← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 158

Sashe 59

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tare suka shigo da Bashir da kallo daya zaka masa kasan ba’a cikakken hayyacinaa yake ba. Idanunsa sunyi jajir sun koma ciki ga jijiyoyin kansa sun fito rudu rudu. Guri ya samu ya zauna ba tareda ya kalli ko gefen da nake ba, nima sau daya na kalle shi na mayar dakai ina ci gaba da share hawaye na dukkan mu munyi shiru se Baba ya katse shirun da cewa

“Bashir me ya hada ka da Asma’u har ta kai ga yanke irin wannan hukunci mara dadi, koda yake abinda ya faru ya faru dawo dashi bashida amfani dan haka koma menene haquri shine maganinsa dakai da ita duk kuyi haquri ka maida ita dakinta tunda da sauran zama bama se wani ya san Abinda ya faru ba”

Luguden duka qirjina ya shigayi na dago na kalli Bashir ina jiran naji amsar da ze bawa Baban, ina ma ace yace daman wasa yake yimun ba dagaske bane ba. “Daman ana saki da wasa ne” zuciyata ta raya mun, sena sun kuyar da kaina qasa ina jin wani abu me tauri ya taso ya tokaremun maqogaro daidai sanda Bashir yake cewa
“Ayi haquri kawai Baba amma ko zan maida ita ba yanzu ba, taje kawai lokacin data san muhimmanci na idan da rabo se mu koma”.

“Kai dai za’a gayawa haka Bashir kaine zaka san Muhimmancin Asma’u a lokacin da ta rigada tayi maka nisa, se kayi kuka da idon ka kayi nadamar da bazata amfane ka ba wallahi tunda baka godewa Ni’imar ubangiji ba ka shirya godewa Azabar sa” Anty ta fada cikin Masifa kamar zata rufe Bashir da duka kafin ta juyo kaina inda nake durqushe ina kuka tace

“Ke kuma kukan me zakiyi kanki aka fara sakin mace ko yaya idan wani yaqi ka da yini wani da shekara ma ze soka har zaki damu dan wani Bashir da dama can ba ajin auranki bane ya sake ki, in sha Allahu akan idonsa zakiyi auran da se ya gigita shi tashi muje” ta fincikeni muka shige dakin ta.

Bansan me suka tattauna da Baba ba ya shigo ransa a matuqar bace yana cewa “Lallai yaron nan bashida mutunchi Halima, yanzu ka saki mace da yaya shida har kana iqirarin ta bar maka gida a yau zaka kawo wata se yanzu na fuskanci kan abun daman akan ze dawo da kishiyarta nan ya saketa kenan, babu komai duk wanda ya cuci wani a cikinsu Allah ya saka mas.
kuje ki tayata ta hada kayanta zanje Management office yanzu naji yanda za’ayi su bada gidan”.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 32

Tareda Anty muka koma, Bashir na zaune a palour muka wuce dakina. Wayata dana gani ta tunamun da gida, wazan kira na gayawa wannan mummunan labarin??

“Alhaji Qarami” zuciyata ta raya mun, nan da nan na danna masa kira cikin sa’a ringing biyu ya daga yana cewa “wato a kwanakin nan dai Ma’u tana yi dani irin wannan kira akai akai haka”.

Kuka na fashe masa dashi sosai ya shiga tambayata ya akayi, dakyar na iya tsagaitawa na gaya masa cewa Bashir ya sake ni. Seda yayi salati ya sanar da ubangiji kafin yayi shiru na wani lokaci yace

“Ma’u kowa da kalar qaddarar sa a rayuwa kiyi haquri ki dauka jarabawa ce daga ubangiji idan kika jure se ki samu saka mako me kyau. Yanzu kina ina?” Alhaji Qarami ya fada cikin jimami, seda Naja sheshsheqa kafin nace

“Yace ya bani iya yau na kwashe kayana na bar masa gidan sa Yaya yanzu ina gidan kayan nake hadawa”.

“Shike nan, ki hada iya abinda ya samu, bari na kira Abubakar dan yace mun yau ze shigo nan din idan yaso ko hotel ne se ku zauna kafin gobe a duba miki gida zuwa muga yanda hali ze yi, ki dena kuka sannan karki kira kowa a gida ki gaya masa kinji ko”.

“Toh Yaya Nagode Allah ya saka da Alkahiri “ na fada kafin mukayi Sallama naci gaba da taya Anty hada kayan dan tuni ta sauke kayan wardrobe dina tsaf tana ta durasu a akwatuna. Seda muka kwashe komai dan seda muka Hada da manyan Jakunkunan Bakko da muke zubo abubuwa daga Gombe daman in na cire kayan ciki sena ninkesu na ajiye da rabon zasu min rana ashe. Har kayana na dakin Bashir seda ta kwaso komai bayan da tayi masa watsa watsa da nasa a qasa.

Da muka gama da nawa kayan dakin yaran muka koma, lokacin Bashir ya bar gidan suma muka shiga hada musu kaya kowa a akwati kafin wani lokaci mun gama Anty ta fita ta samo samari suka ringa dauka suna kaiwa gidanta.

Mun fito da akwatin qarshe kenan Yaya Abubakar ya tsaya da motarsa a qofar gidan, rabon da yazo tunda Bashir ya auri Amirah suka samu sabani sedai mu hadu dashi a gida idan naje Gombe ko muyi waya.

Kai tsaye na fada jikinsa na fashe da kukan dana samu dakyar ya tsaya mun dazu yana bubbuga baya na yace “kiyi shiru Ma’ulle abinda yake so kenan yaga gazawarki bayan shi yayi asara bake ba”.

Tare dashi muka shiga gidan Antyn muka tarar da Baba ya dawo, cikin mutun taka suka gaisa Baba ya shiga bashi haquri akan abinda ya faru kamar shi yayi laifin sannan ya gaya mana ya samu approval an bani gidan kuma harda 50% discount akan kudin hayar ma suka bayar kuma ya biya yanzu ze kira kamfani masu wankin gida suzo su gyara yanzu se muje mu ga gurin ga Key nan an bashi.

A tare muka fita gaba daya, gidan lafiyar sa qalau dan daman ba’a dade da renovating nasa ba qura kawai yayi se yana saboda babu mutane a ciki, muna tsaye ma sega kamfanin daya kira sunzo da kayan aiki cikin qasa da awa daya suka wanke gidan tas har bangwaye seda suka wanke ko ina ya dauki kyalli.

Bansani ba Ashe tunda muka shiga Yaya Abubakar ya kira Alhaji Qarami ya gaya masa maganar gidan, se ganin motar kayan furnitures nayi sunzo da saitin gado da kujera harda labulaye da carpet kamar wasu kayan Amarya nan da nan suka shiga daurawa.

Muna fito wajen gidan motar makaranta ta sauke su Aliyu, da mamaki suka tsaya suna kallon gidan Farida tace “Mami gida zamu chanza naga ana saka sabon kaya a nan”

Gaba daya kasa kallonsu nayi dan ji nayi wata sabuwar karaya tana zuwar mun, yaya zasu ji idan suka gane mun rabu da mahaifinsu? Fitowar da Yaya Abubakar yayi daga cikin gidan ta ceceni daga tambayoyinsu suka nufeshi da murna nan take na sulale na shige gidan Anty ban san Aliyu yana baya na ba seda naji ya ruqo hannuna yana cewa

“Mami meya faru, kukan me kikeyi?”
Aliyu ya wuce shekarun da zance zanyi masa wayo, kai tsaye ina hawaye nace masa “Aliyu mun rabu da Abbinku, kuje ku duba idan akwai sauran abinda ban dauko muku ba a dakin ku wan can gidan zamu koma”.

Gaba daya se yaron ya kasa magana ya tsaya yana kallona, a sanyaye ya saki hannuna ya juya ya fita daidai sanda Itama Aman ta shigo ina jinsa yace mata suje waje na raka su da ido har suka fice daga gidan.

Rayuwa kenan, dan Adam yana tafe besan abinda ze same shi a mintunan da suke gabansa ba, dazu da safe na tashi da yaqinin gyaruwar Al’amura a tsakanina da Bashir, ga labarin abin farin cikin daya same mu bansan mummunar qaddara na tafe tana shirin shafe duk wani farin ciki da nake shiryawa ba.

Shafa cikina nayi, Allah sarki shi kuma tasa qaddarar kenan baze tashi a tsakanin iyayensa ba.

Da taimakon yaran kafin sallar Magriba mun shirya gidan nan tsaf yayin da muka yiwa gidan Bashir qat dan kaida fata Anty ta kafe sena dauke duk abinda yake nawa ne a cikin gidan nan haka kuwa akayi yara suka ringa jidar kaya qananan se murna suke wai mun chanza gida.

kayan Kitchen dina tsaf Gas da qaramar Freezer da muke zuba nama kadai aka bari dan sune nasa babbar me qofa Biyu Yaya Muslim ne ya bani ita da suka tashi daga gidan su na Lagos ya koma Rivers, haka kayan amfani ko ko cokaci Anty bata bari ba harda su spices seda ta tattare.

Haka palour Kujeru da Da Tv se Dining kadai ya tsira dasu sefa gadon dakinsa dan na dakina ma da kudina na siya, wanda ya saka mun shi na cire na sakawa Farida da Amna a dakinsu dan haka masu daurin Gado na gama hada sabon Anty tasa suka hau kwanto nawa tace ko baze hadu a yau ha su kwance a ajiye gobe su dawo su hada.

Har bayan Isha muna jigilar kaya daga tsohon gida zuwa sabo, mungama tattaro komai wanda ze saku a lokacin muka saka ragowar muka barwa gobe idan Allah ya kaimu se a qarasa.

Na fito raka Yaya Abubakar ze tafi masaukinsa daidai lokacin Bashir ya dawo, tundaga waje ya fahimci aika aikar da akayiwa gidan dan ga winduna nan hanhai babu labule ana hango ciki, a sukwane ya shiga gidan, kai tsaye dakin yaran ya leqa ya kuwa yi sa’a se katakwayen gadajen su ya tarar dan mun kwashe katifun saboda bacci a zuwan gobe suma se a dakko su.

Cikin tsananin Bala’i kamar zeyi aman wuta ya tunkaro inda muke
“Ke kadai nace ki tafi bance ki daukar mun yaro ko daya ba” ya fada yana kallona.

Seda na watsa masa wani banzan kallo kafin nace
“Wannan ne kuma kayi kadan Wallahi Bashir, saki dai na saku kuma kamar yanda kace na barmaka gida kafin gobe gashi nan ka gani Allah be hanani inda zan zauna ba amma maganar yara baka isa in bar maka yarana a hannunka ba”.

Sosai rigima ta barke tsakanin mu shi yana rantsuwar sena bashi yaransa ni ma ina ta bazan bayar ba, Yaya Abubakar ne ya katse mu da cewa “Ya ishe ku haka, wane irin shirme ne zaku zo kuna neman tarawa kanku mutane a titi ga yara duk suna kallon ku akan abinda be wuce ku zauna ku sasanta ba.
Ki shiga Gida Ma’u zamuyi magana”
Chapter 59 · 0% Book details