← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 158

Sashe 55

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daman cefane baya yankewa a gidan kusan zece buhun huna kadai yasan yana siya amma sauran abubuwa tunda daman ita yake bawa kudin tayi mantawa yake kuma bata tambayarsa haka zega komai a ajiye. Yanzu a satin daya wuce ta ce masa Bilal ya turo mata wasu motoci idan yana so ita ma zata chanza tata ko School Fees din makaranta na wannan term din ita ta biya se daga baya ya mayar mata da kudinta gashi kuma a kullum cikin yin suturu na alfarma take daga ita har Yaranta har shi tana siya masa takalma da Agogo ga turaruka.

Wadannan abubuwan daya hasaso a shirmensa su yake ganin zasu sa tafi qarfinsa har ya kasa juyata gashi kuma sauran mutane ma sun fahimci cewa Asma’u tafi qarfinsa a ganinsa babbar gazawa ce kamar shi ace matar sa tafi qarfinsa dan haka dole ya dauki mata ki akai.

Kunsan December ansha Bukun kuna
Allah ya bawa Amaren mu zaman lafiya ya kawo na yan baya 🙏🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 30

ASMA’U

Cikin kwanaki biyar muka gama abinda ya kaimu, ada naso na yi weekend na huta ne har nadan zaga dangi amma saboda yanayin rabuwar mu da Bashir yasa na fasa daga gidan Alhaji qarami ko gidan Yayata Junaidiyya da mijinta yayi Accident, naso naje na dubashi amma gudun kar sauran suce banje musu ba yasa kawai na haqura.
A ranar Juma’ar da muka gama na bi jirgin dare zuwa Lagos.

Kadaran kadahan Bashir ya karbe ni, ban damu ba na shiga sabgogina ina dai ta qoqarin ganin komai ya daidaita a tsakanin mu amma yaqi bada hadin kai sam.

Ranar Talata da daddare bayan mun gama cin abinci Bashir da Aliyu suka fita siyo Biredi sauran yaran kuma duk suka koma cikin palour ni kuma na zauna a Gurin Dining din ina danna waya, kiran Muslim Yaya nane ya shigo wayata, mun dan jima muna magana kafin mukayi sallama yana kashewa Khadija qanwata ta kirani.

Abdallah ne ya taso ya kawo mun littafinsa na quantitative reasoning ya kakare a wani guri daman ina jinsu da yayyan yanata su koya masa kowa yaqi dan haka na saka wayar a speaker muna hirar ina nuna masa.

Hirar wata faccalarta takeyi mun, babansu yana da kudi kamar su kashe shi amma irin matsolon nan ne ba’a cin kudin sa se akayi dace data tashi aure ta auri me kwadayi dan shi dalilin auranta ma saboda kudin baban nata ne.

Tofa tunda akayi aure yaga babu lashi se rashin mutunchin yau daban na gobe daban qarshe ya yiwo mata kishiya ma shine yanzu ba’a dade ba baban nasu ya rasu anyi musu rabon Gado ta samu kudi sosai se kuma ya dawo kamar yaron ta se yanda take so yakeyi har Kishiyar ma yanzu ya mayar mata da ita kamar me aiki kome take so shi za’ayi a gidan nan.

“Wallahi Anty se kin ganshi jiya da mukaje sabon gidan da tayi yana tsaye yanda kika san dan aiki daga tayi motsi ze zaburo yace Hajia me kike so Hajia me za’ayi, ni ban taba ganin meson zuciya irin Rabi’u ba wallahi” Khadija ta fada.

Dariya nayi ina cewa “kudi ake gaya miki huce takaici kenan, ai idan mace ta gawurta zakiga har mijin ma wani shakkar ta yakeyi balle kuma kishiya. Shiyasa kika ga mun dage muna neman su maganin wulaqanci” na fada dai dai sanda Bashir da Aliyu suka shigo, wani kallo dana kasa fassara ma’anarsa ya yimun kafin yasa kai ya shige dakin sa.

Hirar mu muka ci gaba sannan mukayi sallama lokacin na gamawa Abdallah Homework din se na tashi daga gurin nima na shiga dakin Bashir.
Qarar ruwa da naji yasa na gane yana Toilet, sena zauna a gefen gado ina jiransa ya fito.

Kudi nake so na ara a gurinsa ina so na qarasa mana siyayyar kayan sallah dan haka nakeyi kafin lokacin yazo na siyi komai idan ya bani kudin se nayi wasu hidimar dasu yanzu kudaden hannuna duk na tattara na bada kudin Umarar Goggo daman Kudin Hayar da zan karba na saka rai dasu to su kuma tun kafin suzo ma na bada Aron su.

Seda na barshi ya gama shiryawa ya zauna sannan nace “Baban Ali Aron kudi nake so dan Allah”.

Shiru yamun ban damu ba na cigaba da cewa
“Kasan na gaya maka zancen tafiyar Goggo to na bada kudin, wadanda kuma nake saka rai na hayar gidajen nan wallahi Yaya Abubakar ya rance wai ya cikawa su Bilal sun tada ginin gidajen su bayan Babbar Sallah nan muke saka ran bikinsu”.

A maimakon ya amsa ze bani ko baze bayar ba se ji nayi yace “Lallai Ma’u karanki ya isa tsaiko.
Wato ban isa ki tambayeni kudi ba sedai kice na ara miki ko? To bari kiji ni ba sakaran namiji bane da har kike tunanin dan kina riqe wasu yan kudade zaki fi qarfina, inaji har fada kikeyi kudi maganin wulaqanci idan mace ta gawurta miji zeyi shakkarta to bari kiji ko kin fi Dangwote kudi ina nan a matsayin mijin ki kuma baki isa na biki ba.

Daman tunda kika fara aikin nan naga halayenki da yawa sun chanza, saboda zan fita nema kema ki fita kina ganin kanmu daya ba? to ya zama dole zan dauki mataki, ki fara shirin ajiye aikin nan”.

Kamar sokuwa haka na ringa binsa da kallo har ya gama magana. Dan Allah meye laifina anan? Daga neman rancen kudi shine ze tado wadannan maganganun haka.

Sena sake matsawa kusa dashi ina cewa

“Yanzu saboda Allah Baban Ali rashin tambayar ka kudi da nakeyi ashe nan ma laifi nake ada da nake tambayar ka kuma cewa kayi ai na ishe ka da bani bani kai bakaga amfanin Kasuwancin da nake yi ba wai dan Allah me yasa ba’a maka gwaninta ne??

Kuma ni a yaushe kaji nace nafi qarfin ka ko ina so ka bini idan dai ba neman tada zaune tsaye ba daga ji mutum yana waya se kace dakai ake baka san hawa ba baka san sauka ba.

Maganar aiki ko kuma wani kudin daban da nake samu kasan idan da tarawa nakeyi da yanzu na kai inda nakai wallahi amma ko na samu jikinka suke komawa tunda kafin na amfani kaina da biyar na amfana wa yaranka da dari. Yaushe rabon da ka dauki sisinka ka bani da sunan wata hidima tawa kota yaran nan?

Siyowar da kakeyi da kanka ma tunda kaga idan ya qare inayi ka sakar mun se sanda ta raya maka sannan zaka siyo ko ka bada kudi a siyayyar.

Idan ba sallah ba na manta rabonda yau Baban Ali ka kawo dankunne kace gashi wannan naki ne kuma kullum kana ganina da sabon abu amma baka taba tambayata a ina na samu ba duk ba sauqin ka bane, idan da bani da abinyi ai duk nauyin a kanka suke”.

“Oh gori zakiyi mun kenan daman ni nace ki ringayi ko ke kika dorawa kanki?
To ki dena, daga yau karki sake saka silenki a hidimar gidana kota yayana ki gani idan bazan iya ba” Ya fada a fusace.

Haka kawai naji zuciyata ta karye wani kuka yana neman taho mun, wai me zanyi na burge Bashir a rayuwa ne? Duk abinda nayi aje a dawo wata rana se ya zama abin fitina, seda na dauke hawayen daya zubo mun akan fuskata kafin nace

“Ko baka fada ba nima bazan sakeyi ba idan yaso seka gani in abin kirki nake maka ko akasin haka” daga haka naja bakina nayi shiru ina goge hawayen da suke zuba daga ido na dan na kasa hana su fitowa.

Meyasa maza ba’a iya musu a rayuwa ne? Idan kika zauna baki nemi na kanki ba a goranta miki idan kin tashi kin nema shima baki tsira ba to ya ake so kayi?

Wayar sa ce ta katse mana shirun da mukayi se ya daga yace “zan kiraki” kafin ya kashe.
Ina lura da yanda yake satar kallona yana zuba tsaki se na dena goge hawayen na barsu kawai suna shata se ya miqe gaba daya ya bar mun dakin yana fita kuwa na fashe da kuka me sauti harda sheshsheqa.

Bashir
Gaba daya jikinsa yai sanyi da ganin hawayen nata, shi da kansa yasan be kyauta sam Asma’u bata cancanci wani abu a gurinsa ba bayan kulawa da tattali amma dole tasa kashi yin koma menene dan a nasa ganin an fara dakko sare sarin da zata fi qarfin nasa saboda sam ada ai ba haka take ba.

Idan ya gaya mata magana tana ji amma yanzu abinda tasa a gaban ta kawai shi takeyi. Bata yij shawara dashi sedai kawai ta gaya masa zatayi abu kaza in aka ci gaba da haka ai wataran ma se tayi sannan ze sani dan haka ya quduri niyyar kawai ta aje aikin nan tunda shi yake sake bude mata ido tana hulda da manyab mutabe tana ganin rayuwa kala kala.

Kwana biyu a tsakanin gaba daya na dauke masa wuta na fita a sabgarsa na kuma qudurce a raina yar biyar dita Bashir baze sake ci ba. Dakansa ya sakko ya ringa neman shiri dayaga yanda na watsar dashi seda na gara shi kuwa sannan na haqura amma fa ba wai na chanza ra’ayi ba jira kawai nake wata yayi na fara tatike Aljihun Bashir.

Sati biyu tsakani wata ya qare kuma a satin nasan zeje Gombe, ina sane na zauna na rubuta uban list kai harda abinda muke dasu seda na rubuta na hada total dina kusan dubu dari da Ashirin, ana gobe ze tafi ina jinsa yana mitar an qara kudin jirgi seda ya gama na miqa masa takardar ina cewa

“Ga wannan karna manta ka tafi, na manta Gas din mu ya qare shima qaramar cylinder da tayi saura ita aka saka jiya sannan lemon yan makaranta da Biscuits suma babu na manta ban rubuta”.

Takardar ya karba ya duba se ya dago ya kalleni yace “Wannan kudin duk na menene haka kusan dubu dari da Ashirin?”
Chapter 55 · 0% Book details