← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 158

Sashe 91

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kina ji ko? indai kina so ki zauna lafiya da yaran nan to ki kama girmanki a cikin gidan nan. Babu ruwanki da shiga shirgin Aliyu ko Jafar. Su ai ba kamar twins bane da se kin ajiye su kin zuba musu abinci ko su ci abinci ko karsu ci ba damuwarki bane abunda yake naki ki dafa musu ki ajiye idan sunji yunwa da kansu zasu fito su nema.

Bana so na sake jin wani abu makamancin haka ya faru wai kin shiga dakinsu har ta kai ku gayin rigima wani yaji ciwo, ki kiyaye”.

“Oh abinda ma zaka fada kenan, laifina ka gani yanzu bana su bama kenan? Toh wallahi bazan yarda ba, daman na bari ne ban dauki mataki ba ina jiran seka zo amma tunda bayansu kabi wallahi se jikin yara ya gaya musu a gidan nan dan babu shegen dan da ze taka ni in saka ido ina kallonsa” Amirah ta fada tana miqewa tsaye zata wuce, a fusace Bashir ya tsayar da ita yana cewa

“Na rantse da Allah kika sake kiran yarana da shegu sena chanzawa bakin ki halitta tunda ke baki da hankali ba kuma kisan abinda zaki fada ba, sannan karki fasa dukan su ni kuma babu yaron da zan tsawatarwa a gidan nan idan ya miki rashin kunya tunda abinda kika zaba kenan” fuu ya wuce daki ya barta a tsaye tana qunquni.

Tana tsaye a gurin su Aliyun suka shigo, ta waiwaya ta kalle su, badan ba wallahi seta tsinka musu maruka koma ta rufe su da duka dan gani takeyi zata iya, amma tsoron abinda Bashir ze iyayi ya sakata watsa musu harara kamar idonta ze fado suma kuwa basu bata lokaci ba suka maida mata har Aliyun yana cewa

“Da magana ne?”
Seta ja tsaki kawai ta wuce dakinta, tabbas da sake dole ta dauki matakin gaggawa tun kafin abubuwa su rin cabe mata yanda bata tsammata ba daga uban har yaran seta dauki mataki akan su ta yanda babu wanda ya isa ya sake nuna mata yatsa a cikin su.

Haka ta kwana saboda tsabar takaici ko dakin Bashir bata je ba, sanda Faridah ta shiga zata kwanta ma da masifa ta hauta yarinyar na kuka ta tafi dakin uban lokacin yana zaune yana aiki a laptop dinsa. Gobe Monday, gashi yana da ayyuka a gabansa da yake so ya qarasa dalilij da ya saka be fita ya kulata ba kenan se kawai ya cewa Faridan ta hau Gadonsa ta kwanta ya ci gaba da aikinsa yana ayyana hukuncin da ze dauka akan Amirah.

Washe gari da Asubar fari ya buga mata qofa sanda zasu wuce masallaci akan ta fito ta samar musu abin karyawa da wuri.
Har suka dawo kuwa yar gaske bata leqo ba dan daman daya tasheta yana fita ta koma baccinta dan tace ba shegen da zata yiwa girki da Asubar nan su tafasa ruwan shayi akwai komai har Buredi su sha ita bata saba wannan wahalar ba.

Sanda suka suka shigo a zatonsa ta tashi tayi sallar harta shiga Kitchen dan haka dakinsa kawai ya wuce ya tashi Faridah yace taje dakin Amirahn tayi wanka ta shirya shima ya shiga wanka.

Da dari dari Faridah ta shiga dakin se ta tarar da Amirah ta shanya baki tana bacci abinta dan haka sadaf sadaf ta shige bandakin ta rufe a hankali dan karta tasheta, har kuwa ta gama wankanta ta shirya ko motsi Amirah batayi ba, saboda neman tsokana ta kwashi turaren Amirah ta feffesa da sauri ta kwashe kayan data cire ta fella gidan Ma’u da gudu dan ita daman Uniform kadai ta dauka a kayanta komai yana dakinsu na gidan a can ta barsu.

Sanda ta je ta tarar da Amna na hada Breakfast Ma’u na wanka dan sun makara tashi da safen, tana ajiye kayanta ta wuce Kitchen takwashi dankalin da Amna take soyawa tana cewa

“Yah Amnah ki qara wani nasan yanzu yunwa zata koro su Yah Aliyu zasu zo har Abbi, bafa ta tashi daga bacci ba haryanzu Anty Amirah bare ta bamu breakfast” se ta miqe da sauri kuma ta shiga hada tea tana cewa “bari na zuba a Water bottle na sha a mota dan nasan yanzu Abbi ze fara a fito a fito bata rufe bakinta ba sega sallamar su Aliyun yan biyu suka tuga Kitchen da gudu jin qanshin abinci babu bata lokaci kuwa suka dirar wa Dankalin dan ma kamar Amna tasan za’ayi haka ta soya da yawa daman niyyar ta ta zuba musu su qara ko a mota kafin suje makaranta.

Tas suka cinye kowa ya dauki container cake dinsa da inibi da yar cakulatin da ake saka musu Suna haka ma’u ta shigo Kitchen din ta shirya tsaf cikin wata doguwar rigar Jallabiyya baqa da bata da Adon komai ta saka hula a kanta kafin tayi rolling mayafin rigar hannunta riqe da qaramar handa bag Fara se qamshi me sanyi takeyi.

ASMA’U

Da mamaki na kalli yaran ina cewa “ku kuma daga ina haka da sassafe se dambe kukeyi da abinci kamar wadanda sukayi kwanan yunwa”.

“Mami ai tashin yunwar mukayi shiyasa ba’a bamu abin karyawa ba” Jafar ya fada yana dariya,

“Allah ya rufa asiri, se kuyi saurin kunsan yana jiranku” na fada ina rufe baki kuwa sega horn din Bashir kamar wanda ze tashi gari.

Tareda su muka fito tunda sun cinye abincin na haqura idab naje office na nemi wani abun, kallon second daya nayi wa Bashir daya bude mota ya fito a fusace inaga da binsu cikin zeyi, har zan wuce se na sake waiwaya wa nace

“Baban Ali ina kwana” be amsa ni ba nima kima daman ban saka raiba, na kunna mota ta na ajiye jakar na sake komawa ciki dan na manta da wayata. Sanda na fito sun yafi nima naja na wuce nawa uzurin a raina ina ta mamakin ya akayi Amirah bata basu abin kari ba?

“Qila tana ta baccin nan nata na asara” na ayyana a zuciyata kafin na tabe baki na ci gaba da tuqina.

BASHIR

Qarfe bakwai saura ya fito daga dakinsa tsaf cikin shirin tafiya aiki, gaba daya wani daban ya ringa jinsa, kayan kansu ji yai kamar ba daidai ya saka ba seda ya ringa kallon kansa a mudubi ya tabbatar dai daidai yake kafin ya fita palour.

Ya rigada ya saba daga litinin zuw Juma’a Ma’u ta ware masa Suit din da ze saka hatta da takalmi da agogo komai seta ajiye masa sannan idan ze shirya tana tsaye tana taya shi ya gama ta fesa masa turare sannan su fito suci abinci cikin nishadi kafin kowa ya tafi aikinsa.

A shirye ya tarar da yaran, Aliyu ne yayiwa yan biyu wanka ya shirya su tsaf kowa ya fito goye da jakar makarantar sa suka zauna a palour shiru dagani shi suke jiran fitowar sa. Yan biyu ne suka gaishe shi ya amsa dan sun rigada sun gaisa da ragowar tunda Asuba, seya kalli kan Dining yaga wayam dan haka ya nufi Kitchen a zatonsa tana ciki amma yana zuwa nan ma babu kowa babu ma alamar an girka wani abu a cikin sa.

Dakin Amirah ya tafi yana shiga tana miqewa zaune da alama tashinta kenan ta gantsare tana miqa, cikin muryar wanda ya tashi daga bacci tace
“Kai qarfe nawa ne naga harka shirya yaya ko daman da Asuba kake fita?”

Be amsa tambayarta ba, ya ce mata “kinyi sallah?”

Shiru ta masa alamar bata yin ba kenan abinda ya qara bata masa rai a mugun fusace yace mata

“Da zan fita sallah ban tasheki ba sannan na gaya miki kiyi mana abin kari da wuri shine saboda rainin wayo kika ci gaba da baccinki ko?”

Seda ta zauna sosai kafin ta kalle shi tana tura baki tace “ni banji sanda ma ka tasheni ba, kuma abin kari baga kayan shayi nan ba harda buredi kawai ruwa za’a saka a kettle fa kawai shine sena tashi nayi muku” ta qarasa tana juyar da fuska gefe, Bashir kuwa kallonta kawai ya ringa yi, badan ba seya kwada mata mari wallahi amma dukan Mace ba dabi’arsa bace, dan haka ya juya kawai yana cewa

“Wallahi Kinji na rantse idan na dawo na tarar da wani abu ba yanda ya kamata ba a gidan nan se kin gane kurenki tunda naga alamar ke ba’a gaya miki magana kiji da kunnenki to masan maganin ki” bamm ya buga mata qofa ya fice.

Amirah kuwa ko a jikinta ta miqe tana cewa “oho dai, girki ne bazanyi ba haka kawai ni ban haifa ba a ringa sakani tashin Asuba. Dama kai kadai ne na daure nayi amma wallahi bazan girkawa wasu qattin yara har shida abinci da Asuba ba suci su zageni ko to sedai suje uwarsu ta basu badai ni ko in ka gaji ka ringa dafa musu” tayi shigewarta bandaki, ba ita ta gama rashin hankalinta tayi sallar Asuba ba se kusan takwas na safe.

Bashir kuwa yana fitowa yaga basa palour, yasan bazasu wuce gidan Ma’u ba a ransa yaji wani sanyi ko banza zaman ta a kusa dasu Alkahiri ne.

Yaransa basu taba tafiya makaranta basu karya ba ko shi kansa se dai idan baqin halinsa ya motsa yaqi ci amma babu ranar banza da bazata dafa masa abinci ba amma yanzu daga zuwan wannan yarinyar ta fara yi musu horon yunwa dole ya taka mata burki.

Yana sane ya ringa fafara musu horn ga haushin yasan yanzu suna can suna cin dadi shi kuwa sedai yaje yaci a Cafeteria kawai yayi manaji gashi har an fara saka masa ido kwanakin nan da yake ci acan har suna tambayarsa ko dai Madam tayi tafiya ne yace musu Eh yanzu hakan dai zeje yau ma amma daga gobe dole ta shiga hankalinta, idan batayi wasa ba harna rana seta girka ta aika masa dashi kuwa.
Chapter 91 · 0% Book details