← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 158

Sashe 7

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kuwa samu yanda take so dan nan da nan hankalin Dada ya tashi ta shiga son nuna mata ita fa ba abinda take nufi ba kenan,
“Idan har da gaske kike kuma kina so na haqura nida kawai kiyi yanda zakiyi Bashir ya dauki Amira ta koma kusa dashi, kuma baze yuwu yace Ze kwashe su su dukka ya kai can ba se dai ki saka shi ya dawo da daya ya dauki daya idan kikayi haka shine kadai Ze sa na haqura in ba haka ba wallahi ki saka a ranki baki da wata Yar uwa Fatu a raye”

Ita dai Dada son su rabu lafiya ya saka ta amince mata, dole ta hado yan kudaden hannunta dubu 30 ta bata tace gashi nan ta kaiwa Amirar ta riqe kafin Bashir din yazo se a san yanda zaayi haka ta rakata har get Addan na sake jadda da mata fa akan tana nan tana jiran saka mako da haka suka rabu.

Numfashi ta sauke bayan ta dawo cikin palour ta tazauna, gaba daya ta tasa ina zata kama akan wannan al’amarin. Har ga Allah bata so ta sake yin wani kuskuren akan na baya amma ya zatayi da Adda Fatu yar uwarta tilo a kaf fadin duniyar nan bata da kamarta. Addan tayi mata komai a rayuwa ya kamata ace ita ma ta saka mata da abinda ta mata. A zatonta Auran Bashir da Amira ya isa ga tukuicin kyautatawar amma se yanzu take dana sanin ma aikata hakan domin kamar ta bude wata qofa ce da Addan ta mayar da ita tamkar birin wasanta.

Ko da yaushe cikin daga mata hankali take tunda akayi wannan auran da ita dai bata ga amfaninsa ba in banda bacin rayuka da ya janyo da yawa, shigowar Nazir Autan ta ya sakata dagowa ta kalle shi
“Yanzu na hadu da fitinanniyar yayar ki a hanya seda tayi mun fashin 10k wallahi, gaskiya Dada ki ringa yiwa Adda fada abubuwan da takeyi basa dacewa. A yanzun fa ga kudi a hannunta amma ta tsaya suna fada da Dan Napep dan yace a 200 ze kaita gida”

“Hmm Allah ya rufa asiri kawai Naziru amma ni lamarin Adda ya fara bani tsoro, yanzu ma fa kaji abinda ya kawo ta” tiryan tiryan ta labarta masa yanda sukayi.

“Wallahi Dada ki kiyayi matar nan, ni dai ina ga Asiri take yi miki ma kike wasu abubuwan idan ba haka ba dan ta riqe ki ai ba baiwarta bace ke da kuma zata ringa juya ki yanda taso. Tun farko abinda muka guda a hadin wannan auran kenan amma kika rufe ido kika ce se anyi zumunchin ku ya qara qarfi ko ai gashi tun ba’aje ko ina ba kinzo kina dana sani. Shima Yayan banga qaddarar daya gani a jikin wannan mara mutunchin yarinyar ba daya yarda ya aure ta”

“To Naziru yaya zanyi Adda yar uwata ce da bani da kamar ta ka sani kuma farincikin Yayanta shine nata idan banyi mata ba a rayuwa ta wa zan yiwa?”

“Ai kuwa gashi nan, kafin da ki sake yanke wani hukuncin se ki tuna cewa Auranki kema yanzu lilo yake yi a garin faranta mata kuma baza muso ace Uwar mu ta shiga zawarci a wadan nan shekarun ba” ya fada ya miqewa dan ya fita dan dagaske Bala’in haushin Adda yake ji har ma da Dadan da yake ganin tana biye mata ne.

“Allah ma baze sa ba Naziru zan lallabata insha Allahu babu abinda ze faru ma” Dada ta fada itama tana miqewa dan neman abinda zata ci, ko karyawa batayi ba Adda ta doko mata sammako.

ADDA FATU
Bayan barinta gidan Dada gaba ta qara dan kuwa bazata koma gida yanzu ba dan tuni Amira ta gaya mata matar tazo karbar kudinta gata nan a tsakar gida tana ta zuba Rashin mutunchi akan Adda ta fito ta bata kudin ta sunce mata bata nan amma taqi yarda, gara ta qara gaba ko Allah ze sa ta dace ta samo wani abun koda taimakon da zesa Bashir ya turo musu kudin ne. Gidan Aminiyarta Haj Balaraba ta wuce, ta sami Balaraban a qofar gida an kira mata me Napep zata fita unguwa.

“Fatu daga ina da safiyar nan haka” ta fada tana qoqarin rufe gida.
“Ke zan tambaya Balaraba keda nasan se ki kai 12 ma baki tashi ba”

“Hmmm ta ina Kishiya na neman sabautani ina naga ta bacci, kinga yanzu ya akayi dan ni a tafe nake neman taimako zan tafi” Balaraba ta fada tana jefa muqulli a cikin jaka.

“Ai kawai muje dan nima matsalar ce ta kawo ni ma tattauna a hanya” nan suka fada Napep Balaraba ta fada masa inda ze kaisu. Suna tafiya Adda Fatu na jerowa Hajia Balaraba matsalinta.

“Ni na rasa wane irin shegen yaro ne Bashir wallahi naje gun malaman naje gun Yan Bori amma an kasa cin galaba akansa, ke har fa nafi ganin aikin kissa idan tayi masa akan na asirin nan wallahi dama Da Nafi nake samun yanda nake so a gurinsa to itama naga alamar tana so tayimun Bore. Ga shegiyar me kayan can da kika hadani da ita bashi kamar na masifa na kasa biyanta”.

“Tab ai seda na gaya miki daman ita fa Indo in kaci bashin ta wallahi toshe maka hanyoyin samu yake kika ce bakomai shiyasa kika ni kudi hannu muke sabga da ita gata bata san sabo ba akan dubu daya seta keta miki rigar mutunchi”

“Ai na gani kuwa yanzu haka fa tana can gidan tana ta tijara nidai na ce su Ummi su kulle qofa kar su bari ta shiga bare ta daukar kun wani abun, kudinta Dubu dari biyu yai saura da Mun samu kan Bashir zan tattara na biyata mun rabu kenan”.

“To ai shi wannan yaron fa se kin dage masa gaskiya amma bari muje nan gurin, Maman lurwanu ta kwatantamun tace aikinsa sha yanzu ne dan shi yai mata aiki akan Isah ya saki Kishiyoyinta dukka biyun rana daya yanzu bakiga yanda take shanawa a cikin gidan nan ba ita kadai” cewar Balaraba

“Kice Allah, ashe gara da nayo nan Allah yasa qarshen wahalata kenan (ko kuma farkon wahalar ki ba) in samu ina kafa Amira da kyau sannan in waiwayo kan nawa qananan kwarin ko da yake ni da zaman su da babu duk daya ai kin sani” haka suka ci gaba da tattauna wa har suka isa unguwar da aka mata kwatancen sedai ta kasa ganewa, sunyi tambaya kowa yace be san mutumin da suke nema ba kuma ta kira Number Maman Lurwanu a kashe.

Kamar Adda zatayi kuka ta kalleta tace “yanzu Balaraba ya zamuyi dan Allah wallahi na gama saka ran waraka ta zo” kafin ta bata amsa Me Napep da tunda ya dakko su bece komai ba, tsaf ya gama nade hirar su ta hanyar voice note daya kunna tareda fahimtar matsalar ko waccen su se ya kashe mashin din yace musu bari ya kama ruwa kafin su gama yanke shawara.

Can Nesa dasu yaje ya zaro wayarsa ya shiga kiran abokinsa aransa yana ayyana Banza ta fadi daga can bangaren aka daga wayar ana cewa “ungulu baka jewar banza da alama ta samu”

Dariya yayi kafin yace “yi maza ka shirya area, ka duba whatsapp na tura maka saqo nan da minti Ashirin zan qaraso idan ta saitu”

Dayan ya bushe da dariya yace”an gama kwaro kamar kasan wallahi dama ina ta lissafin ta inda zam samu kudin yiwa Latifa Anko gashi ta matsamin kwana biyu babu kasuwa, Allah dai yasa ta waru, se kun qara so toh” sukayi sallama.

Gurinsu ya dawo harda karbar pure water a wani shago ya fasa ya zubda rabi ya taho yana wanke hannunsa,
“To hajia ina muka nufa yanzu” ya tambaye su bayan ya kunna Mashin.
“Maidamu inda ka dakko mu kawai” Balaraba da abun duniya ya ishe ta ta fada, se ya cilla suka dau hanya yana jin yanda suke ta jimami. Daidai wani gidan mai ya tsaya ya sha, seda ya dan bata lokaci sannan suka ci gaba ya gama shirya abinda ze gaya musu se yayi gyaran murya.

“Am nace Hajia kuyi haquri fa dukda ban gane kan damuwar taku ba amma idan kuna so akwai wani guri da wancan satin nakai wasu passengers, can na jirasu suka gama gaskiya daga yanda naji sun fito nasan sun samu biyan buqatar data kai su, kun gama saqon daya daga cikin su daga Kano tazo ashe suka karbi Number dazu naje na karbo zan saka mata ta tasha akai mata” ya fada yana bude dan gurin da suke zuba kudi ya zaro baqar leda, basu san mene ne a ciki ba gadai shi harda suna da Number waya an rubuta ta wanda zaa turawa saqon. To wanda kwakwalwar sa ta toshe ai se a hankali ba tareda tunanin komai ba suka ce ya kai su, a ransa ya ayyana “Madallah” ya cilla kan mashin suka dau hanya dan yasan zuwa yanzu an kimtsa komai dukda haka seda ya sake yi masa text ya tabbatar masa komai is ready su taho.

Tafiyar yan mintina takai su layin gidan har qofar gidan me dauke da shago se kuma soro na shiga cikin gidan. Wasu yan samari biyu ya gani daga gefe kan dakali yai musu sallama tareda tambayar su ko Malam yana nan

“Ai kuwa ya fita amma nasan ba dadewa zeyi ba qilan ma yana hanya.. au ka ganshi ma muna maganar” daya daga ciki ya bashi amsa. Se ya nufi gurin Wizy abokinsa daya sha uwar babbar riga harda wani rawanin iskanci shi a dole ga malami ya miqa masa hannu suka kashe amma se ka zata musa baha sukayi. Cikin daga murya Yanda su Adda zasu jiyo su Wizy yace “Mal Kamar kaine ka karbi saqon hajia Larai dazu ko lafiya dai ko mantuwa kayi”
“Eh wallahi Malam nine ba mantuwa nayi ba wasu iyayen daki na na rako ne”
Chapter 7 · 0% Book details