← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 158

Sashe 53

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zabure ya kwalalo ido waje yana kallona yace “Hotona Ma’u? Waye ya dauke mu?”

“Oh ta tabbata kenan ka aikata, kana zaton Asirinka ze rufune? Toh Allah ya tona ka na gani kuma mutanen duniya ma sun sani duk me maka kallon mutumij kirki ka zubarwa da kanka mutunchi a gurinsu” na fada wasu hawaye masu zafin gaske suna zubo mun, Se ya sake matsowa yana qoqarin riqe ni yace

“Ya isa Ma’u karki tayar da yara a bacci ki bari muje daki zan gaya miki komai ba abinda kike zargi bane wallahi”.

Wani banzan kallo na watsa masa kafin nace “Dawa zakaje dakin? Idan kaga na dara daga nan toh ka gayamun wace yar iska ka ajiye a hotel yara kuma ai bakayi tunanin su ba kaje kana zubar musu da qima kana raba musu abin gori a gari”.

Duk yanda Bashir yaso dana sassauta na zauna muyi maganar qi nayi, gani nake yama raina mun hankali tunda alama ya nuna maganar Gaskiya ce dan da nace naga hotonsa ai be musa ba abinda ya qara dagamun hankali kenan na shiga rusa kuka ina cewa “Ka cuce ni Bashir ka cuce ni idan har mugun halinka ya shafi yayana bazan taba yafe maka ba”.

“Wallahi Asma’u ba abinda kike tunani bane ta yaya tun da quruciyata ban nemi matan banza ba se yanzu da girma ya fara kamani na tara iyali? Ku biyu fa nake da ku wace ni’ima ce Allah beyi muku ba da zan fita waje na nema?”

“Ita waccen din da ka ajiye qanwar uwarka ce kenan” na fada a mugun fusace nayi kansa dan rainin hankalin nasa kuma ya fara yawa, ganin da yayi na taho gadan gadan se ya matsa yana cewa “ba wata bace Ma’u Amirah ce, wallahi Amirah ce tazo nasan bazaki yarda ki sauketa a gidan nan ba shiyasa na kaita Hotel”.

Wani burki naci tareda qamewa a inda nake ina rarraba ido tsakanin idonsa da bakinsa, so nake na tabbatar da abinda kunnena yaji ko kuwa ba daidai bane, se ya matsoni yana sake cewa “Amirah ce tazo wallahi tun last week Sunday, nima ban sanda zuwanta ba seda ta sauka tace mun gata a Lagos, ban san yanda zaki dauki maganar ba shi yasa na kasa fada miki wallahi amma gobe ma zata tafi”.

“Bashir dakai da ita kuje Allah yayi muku yanda kuke mini” na fada cikin wani irin sanyi kafin na juya na shige dakina kfain ma ya biyoni na sakawa qofar key. Kan gadon na fada na fashe da kukan da ko mutuwar Mahaifina banyi irinsa ba.

Kuka ne na zallar baqin ciki da takaici wannan wane irin abu ne? Anya Bashir yana da hankali da tunani kuwa, yana lissafi kafin ya aikata wani abun?

Idan ya gayamun Amirah zata zo me zanyi, kai ko be fadamun ba ina zaune ta shigo gidan na ya zanyi da ita ai gidan sa ne kuma ko bata auran Bashir ita me iya zuwa gidansa ta zauna ce amma shine ze dauketa ya kaita Hotel ya ringa satar hanya yana zuwa mutane suna ganinsa yanzu Allah kadai yasan mutum nawa suke masa kallon Fasiqi ya ajiye farka a Hotel.

Inajinsa yana buga qofar yana magiya na bude amma nayi banza dashi na tashi nayiwo alwala nayi na tada sallah ina yi ina kuka ban idar ba seda aka fara kiraye kirayen Asuba, ina idar da Sallar Asuba kuwa wani wahalallen bacci ya kwashe ni da ban farka ba se sha biyun rana shima qiqi qiqin da ake da qofa ne yasa na bude ido na.

Ina dafe da kaina dayayimun nauyi na nufi qofar jin surutan mutane kamar ma ballata ake so ayi se na murza key din naja baya ganin yanda Bashir ya fado kamar an cillo shi, a bazata ya rungumoni ban yi wata wata ba kuwa na hankadashi da dukkan qarfina yai baya Allah ya taimake shi bango ya tare shi, ina kallon securities din daya gayya toh suka juya suka tafi.

Be daddara ba ya sake nufo ni yana cewa “Ma’u lafiya kike tun jiya kin kulle qofa babu irin bugun da banyi ba gaba daya kin tayar mana da hankali ga yara can se kuka sukeyi”.

Tsaki nayi na juya na cire Hijabina na shige bandaki na bar shi a tsaye a gurin, sanda na fito baya nan, riga kawai na zura dan banida nutsuwar da zan saka komai a jikina, bakina har wani daci yake mun saboda bacin.

Lokacin da na fito Suna zaune shida Matarsa da ban san sanda tazo ba sunyi tsuru kamar masu jiran Sadaka. Kallo daya nayi musu na wuce Kitchen inajinsa ya taso ya biyo baya na seda muka shiga ciki sannan na waiwaya na kalle shi nace “kasan Allah ko ka fita ko kuma ka kalli nan (na nuna masa bangaren da wuqaqe suke) gasu nan kala kala in ka qureni se nayi maka aika aika na huta da takaici” ai kafin na qarasa fit ya fice daga Kitchen din duk yanayin bacin ran da nake ciki seda nayi dariya sosai dan dagaske ya tsorata.
“Allah ya tsare ni da irin wannan zuciyar” na fada a fili kafin na zuba ruwa a kettle na kunna kafin ya tafasa na hada kayan shayi a babban kofin dan bazan bari baqin cikin Miji da kishiya su naka sani ba.

Shayina me kauri na hado na zubo dambun nama a bowl na dakko ledar biredi, kamar bansan da tsurom mutane ba haka na nemi kujera na hakince sannan na kunna Tv ina shan shayina ina kallo.

“Ma’u ga Amirah kin ganta wallahi ita ce ba wata daban ba na yarda nayi kuskure tun farko da ban sanar miki da zuwanta ba amma kiyi haquri”.

Yanda yai maganar kamar wanda yayi wa babarsa wani qundumemen laifi yazo bata haquri harda wani zamowa qasa saboda tsabar iya sharri ga muryar sa har rawa take yasa na kalle shi, seda na cinye biredin dana tura a bakina na kora shayi sannan cikin dan murmushi nace

“Oh wannan be ishe ka ba kenan seka qulla mun sharri a sake tafiya dani a baki ace na mallake ka har durqusamun kake ba?
Ni tunda nake dakai ma ka taba bani haquri ne amma da yake yau kana so ka qaramun baqin jini shine kake duqawa ai shikenan, ni na gama magana ta tun jiya duk abinda mutum yayi mun na barshi da Allah” daga nan na ci gaba da cin abincina ina jinsa ya qaraci naci da magiyar sa amma tafi ka mutu bance masa ba.

Amirah da ta shaqa tayi tam daman ga takaicin dakko ta dayayi tun da sassafe ya ringa surfa mata ruwan masifa ga abinda ta janyo masa nan ana yawo dashi a gari an ce ya ajiye karuwa ya taso ta a gaba wai tazo su bawa Ma’u haquri tun bakwan safe take zaune se yanzun dana fito ga wannan Dramar da yakeyi kuma har wata kwallar takaici ce ta taru a idonta. Cikin muryar bacin rai tace

“Ni Yaya ka dakko ni tun safe ko wanka banyi ba bare naci abinci gashi yanzu Azahar tayi gaskiya ni yunwa nake ji”.

“Waya hana ki kici abincin ai gaki ka Kitchen nan duk bake kika jawowa mutane ba” ya hayayyaqo mata, seta miqe zata tafi Kitchen din nayi sauri tare ta da cewa “Ji mana, karki shigar mun Kitchen malama ku koma can inda ya aje ki ki nemi abinci ba’a nan ba” ban qarasa cinye biredi na ba na daure ledar kawai na kwankwade shayin na tashi. Seda na kullo qofar Kitchen din da mukulli na zare kafin na shige dakin su Aliyu na bar Bashir da Amirah baki sake suna bina da kallo.

Aliyu da Jafar na zaune da alama duk suna jin abinda yake faruwa se nayi murmushi na zauna ina cewa “me kuka bawa yan biyuna har yanzu basu tashi ba?”

“Game sukayi tayi Mami basu kwanta da wuri ba jiya dakyar suka tashi dazu suka ci abinci ma” Jafar ya fada. Whatsapp na bude a wayata ina shiga message din Maman Shukra ya fado nayi murmushi na bude
“Maman Farida ina fatan dai bada tashin hankali kika tunkare shi ba ko, kinsan fa irin wannan abun se a hankali da Addu’a kuma in ba haka ba a maimakon a samu sauqi se ka qara tunzura mutum” ta rubuta, se na mayar mata da cewa

“Ai baki sani ba, ashe Amaryar sa ce tazo sh ya sauke ta acan kin gansu tun dazu ya dakko ta tana nan”.

“Tab amma se abar Engineer, to ke me kakace yanzu?”

“Me zance kuwa, gasu can na barsu a palour ni ina daki ma bacci zanyi se anjim mayi magana” na fada dan na datse hirar.

Alawiyya yayata na duba naga bata online, fita nayi daga dakin na koma nawa dan ina so na l kirata, sanda na fito palour Bashir kadai na tarar har na wuce na yi kwana na shiga dakinsa. Addu’a nake Allah yasa tana ciki yau na gwada musu danyan kai daga shi har ita se Allah ya temaketa babu kowa har Toilet na duba bata ciki na kullo qofar na fito se ya tare ni yana cewa

“Ta tafi gidan Ghali daga can gobe seta wuce Gombe” (Ghali dan wan Baban su Bashir ne).

Wunin ranar zir haka yayi shi a palour daya ji motsina ze taso yana so yayi mun magana amma naqi bashi fuska sam da daddare ina jinsa suna waya yana ta masifa nidai qala bance masa, daya biyo ni dakina ma abinda tun tsahon zaman mu a gidan nan be taba kwana a ciki ba yana kwanciya na juya mukayi kai da qafa yana fita sallar Asuba kuma na saka Key.

Haka muka cinye satin, har zuciyata na huce kodan irin ban haqurin da ya ringa yi mun amma ban nuna masa ba, yanzu dai ina dafa abinci dashi kuma in yayi mun magana ina amsawa sakin fuska ne dai babu na kuma dena shiga sabgarsa sannan na koma dakina da kwana kullum kuwa se ya bini.
Chapter 53 · 0% Book details