← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 158

Sashe 40

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farar shinkafa ce se ganyen parsley da aka yi garnishing na maida murfin ina cewa “Aa su Chef Amna harda wani ganye ganye aka zubawa Umfafar. Farida ta miqomun spoon tana cewa “Mami ci sauce din kiji ni nayi ko Yah Amna”.

Na karba na bude kwanon miyar, sauce din hanta da qoda sukayi se qamshi take na kai baki dadin ya ratsani, se na ajiye spoon din, “dagaske ita tayi Amna”
“Ita tayi Mami kawai gaya mata yanda zatayi nake se kuma na bata measurement na komai” Amnan ta fada.

Lallai ashe mun samu sabuwar chef, Yayi dadi sosai amma karki fadawa Abbi ki bari se ya gama ci tukunna”. Ina rufe baki Bashir ya shigo kitchen din, Farida ta ajiye wuqar hannunta ta nufeshi tana masa oyoyo.

“Me kike a Kitchen Farida da wuqa a hannunki bana hana ba” ya fada yana kallon fuskarta, ssannu da zuwa nayi masa ba tareda na amsa tambayar tasa ba dan dani yake ba Farida ba. Ledar hannunsa ya miqo Amna ta karba yace “ki sake warming nasa” ya juya suka fita yaja riqe da hannun Farida.

Fruit Salad din na qara sa hadawa, muka fito da kayan dukka muka jera a Dining lokacin har an fara kiran sallah. Dabino na koma na dakko masa da ruwa mara sanyi na ajiye akan stool din gefen kujera sannan na zubo fruits din a dan qaramin bowl na ajiye daidai sanda ya fito daga dakinsa da alama alwala yayi.

Ina kitchen ina hada kayan da zan soya masa kwai suka fita masallaci dan shi bazaki soya kwai ki ajiye masa ba ya fiso daga kasko se farantinsa. Kayan cikin na dumama na fito da Balangun da Amna ta saka a Oven shima na juye masa a bowl a raina ina jinjina qaunar Bashir da nama. Seda na soya kwan bayan sun dawo na ajiye masa komai sannan na shiga dakina na barshi da yaran suna tayashi shan ruwa.

Dana idar da sallah ma ban fito ba, miqewa nayi ina chat da yan uwa da abokan arziqi har aka yi Isha. Ji nayi ana kwankwasa qofa. Aliyune, bayan ya shigo yace “Abbi yana kiranki”
Da “toh” na amsa na miqe ya qara powder da turare na yafa mayafi na na fita.

Suna zaune a kan kujerun Palour sun cika ko ina, “ikon Allah wai duk bataliyar nan yayan Ma’une” na raya a raina kawai na tuntsyre da dariya se suka juyo dukka suna kallona.

“Lafiya kike dariya” Bashir ya tambayeni, seda na zauna a kusada shi kafin nace “ganin yaran nan nayi da yawa nake mamakin wai duk nawa ne”.

“Da sauran wasu ma a gaba ai” ya fada yana kallona da wani kalar expression, kallonsa nayi nima har sannan fuskarsa bata koma daidai ba da sauran alamun damuwa da bacin rai akanta nace “Aa ni ai na gama, na barwa yan baya gashinan sun fara ai” harya bude baki zeyi magana wayarsa tayi qara, Dr Hadi ne pediatrist din da yake kula da Iman. Daga wayar yayi bayan ya miqe ya shige dakinsa nima sena tashi na qarasa kan Dining na debi abinci.

Ina ci muna yar hira da yara, ina kammalawa suka kwashe komai aka kai Kitchen muka tattare palour qal dan kusan komai da dare mukeyinsa daman saboda fitar safiya muna gamawa nace suje su kwanta gobe akwai school.

Dakina na koma na sake wanka na shirya tsaf na tafi dakin Bashir, yana kwance rabin jikinsa akan Gadon qafafunsa kuma a qasa ya harde hannu a qirji yana kallon sama da alama tunani yake. Banajin yaji shigata har seda na ajiye wayata da Zoben dana zare daga hannuna akan Bedside sukayi qara sannan ya dago a dan zabure.

“Yadai?” Na tambayeshi se ya girgiza mun kai alamar babu komai kafin ya miqe ya shiga toilet. Ina shafa addua ta ya fito daga toilet din daure da towel a qugunsa, kallonsa nayi sam bazakace Bashir ya fara jiyo qamshin Hamsin ba saboda kyan jikinsa, a tsarin halitta befi ka bashi shekaru 35 zuwa 37 ba amma a zahiri shekarunsa 45 ne.

Har ya shafa mai ya saka kayan bacci riga da wando light blue ina zaune ina kallon sa, yanda yake abubuwa a sabule kamar mara laka harya gama ya kashe fitilar tareda hawa kan Gadon ya janyoni jikinsa ya dora kansa akan qirjina mukayi shiru bakajin komai se qarar Ac a dakin, kusan minti goma a zatona ma bacci yayi naji ya riqo hannuna sosai yana cewa “bana so na rasa ta”.

“Qum” naji kaman an jefeni da dutse dan a sukwane zuciyata Amirah ta kawo mun sedai kafin nayi magana naji ya sake cewa “bana son na rasa Iman Ma’u, ina son yarinyar kwatankwacin yanda nake son Farida, na dade inawa Farida fatan ta samu yar uwa se yanzu Allah ya bata gashi ina neman rasata”.

Wato wani sanyi naji a raina, sena gyara kwanciya ta ina cewa “ba abinda ze faru da izinin Allah zata tashi, naga jikin ai da sauqi jiya da muka je koh?”

“Eh da sauqi sosai, yanzu ma kiran da Dr yamun su naso su sallameta ne” ya fada yana tashi zaune sosai.

“Kai masha Allah, Allah ya qara lafiya” na fada ina gyara kwanciya harda jan bargo a zatona maganar ta qare sejin Bashir nayi yana wani soki burutsu

“Idan an sallamota ina so zan kawo ta nan” ya fada. Naji ba wai banji shi ba amma son na tabbatar da ma’anar maganar tasa yasa na dago na kalleshi kafin nace
“Ban gane me kake nufi ba zaka kawo ta nan, Amiran nan zasu dawo ne ban sani ba?”

“Aa ba Amirah ce zata dawo ba Iman nake nufi zan kawo miki ki riqeta na bar miki ita”.

“Ikon Allah” na fada a fili kafin na tashi zaune sosai na ina kallonsa,
“Ka kawota nan fa kace Baban Ali jaririyar da ko wata bata cika a duniya ba, me ya samu ita Amiran da bazata iya riqe yarta ba. To ai ko mutuwa tayi tunda tana da uwa a raye zata karbeta bare da ranta ace za’a raba ta da yar data sha wahala kafin ta sameta ah gaskiya kaima baka zo da maslaha ba”.

Kallona yake har na kai qarshen maganar, nayi zaton ze balbaleni da masifa ne yace seya kawo yarinyar amma aka sin haka sema wani marairaicewa daya sakeyi ya kamo hannuna yana cewa

“Kin fita cancanta daki tarbiyyantar mun da yaya, sam waccen yarinyar bata da tunanin da zata iya kula da kanta ma bare wani. Kina gani bataji tausayin yarinyar ba suka jaza mata wahala bana tunanin zata iya rainon yarinyar”.

Sakato nayi ina ji da ganin ikon Allah rainin hankali da tsakar dare, ace ta haifi amma bazata iya kula da ita ba ni ga jakar Ÿaÿa shine za’a dakko wata bakwaini a kawo mun lallai zanga uban da ya isa kuwa. Fizge hannuna nayi na kwanta tareda juya masa baya nace

“Ai Kowa ma be iya ba daga baya ya koya itama a hankali zata iya tunda babu wanda baya son dan sa” naja bargo na rufe har kaina. Shiru naji har kusan minti goma beyi magana ba be kwanta ba nima ban sake motsawa ba tun ina mita a raina har bacci yai gaba dani amma ahu daya na qudurce wallahi ko sama da qasa zata hade bazan zamar masa yar raino ba.
Ban kuka ga uban daya isa ya saka na karbi yarinyar ba.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 24

Gombe
Bayan Naziru ya kaimu Airport kai tsaye kasuwa ya wuce ya siyi duk abinda Bashir ya gaya masa ya kaiwa Amirah. Tana zaune a palour bayan ta gama kukan ta yai sallama ta amsa fuska a kumbure be kulata ba ya shiga kwaso kayan da taimakon Almajiran daya kira suka shigar mata da su Kitchen.

Har ya gama bata ko sake kallonsa ba dan haushin sa takeji tasan shi yake qara zuga Bashir din ma akan komai, seda ya kai qofa ta tuna da zancen waya seta miqe da sauri tabi bayansa tana kwalla masa kira ya kuwa shareta kamar beji ba seda yaje gurin mota tana biye dashi.

“Meye kike bina kamar naci miki Bashi” ya fada yana harararta, inda haka kawai ne seta rama amma tunda abu take nema seta karyar da kai tana cewa “Dan Allah Yaya Naziru waya zaka siyo mun da layi”.

Seda ya harareta kafin yace “waya? Me zakiyi da waya ina taki?”

“An sace” ta bashi amsa kai tsaye.
“Toh ai shikenan gara da aka sace, kuma ni sa’an kine ko dan aikenki da zan siyo miki waya ke baki da qafa ko baki san inda ake siyarwa ba” Nazirun ya fada. Seta marairai ce tana cewa

“Dan Allah ka taimaka mun Yaya”. Kwafa yayi kafin yace

“Kawo kudin toh badan halin ki ba”

“Nagode” ta fada kafin ta qirgo dubu biyar da dari biyar ta bashi, ya karba ya irga ya kalleta yace

“Saboda a gidan ku ake qera wa ko waye ze siyar miki da wayar dubu biyar”

“Yaya Tecno fa me keypad ai bata wuce haka ba”

“To se kije ki siyo kin tsaya kina batamun lokaci” ya fada yana miqa mata kudin, setayi saurin dakatar dashi tana cewa “yi haquri dan Allah nawa ce se na ciki”

“Dubu goma ce sannan ki bada dubu biyu kudin mai tunda babu siyo miki waya a lissafin da aka mun. Ba yanda ta iya tana ji tana gani ta zare dubu goma sha biyu da dari biyar ta bashi ya tafi, idan da abun nata da mutunchi tasan a kyauta ma siyo mata zeyi amma yanda tasan yana jin haushinta ma tayi mamakin da yayi saurin karbar aiken.

Ciki ta koma ta tafasa ruwan zafi ta dakko kayan Tea a siyayyar da ya yo mata harda bread ta zauna ta karya, tana zaune a gurin ya dawo ya miqa mata leda da kwalin wayar a ciki da layi harda katin dubu daya ta karba tayi godiya harya juya ta kuma tsaida shi tana cewa
Chapter 40 · 0% Book details