Seta miqa masa wayarta kawai ba tareda tace komai ba, karba yayi yana duba screen din sega video Hajia Balaraba tana kici kicin zuge jaka, baya jin me take cewa amma fes yaga sanda ta ciro leda ta guntsi rubutun ta feshe kofar dakin Amarya ta tafi”
Se ya miqa mata wayar dason jin qarin bayani.

“Wallahi Alhaji yanda ka gani dinnan kasan ka fita ka barni kaina yana ciwo dan haka sena kwanta dan ban ma samu zuwa Barkar Haula da nace maka zan fita ba, se bayan La’asar na ma idar da sallah na tashi zan leqa na karbo Kati se naji motsin a bude qofa, in duba ta window fa shine naga Maman Suhaila na wannan ta tsaya tana maganganu tareda bude jaka wayata na hannuna ni kuma shine na kunna video saboda kar a maimaita irin ta wancan karan data zuba magani akace qarya nakeyi yanzu dai ga Hujja ka gani da idonka, nidai ban fita ba koma na menene kai kadai ka tsallaka shi se kasan yanda zaayi azo a karya dan bazan yi ta zama a daki ba kona fita a sabautani a banza”.

Wani irin tuquqin baqin cikine ya rufe Alhaji har huci yakeyi, wato duk Allah ya isar dayai wa matar nan bata daddara ba kenan? Shin wai se Yaushe Balaraba nutsu tasan Annabi ya faku ne ita dai duniya ce kawai a gabanta to kuwa Insha Allahu Allah baze sake bata ikon maidashi halin data jefa rayuwarsa a baya ba shi wallahi badan kar duniya ta zageshi ace ya saki matar sa auren shekara Arba’in ba da rabuwa zeyi da ita ya huta amma yanzu babu wand ze dubi abinda ta aikata masa shedai a dora masa laifi ace Ya wulaqanta Uwargidansa.
Chapter 10 · 0% Book details