← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 158

Sashe 8

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ah to to bismillah ku shigo ka barsu anan kuma kai Iliya me yasa baku bude musu shago sun shiga ba ko ka kaisu cikin gida gurin Maimuna kan nazo” ya fada yana hararar samarin da suke zaune. Seda Iliya yayi dagaske gurin riqe dariyar sa kafin yace “Malam ai ta fita gidan suna itama kuma ka tafi da muqullin shagon ai”
“Anyi haka ya fada yana bude musu kofar suka shiga gaba daya, bayan sun zauna Me Napep yace bari yaje daga waje idan sun gama shima se yazo a bashi taimakon kasuwa.

Malam ya jawo faranti me dauke da yashi ga kuma carbi me dubu ya hau ja yana muimui da baki nan kuma yana faman zane zane sannan ya dago ya kalle su “toh hajia dawa Zamu fara?” Ya tambaye su.

Hajia Balaraba ce ta fara matsawa tace “Malam ni matsalar kaina ce a fara dani dama..” se ya dakatar da ita, “ki bari mu duba abunda bamu fahimtaba se kiyi mana bayani da kuma matakin da kike so a dauka.

Tiryan tiryan ya ringa jera mata zance kamar me gani a film kai har abinda basu fada Me Napep yaji ba seda Wizy ya canka ya fada se kuwa tace kai Malam aikuwa hakane wallahi, yana ta tiqar dariya a qasan ransa to ai labarin duk daya ne dukma wadda tazo indai akan kishiya ne banbancin basu da yawa. Seda ya gama ratta ba mata zance Adda da me gefe ta gama yin Ammana sun zo inda zaa magance musu matsalar su harta gama Ayyano Yanda zasu juya Bashir kaman Tanda a waina.

Tsaf Hajia Balaraba ta gama gaya masa yanda take so ayi nan kuwa ya yanka mata 50k babu neman ragi ba komai ta cake masa su to taji sauqi akan ubannin kudin data ke kashewa babu biyan buqata. Allonsa ya jawo da tawada ya hau rubuta abunda in zaka kashe shi be san menene ba ya gama ya miqa mata da kwano da ruwa yace ta wanke idan taje gida ta guntsi rabi ta fesa a kofar dakin kishiyar ko inda tasan zata taka rabin kuma ta kuskure baki ta zuba a miya kowa na gidan yaci to daga nan babu me jin maganar wani se tata.

Wasu qullin Jan Maganin da kore ya sake dakkowa ya bata su kuma yace ta ringa jiqawa kwana 7 tana sha sannan ya qara mata da wani kuma a jarkoki guda biyu yace ta juye a bokiti ta qara musu ruwa ta ringa sha shima mijin ta san yanda zaayi yasha koda tea ne ta dafa masa dashi sauran aiki kuma karta damu zeyi daga nan shidai idan buqata ta biya kar a manta dashi (kuji dan banza 😂😂Koren Magani na sabara da Jan magani yake ba wa duk wadda tazo se na cikin jarka kuma maganin Basir ne ko banza ai ya temake so ko 😂😂😂😂😂😂).

Adda ce ta matso aka buga mata nata duban se ya kalleta “Wace Mace ce haka gata nan dai Fara kyakykyawa kamar ma bata da lafiya tana gadon Asibiti”
Ai caraf ta amshe “Asma’u ce ita ce kishiyar yar tawa” gyara zama yayi yana ayyano yanda ze tatsi matan nan yace
“Kamar a kudu take fa wannan kai” se yai shiru kafin ya ci gaba
“Tab di hajia akwai babban aiki a gabanki fa dan koma wacece wannan tasha kan shi wannan mutumin sosai dan kuwa Arnan kan dutse ne suke mata aiki an hada shi da gungun Aljanu suna gadinsa gaskiya wannan aiki yafi qarfina”

“Ai Adda kamar zata rushe da kuka tace “haba Malam ba abinda ya fi karfinka ai (haba Adda Allah ne kadai keda maganin komai) ka duba ka taimakamun nidai a tarkato mana hankalinsa ai ko baya auran yata ni me tsayawa na nema masa taimako ce tunda dana ne ai dan yar uwata”.

Zama ya gyara yace “abinda kamar wuya gaskiya kin san aiki da kafiran Aljanu akwai wahala amma in zaki saki kudi ayi musu yanka kinsan su jini suke so to wala Allah a dace”

“Malam indai zaa samu biyan buqata ba matsaka yanzu kamar me zaa yanka?”

“Gaskiya hajia a qalla za’a yanka musu raguna 20” seta dafe qirji tace Malam ina zan samu kudin nan yanzu fa nake maka bayanin na biyan bashi ma nake nema ni a fara rufemun bakin matar nan ma tukunna ta manta da zancen kudin”.

“Wannan duk ba matsala bane kuma zaki iya ringa bayarwa a hankali ai in kin so ma kiringa yankan da kanki amma akwai kalar dabbobin da ake so da kuma abinda ake fada in za’ayi yankan in kina da wanda ze miki duk sena gaya miki ai”

“Aa malam zaa mata komai anan” Hajia Balaraba ta fada
“To ba matsala”
“Kamar nawa kenan Malam” ta tambaya

“To akwai qauyen dana ke siyo dabbobi ana samun qosashshen rago dai daga dubu Arba’in kinga a qalla guda koma dubu Dari hudu kenan amma zaki iya ringayi a sannu in so samu ne dai cikin wata biyu a kammala aikin”.

Nan dai Adda ta zazzage masa dubu tamanin kudin data harhada zata rage biyan bashi tace in an kwana biyu zata kawo abinda ya samu, ita be bata komai ba se wani abu kamar goro yace idan matar tazo ta saka a bakinta ta ringa taunaqmwa tana mata magana kamar remote haka zata controlling nata aikin Bashir kuma Wannan Ze duqufa yai tayi itama Amira jin tana da ciki ya nemo wani garin Maganin zaqi dana sanyi da aka aike shi ya kaiwa Yayar sa da take da ciki ya bata yace ta kai mata tayi tasha zuwa sanda Bashir zezo daya kwanta da ita anci rabin aiki.

Kamar wanda yai musu kyauta suka ringa zabga godiya ya basu Number wayar sa suka fito Me Napep har ya gaji bacci ya dauke shi fitowarsu ta farkar dashi,
“Gaskiya kun dade hajia yau balance kawai zaku bani na maida Machine din nan na huta dan har na gama gajia” ya kunna suna shirin tafiya har sun ja Iliya ya tsaidasu akan Malam yace ya manta da taimakon kasuwar ne, se suka koma ya barsu a cikin mashin ya shiga.

Be zauna ba 40% 60% suke raba duk abinda suka samu Wizy se dauki 50% ragowar 10 ya bawa su iliya da sauran masu yi musu cover a harkar, cas ya cake masa kudin sa tareda bashi wata qatuwar takadda da aka nade kamar laya yace zasuyi waya ya fito, ransa fes suka kama hanya bayan ya saqala Takaddar a gaban mashin wai ta kiran customers 😂😂 ikon Allah kuwa duk inda suka gifta se an tsaidashi yace drop ne har ya ajiye Hajia Balaraba ya wuce Da Adda Fatu dan tace gara taje ta kai mata ta fara sha tunda yau Alhamis a qa’ida gobe Juma’a ze zo

To se muce Allah kauda tsautsayi da Asara 😂😂😂😂https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 6

Da Isar Adda gida bata ko zauna ba ta jiqawa Amirah maganin da aka bata tace gashi nan tayi tasha Zuwa goben sega yanda za’ayi.
“Adda kin ganin ze zo ne ko kin manta yanda mukayi dashi jiya da daddare” Amirah ta fada cikin sanyin jiki.

“Ke dallacan barshi ai idan be zo bama baze samu nutsuwa ba saboda sabon malamin nan da muka samu da zafin sa in gaya miki kedai kakarmu ta kusa yanke saqa, ai da lamarin ki sun gama daidaita zan juya kan wannan me baqin jinin itama ai taimaka a samo mata wani zaman ya isa haka” ta fada tana Kallon Ummi. Se Ummi tai zarab ta miqe tana cewa

“Wa ni wallahi na yafe dadai irin Auran Amira kullum kina tafe ba biyan buqata gara in zauna banyi ba duk randa kika gaji kya barni na Auri Auwalu da nake so yake so na”.
Mafice Adda ta cilla mata tana auna mata Ashar
“Shegiya da bata gaji arziqi ba da dai wallahi ki auri wannan faqirin gara kiyi ta zama ina kallonki ba auran, duk yayan gidan nan wa kikaga ta auri ko Malamin Jami’a bare malamin makarantar primary”

“Wato Fatu bazaki dena yin munanan kalamai akan Yaran nan ba ko? Amma ki ci gaba ai kina gani Idan Alkahiri kike shukawa kanki koma akasin haka” Alhaji Murtala da basuji shigowarsa ba ya fada, be ko qaraso ba ya juya kawai dan yasan wani qarin bacin ran ze jawa kansa. Tun kafin ya fito da safe ta bar gidan haka duk a kunnensa Indo Tazo tayi tijarar ta dakyar Yaran gidan Maza suka lallaba ta ta tafi dan shi qin fitowa yayi. Ya gaji da halin masufar da Fatu take jefashi a kullum shi be san Adadin bashin daya biya mata, idan baazo yau ba gobe se anzo to ya gaji.

Yanzu ma maganar ya shigo ya mata akan ta nemi kudin matar ta bata idan ba haka ba tace gobe idan ta dawo da police zata zo to wallahi sedai su kulleta dan shi sisi baze sake biya mata ba ai badan ita kadai yake nema a rayuwarsa ba.
Adda kuwa ko a jikinta ta cigaba da gayawa Amirah yanda sukayi da malami da kuma tabbacin da ya bata da an gama ai Bashir ze dawo hannunsu.

“Amma fa Adda ni bana yarda idan akace wai Anty tana wa Yaya Bashir Asiri ke kanki Adda kin san ba haka bane”
Hararar ta Adda tayi kafin tace “Ji banza, idan tanayi se tace miki zata fito fili a sani ne? Ko kuma ace da batayi to daman me zatawa Asirin bayan kusan ita ce Mijin shi Matar yanzu kuwa daya bunqasa ai bazatayi sanya wata tazo ta taya ta ci ba. Ni in zaki karbi abu kiyi kawai kiyi kafin ki fara saka wasiqasi ki bata mana aiki dama ni ina zargin bakyayin yanda akace shiyasa komai baya tafiyar mana daidai to ke kika sani wallahi kina ji kina gaji zata kado ki waje ki dawo mujere ana mana Dariya” da haka ta shige dakinta dan yin Sallar Azahar da La’asar da suka sameta a tafe ga Magriba an fara kira.
Chapter 8 · 0% Book details