← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 158

Sashe 22

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asma’u kuwa hankali kwance suka isa gidansu wanda layi daya ne ya raba su da gidansu Bashir dan seka bi ta qofar gidan su Bashir din ma zaka shiga layin da gidansu yake da yake close. Cike da murna Seidu dan Baba Buzu daya daga cikin masu gadinsu tun na quruciya daya maye girbin Babansa yanzu ya wangale mata katafaren get din gidan na Alfarma ta shiga.

Tabbas gidan ya amsa sunan sa na Babban gida domin kuwa layi guda ne gidan haka tun daga get da katangar gidan zaka san cewa ba qaramin gidan me Arziqi bane. Tana gama parking a inda aka tanadarwa motoci gasunan birjik da alama yau akwai mutane da yawa a gidan yaran suka fita da gudu saboda hango cousins dinsu yaran Yayye da qannen Asma’u da sukayi se lokacin ta tuna yau Sunday kusan dukka yan gidan da suke a cikin garin Gombe Mata da Maza suna zuwa gida yau da iyalan su su wuni tun zamanin da Mahifinsu yake raye har yau kuwa basu fasa ba.

Seda ta gaisa da Samarin dake zaune a bakin get yawanci duk masu aikin gidan sannan ta shiga cikin gidan, part din Hajia Babba ta nufa dan a irin wannan lokacin tasan acan zata samu kusan kowa ai kuwa tana shiga katafaren palour nata fuskarta ta qara fadada da Murmushin ganin yan uwanta harma da wanda batayi zato ba.

Kai tsaye inda Hajia Babban take ta nufa Farar Bafulatana da a qiyasi ta bawa Sittin Baya amma jin dadin da take ciki ya boye shekarunta “Maraba Maraba da mutanen Lagos” take fada sanda Asma’u ta nufota, seda ta zauna dab da qafafunta tana daukar wani Dan yaro daya ruqo mayafinta da bata san ko dan waye ba sannan ta shiga gaisheta.

Cike da qaunar junan data ginu a tsakaninsu suka shiga gaisawa da sauran yan uwanta da suke a palour se tsiya suke mata wai ta qara kyau tayi wani haskee ta zama wanke ka taba ita dai se dariya kawai take musu. Suna cikin gaisawar Alhaji Qarami ya shigo Aliyu na take masa baya dan dama mutuminsa ne.

Gaishe shi tayi ya amsa mata cike da kulawa yana tambayarta aiki babu dai wata matsala ko tace babu sannan yayi wa Hajia Babba Sallama bayan yayi musu gajeriyar nasiha da tunatarwa daya saba yi musu a duk sanda suka hadu da yawa irin haka akan su riqe zumunchin da Mahaifinsu yasha wahalar gina su akai, seda yabi duk wanda yake zaune da dubu biyar suda yayan su kaf sannan ya musu sallama Driver sa ya ja shi suka wuce Abuja inda yake zaune da iyalansa. Ance daman babban wa makwafin uba to tabbas sudai sunyi dace dan kuwa Alhaji qarami ya maye musu gurbin uban da suka rasa.

A gaba ta saka yaran suka zaga saran part biyu na matan gidan suka gaisa Hajia Ummah da Hajia Anjin kafin suka wuce sabgarsu ita kuma ta koma part din Hajia Babba inda sauran yan committee suke jiranta a tattauna.

“Ke ashe Kishiyar ki ta haihu, dazu naji Abbas yana gaya wa Hajia Babba” Ikilima yayarta ta fada, seda ta cire yafinta ta ajiye a gefe ta zame dankwalin yayi baya sannan tace “wallahi fa ta haihu an mata CS jiya da daddare an ciro mata baby girl”

“Ayya CS ne Allah ya bata lafiya ya raya abinda aka samu” cewar Anty Hauwa matar yayansu Sunusi suka amsa da Amin gaba daya.

“Kinje kenan?”
“Naje mana daga can nake ma yanzu”

“Cab kuma kika kwashi jiki kikaje nifa wallahi Yah Asma’u kina bani mamaki na rantse da Allah in nice kallon banza yarinyar nan bata ishe ni ba bare na arziqi wallahi bazan je dubata ba, bata da mutunchi kwatakwata baki san abinda ta mana ba ranar sunan Rufaida(qanwarsu ce itama tana auran Yayan Amirah da suke uba daya) wai saboda bata da kunya ta kalle mu muna zaune wai bamu gaisheta ba idan Bashir ne ai dole mu gaidashi tunda mijin yar mu ne dan haka matsayi daya take dashi a gunmu ita Kishiyar yayar muce , wallahi Anty Habi ce kadai ta hanamu nada mata dan iskan duka ranar amma da se mun koya mata hankali” cewar Amina daga yanda take maganr zaka gane zallar takaicin Amirah da take ji.

Dariya Asma’u tayi tace “to ai se ku gaisheta meye a ciki zuwa dubiya kuma kema zakije dan ciwo na gaba da komai sannan ranar suna dole kuzo asha shagali daku”

“Tab Allah ya rufa asiri” Aminan ta fada tana tura baki. Dariya suka saka mata dan dama indai aka fara wannan dramar Amina bata da dama a fili take nuna jij zafin Amiran harma dana Bashir din dan ita fa tunda yai auran nan ta dena gaishe shi. Tace yanda beji kunyar ciwa yar uwarta fuska ba itama bazata ji kunyar dauke kai idan ta ganshi ba taqi gaishe shi.
Asma’u ta kance wai
“Amina inda kece a matsayina ban san me zakiyi ba” ita kuma tace
“Ai wallahi yah Asma’u da ko tsirena su Alhaji Qarami zasuyi na gama auran nan dan bazan koma ba”.

Ranar wunin dadi sukayi suka sha hirar su kamar karsu rabu, se bayan isha suka fara watsewa bayan tayi musu Alqawarin zata bi kowacce gidanta su gaisa da kyau tunda zata kwana biyu a garin.

Daga ita se Abdallah suka koma gida sauran yaran kowa ya kama gabansa dan daman idan suka zo indai ba tareda Bashir ba basa zaman gida in yana nan ne yake matsesu baya taba bari suje ko nan da can su kwana yanzun ma abinda yasa ta barsu yana cikin wannan digimi be zama lallai ma ya fuskanci basa gidan ba.

Seda ta biya Asibiti ta sake dubasu, a can din dai ta kuma samun sa kuma suka barshi sukayi gida yace se ya taho har suka kwanta dai be dawo ba seda Asuba sannan taji motsinsa dan a dakinta suka kwanta ita da Abdallan.

Washe gari Litinin Bashir yayi sammakon komawa aiki bayan yabar komai da zaa buqata hannun Naziru, ranar ma bata wuni gida ba, gidan Yaya Bilkisu taje da suke ciki daya kuma ita kadaice yanzu a Gombe Babbar Yayarsu Anty Suhaima tana America da mijinta se Junaidiyya da take Abuja sauran uku mazane biyun qannenta yan biyu Bilal da Nasir suna karatun masters a China se yayanta daya Muslim yayi aure tuni yana zaune a Rivers da matarsa da yaransu biyu da A Lagos yake shima akayi masa transfer.

Sosai suka sha hira da Yayar tata har dare kamar karsu rabu, sun yi sallama akan Nan da kwana 7 zasu tafi Yola tare gurin maman su dukda ita Asma’u taso nan da kwana biyu ta wuce amma Yaya Bilki tace ta bari se anyi radin sunan yar Amirah idan yaso ko bata samu taron sunan ba babu matsala amma yanzu in ta tafi ze iya zama abin magana ai a kan hakan suka rabu.

Haka taci gaba da zaga yan uwanta har ana i gobesunan Amirah bayan la’asar tana zaune ta jiyo hayaniya an bude get. Ta window palour ta ta leqa da mamaki take kallon su Addah dake fitowa daga mota da Amira tana takawa dakyar bata ga jaririyar ba tana asibitin ita har yanzu.

Bangaren Amiran suka nufa seda suka shige sannan ta koma ta zauna tana mamaki tasan dai yau za’a sallameta dan ya gaya mata da tun Jiya daya dawo amma batayi zaton nan zata dawo ba kodan yanayin jikinta amma ita meye nata. Seda tayi sallar isha da dogon hijabin ta a jikinta ta nufi part din Amiran da kulolin da ta zuba tuwo da miyar kukar da ta saka Amna tayi.

Seda tayi sallama uku sannan suka jiyota ta tura qofar ta shiga duk sukayi wani tsilli tsilli alamar basu da gaskiya da gulmarta sukeyi a lokacin ta shiga. Bayan sun gaisa ta sakeyi mata ya jiki yau dai ta amsa bata zauna ba tayi musu sallama ta koma gurinta.

Washe gari suna da Asuba a masallacin unguwarsu aka radawa yarinya suna taci sunan Addah Fatu, Asma’u na daki Farida take gaya mata Amma Anty Ummi tace Iman zasu ringa kiranta, setayi Murmushi kawai ta tuna sunan Farida da tace nan ma ya saka mata Maryam sunan mamanta tunda yace ba sunan Dada ze saka ba ce mata yayi shi bashi da ra’ayin yiwa wani takwara, ko Aliyu daya saka raayin kansa ne badan Aliyu Abokinsa ba kamar yanda ake zato.

Ana Abdallah kuwa cewa yayi ta siyi rago haka kuwa ta siya, haka aka yanka wa Baby Iman ragunanta biyu ba’ayi wani taro ba ranar tunda tana Asibiti har sannan sun dai qudurce a ransu fa se sunyi daga baya, dalilin ma daya sa suka dawo da ita gidanta kenan saboda duk abunda za’ayi ayi akan idon Asma’u dan Amirah tace shagali zatayi na kece raini.

Washe gari Suka soye naman su ko hanji basu Aikawa Asma’u da bama su san asubancin barin garin tayi ba ita da yara zuwa yola, suka rabe abinsu tas dan Bashir ma ya tafi tun safe kuma har nasa rabon suka cinye.

Toh maji ma gani dai.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 15

YOLA
Su Asma’u sun isa yola lafiya sun kuma samu tarba me kyau daga mamansu da suke kira da Goggo da bakinta yaqi rufuwa ganin yayan nata da kuma jikokinta a gabanta ba qaramin faranta mata yayi ba. Se sannu da zuwa take musu tama rasa wanne zata kama ciki idan ta janyo wannan yaron se saki ta kamo wancan su Asma’u har seda sukayi kwallar kewar Mahaifiyar tasu.

Seda suka nutsu sukayi sallolinsu sukaci abincin da Abokiyar zaman Goggon Innawuro ta kawo musu ga fura me sanyi da gardi sannan Goggo tayi musu jagora zuwa bangaren megidan su gaishe shi.
Chapter 22 · 0% Book details