← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 158

Sashe 109

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Idan kika sake cewa wani abu se kinci ubanki Amirah, bazaku kasheni ba yanzun nan zan turo miki da akawun na fasa zuwa POS din ma zan shiga gidan Talatu kawai mu zauna a can zuwa lokacin da zamu koma idan yaso se na turo miki da ko na Dan ta ne ki saka kudin nasan in muka koma gida wannan Uban naku ba lallai ya sake barina na fita ba” tana gama fadar haka ta kashe wayarta tana aunawa Amirah Ashar shidai me Napep se leqenta yake ta mudubi Allah Allah yake ya sauke su ya samu wanda ze bawa labari.

Amirah kuwa tana jin Addah ta kashe waya ta shiga neman layin Babansu, yana dagawa kai tsaye ta gaya masa Addah na gidan Anty Talatu ta kashe wayar tana Addu’ar Allah yasa Babansu yaje kafin su Addah su koma inda tace.

Addah kuwa a gidan Anty Talatu suka yada zango, yar uwarta ce yayan mata suke yar bala’i ce ta gaske itama dan har tafi Addah rigima.

A tsakar gida suka tarar da ita tana wa wata jikarta masifa, ko sallamar Addah bata amsa ba seda taji yarinyar na gaida Addan sannan ta waiwaya inda suke tana huci.

“Aa Fattu kune a tafe? Ku shigo mana ita kuma wannan me aka mata ta dora hannu aka tana kuka? Nifa bana son fitina shiyasa kikaga bana qaunar baqar yar nan taki saboda mugun halinta gara Amirah tafi mun ita sau dubu”

Cikin dakinta suka shiga tana gaba suna binta a baya. Seda ta kawo musu ruwa me sanyi da Fura, ta futa ta bawa jikar tata kudi tace taje qaro taliya leda daya dan gama miyar ta kenan sun maida ruwan taliyar yarinyar ta juye tayi wanka dalilin masifar tata kenan.

“Daga ina haka Fattu da uwar ranar nan fatse fatse keda bakya gajiya da yawo” Talatu ta fada bayan data zauna.

Se Addah ta janye tagumin data buga tace “ki bari kawai Talatu wannan yarinyar ce ta kwaso mun tashin hankali” nan ta zayya na mata abinda yake faruwa.

Anty Takatu ta hau salallami tana tafa hannu tace “yanzu Ummin? Ke da nakeyiwa kallon ta kirki kai yaran yanzu se abarku abinda se dai muji daga nesa shine kika kawo mana a cikin zuri’ar mu Allah ya wadaranki dai Ummi”

Nan suka hadu suna ta nanata zancen, seda ta dafa musu taliyar suka ci kafin Anty Talatu ta kalli Addah tace

“Ni Fattu maganar zubar da cikin nan ki barta kina gani dai ance mutuwa akeyi wallahi, yanzu abinda duk ya kamata ayi shine tunda tasan uban ciki a nemo shi a taru a rufawa juna asiri ko yaya ne ayi musu aure shikenan”

Hayayyaqo mata Addah tayi tana cewa
“Ban gane abar ciki ba in barta ta haihu kenan a ringa nunani a gari ace nayi jika shege to bazata sabu ba wallahi, kuma zancen aure da kije badai da wannan matsiyacin ba sedai idan mutuwa nayi”

“Ai kuwa idan baki mutu na zakiyi ta goya shegu tunda ke zuciyarki irin ta kafiran farko ce. Yanzu tashi zakiyi mu zagaya nan baya gidan me sittin tara a kwantar da cikin daga nan a nemo yaro idan sukayi aure wata kadan se a tayar dashi dukma uban da za’a fada dai daga baya ne tunda sun rigada sun yi aure”.

Shiru Addah tayi qasan zuciyarta ta yarda da shawarar Anty Talatu, miqewa sukayi Anty Talatu tace Ummi ta shiga ciki ta hau gado ta huta kafin su dawo suna zuwa qofar gida sukaci karo da yan sanda a tsatstsaye.

“Lallai Asabe, ba nace ta bani sati daya zan biyata kudin ta ba shine zata hadani da hukuma ai kuwa wallahi tayi ta kudinta muje duk uwar da za’ayi ayi amma bazan biyata ba kuwa” Anty Talatu ta fada dan a zatonta wata mata da rigimar Adashi ta hada su tace zata dakko mata yan sanda ce ta turo su.

Fitowar a Alhaji Murtala daga mota ce ta dakar dasu Addah ta shiga zare ido tana komawa bayan Anty Talatu.

“Gata nan yallabai” ya fada yana nuna musu Addah nan da nan yan sanda mata biyu sukayi kanta se ta sake riqe Talatu tana cewa

“Me kuma nayi Alhaji? Wane munafunchin aka qullamun da zaka dakko mun yan sanda saboda ka tozarta ni”

“Ai kin rigada kij gama tozarta kanki Fattu, ina Yata take? Se na tabbatar da lafiyar ta idan wani abu ya sameta daga nan kotu zamu wuce dan se nayi shari’a dake Fattu” ya fada cikin tsananin dacin rai.

Anty Talatu ce ta tare yan sandan da suke neman jan Addah tana cewa
“Ummi tana ciki Alhaji lafiyarta qalau, bari na kirawo maka ita ka ganta wannan kuma ai abu ne na cikin gida be kamata ace ka saka hukuma a ciki ba”

Daga bakin soron gidan ta tinga kwalawa Ummin kira, Ummi da har bacci yadan fara fizgarta ta fito jin muryar Talatun tana fita tayi arba da Baban su seta fada jikinsa ta fashe da kuka tana cewa

“Dan Allah Baba kar ka bari ta kaini a cire mun mutuwa ake yi ni kuma bana son na mutu”.

Riqeta yayi sosai a jikinsa zuciyarsa na tafa sa, tausayinta ya cika shi ya tabbatar duk abinda ya sameta qaddara ce da kuma halin Fattu ya janyo.

Cikin bacin rai ya kallo yan sandan yace “ku rabu da ita tunda naga Yata kuje kawai zan zo station din anjima na gode”

Sukayi masa sallama suna harar Addah sukaja mota dan sun so sun samu damar moreta.

A motar sa ya saka Ummi ya zagaya ze shiga Addah ta biyo shi ba ko dar tana cewa
“Bari nazo mu tafi Alhaji, Talatu se munyi waya ko zan kiraki idan naje gida”.

“Idan kinje wane gidan? Da alama baki ji saqona ba kenan” Alhaji Murtala ya fada yana dakatawa daga shiga motar da zeyi, Addah ko qoqarin bude mota take tana cewa

“Saqon me kuma wa ka bawa ya bani? Ni ba’a ce mun komai ba”.

“To bari na gaya miki yanzu da kaina, na yanke igiyoyin aurena biyu da suke kanki, ma’ana na sake ki Fattu saki biyu”

“Alhaji ka sake ni fa kace kuma har saki biyu? Uku fa kenan ko ka manta akwai daya daman?” Addah ta fada cikin ihu tana ja da baya hannunta aka, seda ya shiga motar ya danna lock kafin yace mata

“Ina sane Fattu na gaji da halinki na dade ina Addu’ar Allah ya yakice mun ke se yanzu ya karbi Addu’ata, zan ma aiko miki dashi a rubu ce saboda shaida” yana gama fada yaja motar sa Addah kuwa kamar sabon kamu ta bishi da gudu tana ihun ta shiga uku ta lalace.

*SODA COMMUNICATION📱💻📱
*CHEAPEST & RELIABLE DATA SERVICES*💃🏽💃🏽 with the validity of 30days at affordable price we are available 24/7 08137145294

*MTN DATA*
1GB@280✅
2GB@550✅
3GB@850✅
4GB@1150✅
5GB@ *1400* ✅
10GB@2800✅

*AIRTEL DATA*
1gb@320✅
2gb@640✅
3gb@950✅
5gb@1600✅

*Pay through👇🏽👇🏽*UNION BANK*
*0139814463
Khadija shehu soda*🥰🥰🥰we are always there at ur service. WhatsApp/Call📞08137145294🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 51

Seda motar Alhaji Murtala ta bacewa Addah kafin ta tsaya tana haki ta dora hannaye biyu akai tana rusa ihun ta shiga uku ta lalace

“Ni Murtala ze saka? Shekara Hamsin da aure ace zanyi zawarci gidan ubanwa yake so naje yanzu wallahi be isa ba, ban saku ba dole na koma” Addah ta ringa sambatu tana rusa kuka.

Anty Talatu ce ta ruqota suka shige gida tana cewa
“Se kace kanki aka fara saki ji yanda kika bishi da gudu kamar wata karya. To Fattu ai ya miki da kyau ma daya tsaya a iya sakin dan ni na dade ina hasaso miki haka a irin tashin hankalin da kika dade kina kwasowa bawan Allahn nan. Ni da ban kaini Jaye jaye bama aka sake ni bare ke? Kawai muje ki share guri ga daki nan na kusa da nawa ki shiga ki zauna Allah ya kiyaye na gaba”.

Kuka sosai Addah ta ringa sharba se kace qaramar yarinya. Anty Talatu tun tana bata haquri har abin ya bata haushi ta tashi qarshe ma ta fice gaba daya ta bar mata gidan ta tafi karbo zubin Adashen mutane dan ita uwar Adashe ce.

Se bayan Magriba ta dawo gidan, lokacin Addah tayi kukan ta dangana, dukda ba haqura tayi ba ta bari ne zuwa gobe da safe zata koma gidan ta idan Alhaji yaqi kuma zata bi Aminansa da yan uwa a saka baki dan bazata iya barin gidan nan ba.

Toh ta kama ina dan zaman ta da Talatu tasan ma ba me yuwuwa bane kawai dai zata zauna na dan lokaci kafin komai ya daidaita.

Tana kan sallaya bayan ta idar da sallar Isha Talatu ta shigo tana ta masifa akan matan sunqi bada zubi. A qofar daki ta zaune kan taburma, Addah ta leqo kamar wata me takaba murya duk ta dashe saboda kuka tace

“Talatu se yanzu? Tun dazu nake zuba ido na jiki shiru ga duhu seda wannan yarinyar ta dawo ta kunna mun fitila”

“Ba dole ki ganni yanzu ba Fattu, Mata saboda bala’i sun qi bada zubin Adashi ai basu isa ba, gobe dirar Asuba zan wa kowacce kafin mijintavya fita sedai ayi wacce za’ayi”.

Guri Addah ta samu kusa da ita ta zauna ta rafka uban tagumi, ga damuwar saki ga Yunwa tana sakadarta dan ita sam bata da jumurin Yunwa.

Shinkafa Talatu ta sake dora musu suka ci da miyar dazu kafin suka kwanta tana ta jan Addah da hira dan ta saki jikinta amma ina tayi shiru idan ka ganta bazaka ce wannan Addahr bace yar rigima.

Washe gari Asubanci tayi ta tafi gidansu Amirah, a qofar gida suka ci karo da Alhaji Murtala yana tsaye kamar daman jiran zuwanta yake yi kanta a qasa ta shiga gaishe shi ya dakatar da ita da cewa

“Lafiya Malama? Me kika zo yi mun a gida?”

Gaba daya yau se taga yayi mata wani kwarjini tsoronsa ma taji tanayi, murya a rarrabe tace masa

“Dama, am dama Alhaji kayan sawa ta nazo dauka”.
Chapter 109 · 0% Book details