← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 158

Sashe 141

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Malama ba dake nake ba, ke ko kunya bakya ji ki ringa shigo da qarti cikin gida kina tara zawarawa Saboda rashin kamun kai tunda ke baki san daidai ba to ni dole na kare martabar yayana dan bazaki lalata musu tunani su dauka abinda kikeyi daidai ne ba, kai kuma tashi ka fita idan ba haka ba se kayi dana sanin zuwan ka gidan nan yau" Bashir ya fada cikin fitar hayyaci da kishin da yake cin zuciyarsa.

"Ni kake kira mara kamun kai Bashir nice mara Tarbiyya?" Na fada ina nuna kaina saboda yanda maganar sa ta dakeni, ban fito daga jimamin ba naji yace

"Na fada, wace mace ce zata ringa shiga da Namiji gidanta a kirata me kamun kai? To bari kiji, idan ma kinayin haka ne danki bata mun tai kinyi a banza saboda na tabbatar miki duk wadanda suke rudar miki da tunaninba auranki zasuyi ba. Ni din dai nine duk ma inda zakije ki dawo ina zaune sekib dawo mun dan na tabbatar har duniya ta nade bazaki taba son wani abu bayan ni ba Ma'u idan kuma nayi qarya to ki fda muji".

"Tab Allah Nagode maka daba ka bani damar aikata aikin dana sani ba" na fada a zuciyata kafin na koma kan kujerar dana tashi na zauna ina qoqarin yaqi da maganganun da Bashir ya yaba mun ni Asma'u ya kalli tsabar ido na ya kirani da mara kamun kai lallai Bashir ya isa tabbataccen mara mutunci.

Yusuf daya harde hannu yana kallonsa ne ya bude baki zeyi magana nayi saurin dakatar dashi da cewa

"Ka zauna, mema nake ce maka ne kafin ya shigo?" Na fada fuskata dauke da murmushi, zama yayi shina yana mayar mun da murmushin yace

"Ina jinki, wannan albishir din da kika ce zaki mun fadi ina jinki".

"Oh ga mahaukaci yana magana shine dukkan ku zaku mun shiru ko? Malam tashi ka fita ke kuma Ma'u zaki san ni kike wulaqantawa akan wani can dan iska da be san darajarki ba" Bashir ya fada a haukace kamar ze rufe mu da duka.

"Ko dai mu bari anjima na gaya maka a waya? Kaga yanzu akwai hayaniya bazata barmu mu tattauna da kyau ba kuma maganar tana da buqatar nutsuwa sosai" na fada ba tareda na mayar da hankali akan shirmen Bashir ba

"Aa muje waje toh ko cikin mota dangaskiya kika ga na tafi ba tareda naji dalilin kiran nna ba toh inaga yau bazan iya bacci ba"

Dariya nayi na miqe ina cewa
"Gaskiya dai muje nasan ko ka ji din ma duk haka take be zama lallai ka iya bacci ba yau" fizgoni da akayi baya yasa nayi shiru ina gama daidaita tsayuwata kuwa na kwashe shida mari a mugun fusace nace

"Rashin kamun kan nawa be kai kowanne gaja ya ringa dora qazamin hannunsa a jikina ba" na waiwaya na kalli Yusuf da yanayin fuskarsa ya chanza zuwa matuqar bacin rai nace

"Yusuf bazan iya magana yanzu ba saboda raina ya baci, kaje kawai ka gayawa Alhaji Qarami sati biyun daya saka sunyi yawa a mayar dashi Juma'ar nan me zuwa"

"Bangane abinda kike nufi ba Asmy? Me za'a dawo dashi wannan juma'ar ko daurin auran mu kike nufi?" Ya shiga jero mun tambayoyin a rikice, wani mugun kallo na jefawa Bashir daya dafe kunci yai mutuwar tsaye nayi kafin nace masa

"Haka nake nufi ko yayi maka wuri da yawa.." kafin na idar da maganata ya kife a gurin yayi sujjada ya dago cikin wata kalar madaukakiyar murna ya riqo Bashir yana cewa

"Nagode Nagode Bashir ka gaya mun dame zan biyaka a rayuwa? A da na dauka a matsayin babban abokin Adawa ashe ban san banida masoyi sama dakai ba tunda gashi kayi silar da zan mallaki muradin zuciyata.

Kai na rantse ka shirya samun double promotion, a ina kake aiki? Koda yake barshi zan binciko da kaina" seya sake shi ya juyo ya kalleni

"Wife! Ina fatan wannan hukuncin ya zama mafi Alkahirin hukunci da kika taba yankewa a rayuwarki bari naje zamuyi waya" ya kwasa da gudu kamar yaro ya fita, seda naga rufe qofar sa kafin na juyo kan Bashir muka hada baki ni ina cewa

"Fitar mun daga gida kafin nayi maka tijarar da baka taba zato ba dan daman saboda shi na daga maka qafa kar nayi abinda zan zubar da mutunchi na a gabansa"

Shi kuma yana cewa
"Aure zaki daura da wani namiji nan da sati daya Ma'u? Dagaske zaki iya rayuwa da wani bayan ni? Nasan kinyi ne dan ki baqantamun rai na yarda amma ki janye dan girman Allah.

Bana nufin duk abinda na fada subutar baki nayi da kishinki da yake damuna amma kema kinsan ba abinda nake nufi ba kenan" ya fada yana durqusawa kamar ze kamo qafafuna.

Juyawa nayi ina cewa
"Karka ja nayi abinda yayanka zasu tsaneni Bashir tunda sauran mutunchin juna a tsakanin mu ka fita, badai ni ka kira mara kamun kai ba? Ka jira na fito daga daki yau zan nuna maka qarshen rashin kamun kai kaji ko" na shige dakina ina tunanin me zan aikatawa Bashir da zan nuna masa bashi kadai ne saitin kansa yake gocewa ba, nima wani lokacin nawa notinnan suna tabuwa.

Posting se baba ta gani 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page. 61

AMIRAH A DAREN JIYA

Se dare Bashir ya koma gida har sannan tana nade tana jiran yazo ya rarrasheta. Bayan sallar Isha ya shiga lokacin ta gaji ta fito palour tana zaune tana kallo ga yunwa tana ji amma ta kasa tashi ta girka abinda zata ci, jira takeyi ya dawo se suje su siyo abinci.

A sake ya shigo gidan tayi masa sannu da zuwa ya amsa kafin ya ajiye ruwan dispenser daya siyo ya dawo palour ya zauna yana cewa
“Kawo mun Abinci yunwa nake ji”.

Seta tsaya tana raba ido, wane abinci kuma yanzu ita da take jira ya dawo su siyo shine ze zo yana wani tambayarta dan haka ta gyara zama a shagwabe tace

“Nima fa Yaya yunwa nakeji, kai nake ta jira tun dazu ka dawo se muje muci abincin”.

“Saboda babu kayan girki a gidan nan ko kuma baki da hannun da zaki dafa ko yaya?” Ya fada cikin muryar bacin rai, zata qara magana ya daka mata tsawa yana cewa

“Ki wuce ki samar mun abinda zanci Yanzu bana son bata lokaci, sannan daga yau ma idan zakiyi girkin dare ki ringayi tareda yara anan zasu ringa cin abinci”.

Harta miqe ta koma ta zauna tana cewa
“Wane Yara zan ringa girki dasu ba a gidan su suke ba sannan kuma ni zan ringa musu abinci gaskiya bazan iya ba”.

“Ba wai shawarar ki na nema akan zakiyi ko bazakiyi ba umarnine tunda gidan ubansu ne dole ki dafa abinci ki ajiye musu ko bazasu ci ba, kuma kitashi ki samar mun abinda zanci yanzu karki bata mun rai”.

Miqewa tayi ta tafi Kitchen din tana mita “haka kawai wallahi babu dan da zan yiwa girki yaran ma suna gurin uwar su ace ni zan basu abinci wannan ma bame yuwu ba bane ai”

Haka ta dora ruwa ta saka kwai guda biyu sannan ta dora wata tukunyar ta hau dafa musu Indomie, a maimakon ta jajjaga attaruhu ta zuba se kawai ta saka dakakken Yaji ko Albasa bata saka haka ta zuba masa a plate da kwai kwalli daya a gefe ta saka fork ta kai masa.

Akan centre table ta ajiye, ta koma ta dakko masa ruwa da lemo sannan ta dakko nata abincin harta fara ci sannan Bashir ya fito daga dakinsa ya chanza kaya da alama wanka yayi.

Seda ya zauna akan kujera kafin ya kalleta yace “Ina abincin nawa?”

“Gashinan tun dazu na gama baka fito ba Allah yasa ma bata huce ba”.

Wani kallon banza yayiwa farantin da abinda yake ciki kafin ya saka hannu ya dauka ya tona Indomin da cokalin ciki yana kallonta yace

“Ni zanci wannan abun? Meye wannan kikayi? Idan ma Indomin zaki dafa haka akeyi duk kayan hadin da suke a cikin Kitchen kika gagara sakawa shine zaki kawo mun abu kamar na yan birsin ga wani kwai guda daya akai”.

“Wallahi Yaya ka fiya qorafi kaci mana kaji ai tayi dadi ba gashi ni har na kusa gama cinye tawa ba kuma wane hadi za’ayiwa Indomie bayan wannan harfa yaji na zuba a ciki dan tayi dandano....”

A mugun zuciya ya wulla mata farantin Indomin Allah ya taimaketa be qarasa kanta ba ya fadi a qasa ya tarwatse abinka da tangaran, a tsorace ta kalle shi, ya miqe yayi yo kanta se kuma meya tuna ya kaiwa Iska naushi kafin ya zari key din motarsa yana cewa
“Allah yasa na dawo na tarar da gurin nan a haka” ya juya ya fita.

Badan tana tsoron abinda kaje ka dawo ba babu abinda ze sakata gyara gurin haka ta dakko tsintiya da mopper ta kwashe fasashshen tangaran da Indomin ta kai shara kafin ta saka ruwa ta goge gurin.

“Haka kawai mutum se baqar zuciya kamar kuturu ina laifina dan Allah dama na dafa, ni da yasan baze ci ba se ya bani na qara dan ban qoshi ba yanzu ya wa mutane Asara aikin banza kawai” haka dai ta gyara gurin tsaf ta wuce dakinta ta fada wanka, tana fitowa ta shiga shiri shafa wancan goga wancan ta gama ta saka wata hadaddiyar Night gown ta gyara gashinta tsaf ta wuce dakin Bashir dan har ga Allah a matse take.

Tana kwance tayi daidai tana chatting ya shigo dakin fuskar nan kamar hadiri, to jiki da jini gashi daman kwana ya dade rabonsa da abin dole ya ajiye fushi suka raya sunnah kafin sukayi baccinsu cikin salama dukda seda a ka kusa sake wani fadan da yace taje tayi wanka tace seda safe, dataga yana neman bata mata farin cikin data samu dole tayi wankan suka koma sukayi bacci.
Chapter 141 · 0% Book details