← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 158

Sashe 63

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Me yasa zan gaya maka tunda baka son mu hadu yanzu, daman zuwa nayi in gaya maka dan karka ji a gari, tunda dai ka gagara turowa zan bawa wadanda suka shirya dama. Na kuma gode da batamun lokaci da kayi da duk alqawarirrikan qaryar da kayi mun akan zamu rayu tare” ina gama fadar haka nayi gaba na barshi a tsaye ina jinsa yana kwala mun kira nayi banza dashi.

A zatona ze biyo mu amma har muka je gida babu ko sahunsa, abinda ya qara qona mun rai ya tabbatar mun dagaske kenan daman Bashir yaudarata kawai yayi ba aurena zeyi ba yasa na gama fadawa a soyayyarsa sannan yanzu ze gudu ya barni. Ranar haka na kwana ina kuka, gashi ko a waya be kirani ba, babu wanda yabi ta kaina a gidan,

Hajia Anjij cema da safe da ta ga yanda idona ya kumbura ta jani tanayi mun nasiha da nayi haquri, lokaci da yawa abinda muke so be zama lallai shine Alkahiri a gare mu ba dan haka na fawwalawa Allah, idan Bashir mijina ne se munyi aure idan kuma Allah be yi ba duk nacin mu sedai mu haqura.

BASHIR

Tun lokacin da Asma’u ta gaya masa zancen an ce ya turo gida se maganar ta rabe masa biyu, bangare daya na farin cikin ya kusa mallakar Ma’unsa se kuma daya bangaren tashin hankalin da me ze aureta?

Har yanzu bashida komai be kuma bawa wani ajiya ba, dan aikin da yakeyi dubu goma ce ake biyansa a wata wadda dawainiyat karan kansa ma ba isar sa takeyi ba ga qannensa suma da qananun buqatunsu tunda Babansu yayi ritaya, kudin garatutinsa suya har hada yake dan juyawa ana samun abinda za’ayi cefane a gidan yanzu gaba daya duk burinsu akansa suke na ya samu aiki toh ta ina kuma ze fara daddago maganar aure.

Kullum da wannan zulumin yake kwana yake tashi ya kuma rasa dawa zeyi shawara baze iya tunkarar Abubakar ba, Aliyu kuwa tun tuni daman ya gaya masa ya rabu da Asma’u dan tafi qarfinsa toh se a yanzu ya ga gaskiyar abinda yake fada din amma kuma baya jin ze iya rabuwa da ita saboda sonta ya riga yayi masa irin shigar da fitar rai ce kadai zata iya raba shi da shi wannan dalilin ya sa yake zille mata dan ganinta ma kullum qara rura wutar sonta yake a zuciyarsa sannan ya rasa ta yanda ze fahimtar da ita halin da ake ciki.

Maganar data gaya masa dazun ba qaramin tayar masa da hankali tayi ba, gaskiya bazata sabu ba. Dole ya nemi mafita dan yana ji yana gani baze iya zuba ido wani ya raba shi da Ma’u ba ya rusa duk wani tsari da mafarkin sa akanta.

Jiki a sabule ya koma cikin gidan, palour Dada ya shiga ya tarar dasu ta zazzage turarukan tana ta santinsu gaba daya ta kwashe se kwalli daya ta barwa Dadan wai ai kullum ana kawo mata na yau rabonta ne kudin ma seda ta raba biyu ta dauka, ganin yanda Bashir ya shigo kamar kazar da tasha ruwa yasa suka dakata suna kallonsa.

“Lafiya Bashir ka shigo kamar wanda aka zarewa qashi” Addan ta fada tana kallonsa, se ya ja guntuntsaki yana kallon Dada yace “Dada maganar da mukayi dake akan sunce mu tura ne, kinsan tare ake so a hada dana sauran toh shine yanzu tayi fushi har tana cewa kawai zata bawa wasu dama tunda ban shirya ba”.

“Me zanji haka magana babu dadin ji, kai yanzu Allah ya kashe ya baka shine ka tsaya salubanci da sunce ka tura din amma ba’a je ba to uwar me kake jira?” Addah ta fada tana gyara zama.

Shiru Bashir ya mata, dan shi kwata kwata baya so tana shiga sabgarsa ma, Dada ce tace
“Toh Addah kin manta har yanzu be samu aiki bane, aure ai baze yuwu ba babu abinyi dame ze riqe matar?”

“Sannu Nafi, kai Allah Nagode maka da Halin Nafi. Wane irin aiki kuma kuke magana mutumin da Allah ya kawo masa hanyar arziqi, yanzu in banda rashin tunanin irin naki har kwa tsaya kuna zancen wani aiki ga babban aiki ya samu.

Ka samu yarinya irin wannan daga babban gida tana sonka kuma iyayenta sun yarda zasu baka qarewar aiki harda gida da mota se an hada maka nasan kai dai kawai ka tura ayi magana asan dagaske kake seka gaya musu baka da aikin yin Aradu zasu samo maka tunda yarsu tana sonka.

Kai ashe Nafi kina dab da ja mana Asara kai Jama’a Allah kayi magani”.

Kallon ta kawai suke har ta gama hayagagarta, se Bashir ya miqe ya fice a ransa ya na qudurce kawai ze gayawa Alhajin su aje, idan yaso su abar maganar nasu bikin zuwa sanda Allah ze sa ya samu madafa tunda ya rarraba CV dinsa a gurare yanzu jiran tsammani kawai yake yi. Kasa zama yayi a gidan ya fice, yana so ya kira Ma’u kuma yana tsoron abinda zata sake gaya masa Allah Allah kawai Yake Alhaji ya dawo ayi wacce za’ayi kawai.

Addah kuwa ci gaba tayi da surutan ta har tana cewa Dadan idan ma maganar kudi ce se a nemo Bashi ayi komai da an gama biki abinda ya samu a tattara a biya.

“Kiji ki Addah wane irin bashi ana zaune qalau dan Allah, babu komai idan Allah ya nufa matarsa ce to se kiga Allah ya kawo hanyar da za’ayi komai cikin rufin asiri. Haka suka rabu dai Addah na sake jaddada aje ayi maganar nan kar su bari damar nan ta wuce su.

Bashir kuwa Alhajin su na dawowa da yamma ya shaida masa, ba tareda wani ja inja ba kuwa ya amince shima abinda yace Allahn daya taso da maganar ze hore yanda za’ayi komai cikin rufin asiri, tun a daren ranar ya tashi qaninsa ya aikashi gurin Baffan su Asma’u akan a basu dama zasu kawo goron gaisuwa, a take kuwa yace duk sanda suka shirya suzo, washe gari kuwa suka hadu da Qannensa guda biyu da Amininsa daya sukaje aka kai gaisuwa.

Tarba me kyau suka samu daga gurin Baffan da yayyen Ma’u biyu manya, nan da nan aka qulla magana sedai sun nemi alfarmar a qara musu lokaci akan wata shida da Baffa yace ya yanke ranar auren.

“Kasan haryanzu Alhaji be samu wani aiki na gaske ba, yar buga buga ce kawai akeyi ana dai saka ran samun aikin nan kusa, abinda yasa muka zo din ma saboda kaga kar aga kamar wasa ne abun” Aminin Baban su Bashir Malam Salisu ya fada.

Se Baffa yayi murmushi yace “Babu komai Malam Salisu in sha Allahu babu abinda ze gagara, kuje kuyi shirinku iya abinda ya zama dole sadakine se ya nemi muhallin da ze ajiyeta duk abinda ya kakare masa yazo ya sameni babu komai” suka yi sallama suna ta godiya, haka suka koma gida suna ta yabon dattako da karamci irin na Baffa, dan lokacin da sukaje gidan daya daga qannen Baban su Bashir din har yana cewa anya za’a barsu su shiga kuwa shi Bashir me ya kaishi dakko abinda yafi qarfinsa.

ASMA’U

Ina kwance ina ta baqin raina tun jiya har yanzu ban ware ba, gaba daya na rasa ya ma zanyi dan bazan iya hasaso rayuwa da wani namiji da ba Bashir ba. Addu’ata kawai Allah ya mantar da Baffa karya kuma tado mun da maganar har zuwa sanda zamu samu mafita.

Ina cikin wannan tunanin Baba Jummai shugabar masu aikin gidan mu ta shigo dakin ta sakar mun guda a tsakiyar kai, da saurin gaske na toshe kunne ina zare ido ita kuwa se sake rangada abarta take ragowar na taya ta.

“Uwar dakina ta zama amarya mun shaida mun tauna goro da alawa Allah ya nuna mana randa zamu sha taushen daurin aure” ta fada kafin ta sake kwasar wata gudar.

Wani mugun bugawa qirjina yayi, waye ya kawo goro na? Na shiga uku kardai fa Baffa ya amsa wa wani daga cikin manemana magana.

Dafe qirji nayi na qara fito ta idanu waje nace “Baba Jummai gorona aka kawo dawa?”

“Wato Uwar dakina kina nan da halin ki na tsokana, baki ma san waya kawo goron ba kenan, to wannan Me gidan da baya dariya ne Engineer kike ce masa kowa” Baba Jummai ta fada.

Se naji kamar an kwararamun ruwan qanqara a tsakiyar kaina, wata wawuyar ajiyar zuciya nayi kafin na koma na kwanta ina yiwa Allah tasbihi. Gaskiya Bashir ya shammaceni.

Waya ta ce ta dauki qara, a jikina na ji cewa Bashir ne, seda na tura baki kamar yana gabana kafin na daga wayar.

“Amaryata” ya fada cikin qaramin sauti, shiru na masa ina ta faman juya baki kamar yana gaba na ina jinsa yayi murmushi yace “Fushi ake yi dani ko Ma’una ayi mun afuwa. Gani a qofar gida nazo bada haquri”.

“Ni bazan fito ba” na fada cikin muryar shagwaba, se ya marairaice shima yace

“Haba mana Amaryata so kike yi na kasa bacci dan Allah ki fito na ganki mana kafin nan da wata shida na dauke ki gaba daya ki zama tawa”.

Rufe fuska ta nayi ina murmushi nace “Dagake bazan fito ba, nima ai jiya banyi baccin ba kaga mun yi 1-1 kenan ka tafi se bayan sati uku zaka sake ganina”.

“Kice kawai sena zare sannan, ki taimaka mun nidai ki fito na ganki ko minti daya ne ki koma na yarda”.

Seda naja masa rai kafin na zura dogon hijabina har qasa na fita, a palour na tarar da Goggo da su Nasir suna kallo naja hannun Mimi yar dakin Hajia Umma ce muka fita.

Bashir na tsaye daga bakin Get gurin masu gadi, har wurin naje nace masa”A nan ka tsaya maimakon ka zauna, muqarasa toh”.

“Aa Gimbiya daman zuwa nayi naga kyakykyawar fuskar ki sannan na kawo miki wannan(ya miqo mun wata farar leda da kwali dan kwali qarami a ciki) ina so na kwanta da wuri gobe zanje wata Interview kiyi mun Addu’a Allah yasa a dace”.
Chapter 63 · 0% Book details