← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 158

Sashe 78

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan Ace duk matan duniya manya da yara farare da baqar fata Bashir ya rasa wadda ze aura se Amirah yarinyar dana gama bautawa tun tana qanqanuwarta har girma yanzu ace da ita zanyi zaman kishi yarinyar data  san sirrina, na bude mata duk wasu sirrika da nake taqama dasu saboda yanda na dauketa tamkar qanwata na gyarata saboda ta samu daraja a gurin mijin da zata aura yanzu ashe duk mijina nayiwa wannan tanadin? Ni za'a yaqa dasu?

"Yah ubangiji kaika halicceni, kai ka tsara mun rayuwata tun kafin wanzuwa ta a doron duniya Allah kasan zan iya shi yasa ka dora mun na roqeka nayi tawassali da sunayen ka tsarkaka nayi tawassali da Annabin ka Muhammad SAW Allah in har sunyi dan su cutar dani na roqeka karka basu ikon ganin gazawa ta, ka sanya min juriya da dakiyar tun karar duk wani qalubale da zan fuskanta a rayuwa. Ubangiji ka sauqaqa mun dau wani ka bani zuciyar da zan iya dauka" na fada a fili ina fashewa da wani irin kukan baqin ciki.

Wallahi ko kadan banji haushin auran da Bashir yayi ba, da ace wata ce daban zan shanye na danne bazan taba nuna masa komai ba har in ga iya gudun ruwan sa amma Amirah fa Amiran Addah me yasa se Ita? Da ace Ummi qanwarta ya aura nasan bazan ji baqin ciki irin wanda nake ji yanzu akan auran Amirah da yayi ba.

"Amirah zata dawo gidan nan kuma a sannan baki isa ki koreta ba" kalaman Addah suka dawo mun a kwakwalwa ranar da na kori Amirah daga gidana a Gombe. Ashe abinda suka shirya yi mun kenan daga ita har Dadan suka dakko kishiyata suka kawo mun da nufin na gyarata su kuwa wasu irin mutane masu saka Alkahiri da sharri ta ina na kuskure musu a rayuwa da suka zabi hukunta ni ta irin wannan hanyar?

Kuka na ringayi wanda tun likitocin da suka dubani suna bani haquri har suka haqura sukayi shiru, bana buqatar sauran bata lokaci a qasar tunda daman ba dan Allah ya turani ba dan ya aiwatar da nufin sa ne to yaci galaba amma nima dole na koma Nigeria muyi wacce zamuyi da Bashir dan bazan taba hada miji da Amirah ba.

Yana da damar ya auro mun mata uku mu zauna amma ba Amirah yarinyar da nakewa Kallon Yata ita ce ze hadani kishi da ita baze sabu ba.

Sanda na koma Hotel din da muke na tarar da yara zuru zuru dan da aka kaini Asibiti can suka koma saboda a qa'idar su ba'a barin dan jinya.

"Ku hada kayan ku yau zamu tafi" na fada ina hargitso duk abinda hannuna ya kai kansa ina sakawa a jaka. Seda na gama sannan na tuna da ai Passport dinmu ma baya hannunmu yana gurin Agent din da Bashir ya hadamu dashi, wayata na dauka na shiga kiran nayi sa'a tana shiga ya daga.

"Malam Isah kayi mana booking jirgi idan da akwai Yau ka, ka fada mun kudin ko nawane zan biya wani abu ya taso mun bazan iya jira har se gobe ba" na fada ba tareda na amsa gaisuwar daya fara mun ba.

"Amma Hajia me ya faru haka, bayan haka kuma ai Ticket din ku bana komawa Nigeria bane Dubai zaku wuce daga nan na zata ai Engineer ya gaya miki ma"

"Isah dakai da Dubai din da Engineer kunci abu ta kazan ubanku" na lailayo wata Ashar me maiqo da ni kaina bansan na iya ta ba na kora masa kafin na ci gaba da cewa

"Ka kawo mun passport din mu nan da Awa daya idan ba haka ba wallahi se nayi qarar ka nace safarar mu kayi, kasan ina da duk wasu bayanai naka da zan bayar ka kuskure lokacin baka zoba ka gani".

"Kiyi haquri hajia ku shirya yanzu zan turo mota da zata kaiku Jiddah ni ina can yanzu haka akwai jirgin da ze tashi yau da daddare bari na bincika idan da akwai guri se a siya" Isah ya fada jin abin yafi qarfinsa.

A dakin muka bar kusan rabin kayan mu dan bana buqatar abinda ze bata mun lokaci bate har aje ana maganar wani awon kaya ko wani abu muka hau mota se Jiddah gaba daya ma gani nayi motar bata sauri, ina ma ace zan iya rufe ido na ganni a Nigeria, ina buqatar naje naga da wadanne idanu Bashir da danginsa zasu kalleni.

Mun samu jirgi amma se munyi jiran Awa goma sha biyu kafin tashinsa, haka Isah ya nema mana hotel gaba daya ya rasa meya faru haka gashi kiran duniya Bashir yaqi dagawa daga qarshe ma ya kashe wayar gaba daya Asma'u kuwa bega fuskar da ze mata tambayar abinda yake faruwa ba ma dan haka yaja Aliyu yana tambayarsa ko mutuwa akayi

"Nima ban sani ba, kawai daga Masallaci aka kaita Asibiti kuma data dawo mun kasa tambayarta abinda ya faru idan mukaje gida koma menene se mu gani" Aliyun ya bashi amsa.

Haka muka hawo jirgi se Nigeria ya sauke mu a Kano,Asuba ranar lahadi muka sauka tun a AirPort na samu shatar mota ta kwashe mu kafin Goman safe mun sauka a Gombe muka ci burki a qofar gidan su Bashir cikin Sa'a nayi kyakykyawan gamo da Ango Bashir da tun daren Alhamis rabon da ya sake daga wayata.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 39

A qofar gidan motar mu ta tsaya, idona akan Bashir da suke tsaye tareda wasu mutum biyu da ban gabe su waye ba.

“Ku jirani karku fito” na fadawa yaran, seda na yi kokawa da duk wani rauni da karayar zuciyar daya taso mun kafin na bude motar na fito ina gyara mayafin kaina gaba daya mutanen gurin suka bini da kallo banda Bashir da tunda muka hada ido ya maida kansa qasa kaman wanda aka kama yayi qarya.

Kai tsaye cikin gidan na shiga, nayi sallama ina jiyo hayaniyar su daga cikin dakin Dada amma ba’a Amsa ba dan haka na nufi can din, har na kai bakin qofar naji an kira sunana, sena waiwaya.

Alhajin su Bashir ne yana tsaye daga qofar dakinsa ya yafito ni da hannu sena juya na koma gurinsa.

Ina durqushe a gabansa kusan minti biyu kafin yaja numfashi yace dani

“Asma’u kiyi haquri nasan an cutar dake amma zan roqeki Arziqi kar kice musu komai yanzu, ki barsu akwai ranar da su da kansu zasu maidawa junan su martanin abinda sukayi miki.

Na sani Qarin aure ba haramun bane amma ta yanda aka shirya naki sam be kamata ba. Ya zama zamba cikin aminci. Ki sani Ita Amana daya ce kuma wanda yacita baya taba zama lafiya, idan har Bashir da uwarsa sun qulla wannan aure dan su ci mutunchin ki Asma’u in Allah ya yarda muna raye ko mun mutu se sunga sakayyar cin Amanar da sukayi miki.

Ina qara roqonki da kiyi haquri, ki qara akan wanda kike yi in sha Allahu bazaki tabe ba, duk me neman gazawarki akan idonsa zakiyita ci gaba da yardar Allah”.

Kuka nakeyi dagaske a raina ina hasaso irin tarin qaunar da na nunawa Bashir da Ahalinsa, a tsahon zamana dashi kusan shekara goma sha uku yanzu bazan iya cewa taka maimai ga wani abun laifi daya taba hadani da wata daga cikin su ba, a kullum cikin kyautata musu nake iya qarfina kuma duk albarkacin so da qaunar da nakeyi wa Bashir din ce ta shafi su amma ace a gurinsu basu da abokin hamayya seni.

Sosai nasha kuka na ba tareda Baba ya hanani ba in banda “kiyi haquri Asma’u” babu abinda yake cewa.

“Naji zan haqura Baba bazan tanka musu ba amma kayi haquri bana jin zan iya ci gaba da zama da Bashir. Bazan iya ci gaba da zama cikin Ahalin da basa qaunata ba Baba. Sannan Baba Amirah fa, yarinyar dana raina da hannuna ita zan hada miji da ita wallahi bazan iya ba.

“Zan bi umarnin ka a yanzu zan koma ba tareda na cewa kowa cikin su komai ba amma Baba karka roqeni ci gaba da zama da Bashir saboda ina girmamaka bazan iya tsallake unarninka ba amma tabbas zan cutu. Zuciyata zata iya bugawa a dalilin haka muddin zan zauna inuwa daya da Amirah a matsayin kishiyata” na fada cikin sheshsheqa me qarfi.

Se Baba yayi murmushi wanda da ganinsa na takaici ne kafij yace
“Asma’u ke Yarinyar kirki ce sannan abar Alfaharin duk Miji me hankali da yayi katarin samun irin ki sannan ko wanne uba zeyi alfaharin zamtowarki Suruka a gare shi.

Bazan so na rasa nagartacciyar suruka irin ki a cikin zuria’ata ba domin ke din mayafi ce da kika lullube Bashir duk kuma ranar da wannan mayafin ya yaye ba baki nayiwa Bashir ba tabbas se rayuwar sa ta shiga cikin gararin rayuwa.

Idan har ki ka ce bazaki ci gaba da zama da Bashir ba ni me tsaya miki ne in tayaki kwatar yancin kanki amma yanzu kije ki samu nutsuwar zuciya, karki yanke hukunci cikin fushi idan kika nutsu duk abinda kika yankewa zuciyarki ki dawo ni ki gaya mun in Allah ya yarda zan baki goyon baya dari bisa dari ki share hawayenki yanzu”.

“Baba bana tunanin ina da buqatar yin wani dogon nazari ka taimakeni kawai kasa Bashir ya sawwaqe mun dan ina da yaqinin ko ba yanzu ba watarana se sunyi nasarar fiddani daga dakina” na fada cikin kuka, se ya tare ni da cewa

“Haba Asma’u ke da na sanki jaruma ya zaki karaya tun yanzu ki bada qofar da za’a ci galaba akanki? Maganar su fitar dake daga dakinki kuka babu wanda ya isa yayi Abinda Allah beyi ba, kije gida ki huta ki bawa zuciyarki haquri idan kuma kinga bazaki iya karbar Al’amarin ba ki dawo zan tsaya miki”.

“Shikenan Nagode Baba Allah ya qara girma”
“Nima na gode Asma’u Allah yayi miki albarka keda zuri’arki gaba daya”. Haka mukayi sallama da Baba seda yasakani na share hawayena tas yace naje na dauraye fuskata a bayin da yake cikin palour sa kafin na fito.
Chapter 78 · 0% Book details