← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 158

Sashe 134

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Aa karki kuma ai ke kika cancanci ban haquri,ki ci gaba da haqurin dai in sha Allahu zaki dauke shi a gaba. Ina Alhaji Abdu? Dazu da safe yazo ai ya kawo mun magani kin gansu can wai shi likita ne saboda jiya na gaya masa ina ciwon kai da daddare da zasu tafi” ya fada yana nuna mun paracetamol din da yake gefensa.

“Au wai daman kai ze kawo wa? Yazo yana ta tambayata wai maganin ciwon kai na zatama shi ze sha na bashi a she nan yayiwo”

“Nan yazo ai ya jima ma, amma fa nayi nayi yaci abinci yaqi wai Mami ta hana su kwadayi banda abin Abdullahi nan ai gidan su ubansa ne ko yana inda yafi nan ne ko da yake qila ba’a fayyace masa ba” Dada ta fada da yar dariyarta, sena daga kai na kalleta kawai nayi murmushi

“Yaushe zaku wuce saboda aiki? Koda yake akwai bikin Su Bilalu na manta se an qare zaku koma kenan” Baba ya sake fada ba tareda yabi takan zancen Dadan ba.

“Eh se an gama biki Baba, daman sati biyu zamuyi gaba daya”
“Toh Allah ya taimaka yasa ayi a sa’a. Kema Allah ubangiji ya fito miki da Miji na gari kiyi auranki kinji”

“Amin Baba, Ai Allah ma ya kawo mata sedai ayi Addu’ar fatan Alkahiri kuma” Alawiyya tayi caraf ta amsa.

“Kai madallah amma naji dadi ubangiji ya tabbatar da Alkahiri yasa zamu gani kai nayi murna sosai, Nafi kinji abin Allah ko Baba ya fada har yana miqewa zaune.Dada da tun fara maganar Alawiyya tayi kasaqe tana kallon ta tace

“Uhm” tareda yaqen dole,har muka gama hirar da zamuyi Baba nata sa mana Albarka muka miqe. Jakata na zuge na ciro bandir din yan dari biyu sababbi dana tanada na ajiye a gabansa ina cewa

“Gashi Baba babu yawa a siyi Goro, an jima na turo su su duba jikin naka”
“Kai kai Haba Asma’u dauke kudinki kinji ai gaisuwar da kika zo mukayi ma tafi komai Nagode Allah yayi miki albarka” ya fada yana turomun kudin se na nufi qofa ina cewa

“Dada se anjiman ku toh”. Seda Alawiyya da Khadija ko wacce ta qara aje masa dubu biyar biyar kafin muka kama hanyar gida. Har Get Dada da duk jikinta yayi sanyi ta rakamu kafin ta juya, har mun fita Samurah ta kwaso da gudu tana tambayata wai
“Anty zan samu chanjin sabon kudi?”

“Sabon kudi ai yana banki Samirah, ki nemi Sa’ad mana sune ma’aikatan banki” na bata amsa muka qara gaba.

Oh ikon Allah, ada fa idan zanje gidan irin haka sena shaqe uwayen kuloli da Abinci kala kala, Dubu Goma nan sena aje mata ta goron sallah banda wadda zan rabawa kaf jikokin gidan idan sunzo sannan su kansu qannen nasa wasu su fake da chanjin sabon kudi wasu kuma kai tsaye ma zasu ne na basu barka da sallah idan kuma zamu tafi nawa Yayan ko yar biyar babu me basu idan ba Amiru ba shi daman har gida yake zuwa ranar idi tareda Sa’ad da Naziru suci tuwon sallah ya raba musu kudi amma matan babu me karar ko dan kunne ta kawowa Farida seni jaka na hidimta musu nayiwa Yayansu kai kar Allah ya kawo abinda baze wuce bama.

A daren ranar Alhaji Qarami yaki rani bangarensa yana tuntubata wai ya muke ciki da Yusuf?
“Mutumin nan na qaunar ko Ma’u, dukda baka shaidar Dan Adam amma ina kyautata masa zato akanki wallahi ga danginsa suna sonki”

“Uhm toh Yaya nidai ina ta Addu’a Allah ya zabamun mafi Alkahiri dai, kuma fa shi Yusuf din nan ma ni ban gama gane masa ba. Wai ita matarsa wane irin aure nema suke tana wata duniya yana wata nifa sau daya naji yace yaje can inda take” na fada ina gyara zama.

“Wayaga Ballan sori, ke har lissafin wannan kikeyi ma ai in kinji ana da ita da babu duk daya to wannan mata ta Yusuf kenan. Ita fa tsabar Gayunta ne ta girmi zaman Najeria, daman yar uban gidansa ce Ambassador Musa Manzo ya aureta uwarta Baturiya ce.

Shikansa Baban nata irin wannan gantalallen auran sukeyi da uwar tana can America shi da sauran Matansa suna Nigeria se sanda yai ra’ayi yaje ko ita tazo to itama Inteesar din da akwai yayarta itama me aure ce duk haka dai suke wannan gantali da Yusuf din.

Dan haka ma ki saka ranki a inuwa kamar ma ke kadaice bakida wata kishiya dan yanda kika San ba Mata ba wallahi. Su yawon shaqatawa da zaga duniya da kwalliya suka saka a gaba. yo tikita ta yanka masa fa yaje ya nemi duk wadda yake so akan dai tazo Nigeria tayi zaman aure wai kuma a haka sonsa take kamar me badan ma Allah yasaka nutsatstse neba aida yayi tambari yanzu a neman matan banza tunda auren fa kusan shekara biyar kenan ana wannan gantalin kawai ki amsa mana musha biki se mu daura Addu’a qanwar mu ta zama Firs Lady ai mukam ras damu” Anty Ladi da muke cewa Momi uwargidan Alhaji qarami ta koromun wannan jawabin.

Tagumi na rafka ina jinta, ikon Allah kunji wata sabuwa kuma su haka suke kenan daga uwar har yayan?

“Toh kinji ai se kuma me kike buqatar sani ki tambayeta” Yaya ya fada yana yar dariya.

“Kai ni fa Yallabai randa mukaje ganin ginin nan nasa kwana nayi da takaicin da yanzu mu zamuje muyita iyayi muna zuba kaya gidan qanwar mu, na ringa raya da ina da Yar data isa aure ko qanwa to fa duk ma yanda za’ayi se an hada auran su da dai a dakko bare taci arziqin dan nasan aure ze qara.

Harfa na fara tunanin na qyasawa Suwaiba se kuma nace kar kayiwa kishiya hanyar arziqi se abu ya samu a manta dakai kwatsam se gashi wannan abu ya wakana kai nifa harda sujudushshukur nayi kana fita randa ka gaya mun maganar nan, yo ko zuwa nayi na dauki hoto a gidan ai an biyani wallahi”

Sosai muka ringa dariya nida Yaya musamman wai kar ta gayawa Anty Suwaiba kishiyarya ae arziqi ya samu su manta da ita.

“Ku zauna kuna dariya shi ai yasan me muka gani wallahi keni ko bakyason sa dan Allah ki aure shi kowa ya san gaba kika ci ba baya ba”

“Aa dai gara tana son nasa dai, ni na zata ma sun gama komai ai yanda yake addabata da waya duk lissafina kawai mu hada danasu Bilal a daura daga baya se suyi tariya ko” Alhaji Qarami ya fada

“Ai da ka gama mun komai wallahi yallabi kawai ayi haka, kai infa aka biye ta Ma’u ba wanda zata so wannan mijin nata me fuskar shanu ya rigada ya rubuce sunanta a Allon qarfe se ta Allah kawai gara in ma dole za’a mata ayi a wuce Gurin”

Dariya sosia Momy ta ringa bani daman ita haka take akwai abin dariya, tana da matuqar kirki ta kuma kama girmanta a matsayinta na matar babban wan mu babu raini haka babu wulaqanci kowa natane sefa wanda yazo mata da abin da be mata ba bazata dauka ba.

A gaba da sakani da hudubobi dan Alhaji tashi yayi ya barmu bayan daya jaddadamun na san matsaya dan Goggo fa dagaske tace tana dawowa dole na fitar da miji nayi aure kona tattaro na dawo Gombe na bar aikinsa yayi sanadin gurgudewar aurena.

Ranar raba dare nayi ina saqa da warwara, daga qarshe na tashi na raya daren addu’ata dai a kullum zabin Alkahiri daga Allah (To Hajia Ma’u kwankwasa qofa za’ayi ace fito ga zabin da Allah ya miki ko yaya? Ke zaki saki ranki ki bude zuciyar ki sannan ne zaki fahimci abinda Allah ya zabar mikin).

BASHIR
Haka ya sallace cikin quncin zuciya da takaici da dana sanin me yasa ma be tafi Gombe ba shima. Sallah guda haka ya zauna a gida yana zare ido dama dama ran idi yaci abinci dan Fried rice Amirah ta daure tayi musu ranar harda Salad ga Zobo me sanyi da dabgen kaji.

Haka yaci ta a babu yanda ya iya to yaushe rabon ma daya samu kamarta din? Babu tuwon sallar nan dasu Sinasir da waina kai gaba daya Eatate din qiyau miyau kodan qamshin abincin sallar nan da zakaji gari ya dauka babu toh duk musulman sun wuce garuruwanau sallah shima tsautsayi ya zaunar dashi dan be tabayi ba se wannan karon.

Yana daki yana aikin kallon status din Jama’a na sallah kowa da Yayansa sunje Ido seya tuna yanda Ma’u take tasa shi su kashe hotuna ran sallah da duk wnada ya kalla seya yaba wannan karon ko Babbar rigar ma ajuye ya sakata seda yaje masallaci aka gaya masa ya gyara dan sanda ya shirya ya tafi Matar gidan bata ma fito daga daki ba bare ta taya shi shiri, daya dawo dai ya tarar ta cancada kwalliya da kayan daya mata ta kuwa yi kyau sosai masha Allah haka gidan an gyara abinda ya sauqaqa bacin rabsa kenan sannan ko ba komai ya dan samun abin kaiwa bakin salati.

A status din Amnah yaga hotunan su na Idi, shaddar gurin Yusuf me babar riga yaran suka saka sunyi kyau kamar ka sace su ka gudu haka ya ringa zooming yana murmushi da jin kansa na fasuwa wai fa yayansa ne da Ma’u, yo ko dan su ai dole ma ta haqura ta dawo su zauna.

Hoton da sukayi ita da yaran ta cakare kamar wasu qannenta sun sakata a tsakiya ya tsaya yana kallo nan da nan ya kwafa ya dora a status dinsa kuwa. Haka ya wuni kallon hotuna Daya gaji da zaman gida ya fita zaga gari, su Addah dai ana palour ana warkajami da Kajin da sukayi Dabgensu.

Ranar kwana uku da salllah da yamma sakakiya Dada ta kirashi tana gaya masa abin tashin hankali zancen wai Asma’u ta samu miji sun daidaita lokaci kadan ya rage ta daura aure.
Chapter 134 · 0% Book details