← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 158

Sashe 74

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin jin Maman Ahmad kawai nayi bawai na dauki abinda take fada da muhimmanci bane dan na yarda a zuciyata Bashir baze taba kallon Amirah a matsayin mace ba balle har yayi sha’awar auranta.

Yarinyar da banda kyara da tsangwama babu komai tsakaninsa da ita har haushi nakeji idan yayi mata wani abun, barar magi na bawa Amirah idan har na kuskura Bashir ya sani to ranar baze ci abincin ba saboda yanda yayi mata tambarin qazanta balle har takai ace ze aureta na tabbatar wannan ko a mafarki ba abu ne me yuwuwa ba.

Shigarta SS3 yasa ta qaro wani sabon tsagwaron rashin kunya da fitsara. Ganin ta takeyi kai daya dani dan yanzu idan na gaya mata magana ma se ta ga dama zata aikata, fita kuwa ko Bashir ze kasheta idan ta dawo setaje daman tuni ta sallama Islamiyya ta dena zuwa qarin daurin gindin data samu a gurin Addah harma da Dada kanta dan sunce data kammala makaranta aure zasuyi mata dan haka dole a barta ta fara tsayuwa da samari ta samu wanda zasu daidai ta a ciki.

Nima banqi ta tasu ba tunda har aure za’ayi mata ya kamata a barta ta farayin zancen dan haka koda Bashir yace sedai tabar masa gida ko kuma in zatayi zancen ta ta tafi gidan su se nace masa baza’ayi haka ba.

Dakyar na lallashe shi ya yarda sedai ya kafa mata sharadan kar ta kuskura ta mayar masa da gida centre tara samari duk randa ya ga sama da mutum biyu suna zuwa gurinta se ya mugun saba mata daga nan ta fitar da wanda take so a ciki ta sallami daya amma da yake me kunnen qashi ce kullum da wanda zata gayyato yazo gidan.

A cikin samarinta akwai wani Yaro Sadam, irin fitinannun yaran masu kudin nan ne. Tana bala’in sonsa musamman yanda yake mata barin kudi duk sanda zezo haka ze ciko ledoji niqi niqi da kayayyaki ya kawo mata sannan haka zebi su Aliyu da kudi idan sukaje suka gaida shi wani sa’in harni yake shiga ya gaisar,

yana da kirki amma idonsa a bude yake na kuma tabbatar ita kanta Amiran ba dagaske yake son ta ba duk yanda kuma naso na nisar da ita qarshe dukda ba kai tsaye ta fada ba se jin ta nayi tana cewa duk baqin cikin mutane seta auri Sadam da kowa ze ringa wani ce mata ba auranta zeyi ba, daga ranar na cire bakina a sabgar samarinta, Allah Allah nake ma ta qarasa makarantar ayi mata auran kowa ya huta.

Bazan taba manta wata rana da mukaje gidan Dada ba, akwai wani Lace me kyau da tsada da nayi mana nida Amiran da Amna harda Farida da sallah shi muka saka ranar mukaje.

Muna zaune kamar an matsi bakin Addah se cewa tayi “Baku ganku ba wallahi Abin sha’awa kamar wasu Uwar gida da Amarya”.

Ban kawo komai ba a raina nayi murmushi muka yi hirar mu muka gama, har mun tashi zamu tafi Addah take cemun

“Ni kuwa wata shawara nake nema Asma’u, kinga nida Nafi mu kenan shaqiqai da iyayen mu suka haifa, gara ita ma Allah ya bata yaya da yawa ni kuwa kin gansu nan biyu kamar kunnuwa.

Shine nayi wani tunani ina so ko bayan ranmu zumunchin Yarana da nata ya dore kinga ta hanyar Auratayya ne kadai hakan ze tabbata. Toh yanzu ina so na gabatatar mata da maganar cikin yaranta maza daya ya nemi Amirah ko ya kika gani?”

“Kai Amma kuwa kinyi tunani me kyau Addah idan abin ya yiwu kuma zakuji dadi wallahi Allah ya tabbatar da Alkahiri yasa zamu ga lokaci” na fada sak da zuciya daya dan dagaske naga kyan tunanin ta, Auran zumunchi yana da dadi idan yayi kyau.

A lokacin tunanina gaba daya kan Amiru ya tafi dan shine me shirin aure a sannan amma kuma sam basa shan inuwa daya da Amirah saboda rawar kanta.
“Idan Allah ya qulla abun haka zasu shirya su zauna tare” na raya a raina.

A haka muka ci gaba da lallabawa har Amirah ta fara rubuta Jarabawar fita daga sakandire lokacin ina da tsohon cikin yan biyuna.

Daman iya WAEC tayi, dan haka suna gamawa ta tattara kayan ta ta koma gidan Addah haka kawai ba tareda wani abu ba, nima ban takurata ba, nadai tambayeta ko wani abu aka yi mata tace Aa daga nan na barta ta tafi.

Ranar da na haifi yan biyu ranar Bashir ya samu aiki a wani Babban Oil company a Lagos. A tsakanin watanni uku Alhaji Qarami ya tura masa da Advert dinsu yace ya cike, yana rashin mutunchi da fadar maganganun sa dai ya cike din cikin ikon Allah kuma da yake se a sannan rabon sa ya tsaga se gashi suka gayyace shi Interview shine yanzu kwasam muna Asibitin sun aika masa da Email cewa sun dauke shi aiki.

Fadar irin farin ciki da murnar da muka shiga ma bata baki ce, Allah kenan me kyauta da qari a kuma sanda yaso. Lokaci daya ya bashi kyautar yara har biyu sannan ya qara masa da tukuicin Aiki me gwabi irin wanda ya dade yana fatan samu se gashi ya same shi a sanda be taba zato ba.

“Albarkar yan biyu kenan, yanzu Legas din zaka koma kenan? Daman ina so naje legas nima naga yanda take yanzu tunda dana zeje kaga na samu gidan zuwa” Addah ta fada cikin murna kamar ta taka rawa musamman jin yanda su Amiru suke ta zuzuta irin aikin da Bashir din ya samu da kuma Albashin da ze ringa kwasa a wata.

A ranar aka sallamo ni na koma gida, da Daddare Bashir ya shigo dakina, fuskarsa dauke da murmushin da na dade banga irinsa ba. Seda ya dakko yan biyu daga cikin gadonsu kafin ya dawo kusa dani ya zauna yana kallona yace

“Wane suna kike so a saka musu”
Se da na kama baki ina yar dariya nace
“Tofa, yaushe aka fara haka? To bana dai bani da kudin siyan raguna har hudu dan haka ka saka musu duk abinda kaga yayi maka”.

“Kina so ki ringa dawo da abinda ya rigada ya wuce, dagaske nakeyi, ki zabar musu sunan da kike so kin cancanci fiye da haka ai” ya fada yana kallona.

“Toh Daya dai a saka masa sunan Baba dayan kuma na bar maka zabi”

Da daddaya yayi musu huduba, seda ya gama ya miqo mun Hassan yace “Ga Ahmad” sannan ya bani Hussain shima yace “Muhammad Tukur”.

Sosai naji dadin karar da Bashir yayi mun ta saka sunan Alhaji Qarami dan kuwa ya cancanci sama da haka a gurin mu.

Wannan haihuwar dai nayita da qafar dama dan sosai Bashir yayi bajinta ya gwangwaje ni da zadaddun sururu na fitar suna haka yaran ma akwatunan su tsaf aka ciko da kaya, ga kuma kayan takwara da Alhaji Qarami ya jido mana abin dai se sam barka haka shagalin sunan da mukayi kansa bazakace haihuwa ta biyar bace tamkar sunan Aliyu da akayi shi lokacin ina cikin gata na a gidan wannan kuwa ya samu qarin tagomashin cigaban zamani.

Tuni Bashir ya kama aiki a Lagos bayan da ya dauki leave a tsohon gurin aikin sa a matsayin ze tafi qaro karatu saboda baka barin aiki kai tsaye har sekaga kamun ludayin wanda ka samu tukunna. Shi kadai ya tafi Lagos duk qarshen wata yake zuwa Gombe.

A cikin shekara daya da fara aikin Bashir rayuwa ta qara sauya mana sauyi irin na Alkahiri, ba qananun kudi yake karba a Albashin sa ba sannan ga Kasuwancin mu da Allah ya sakawa abin Albarka tuni mun sake bude branches guda biyu bayan na farkon a wasu unguwannin ga kuma harkar siyar da baqin mai daya kafa bayan daya fara sabon aikinsa ya zamana yana supplying daga kamfanin zuwa gombe ya rabawa yan sari abin dai se godiyar Allah kawai.

A shekarar ya biyawa Dada da Alhajin su Aikin Hajji suka tafi tare da shi kansa bayan sun dawo ya sake biyawa Addah da Anty Amina Babbar yayarsu harda Amiru sukaje Unarar Mauludi.

Bayan dawowar su Addah da sati daya sega Amirah ta dawo mun harda jakar kayanta bayan kusan shekara guda da barinta gidan, yanda sanda zata tafi ban hanata ba haka yanzu ma data dawo ban tambayeta dalili ba ban kuma chanza mata ba muka ci gaba da zaman mu kamar baya.

Abun daya fara hadamu bayan ta dawo wasu halayen data tsiro dasu, Duk lokacin da Bashir zezo gari yanda zanyi shiri nayi kitso dasu lalle haka Amirah ma zatayi tamkar matar gidan taci kwalliya itama ranar da ze dawo ta kame a palour.

Sannan a da idan har Bashir yana gida indai bashi ya zaunar dasu ba da daddare daga mun gama cin abinci zasu shige dakinsu tunda ko wanne daki na saka musu Tv idan ma kallo ne zasuyi acan wannan karon kuwa tun dawowar ta idan muna zaune itama zata nemi guri ta zauna ne babu ruwanta.

A ranar farko data fara zaman dakansa ya mata magana ta tashi hakan be hana washe gari ta sake zama ba har tana tsoka baki a cikin hirar da mukeyi nan ma yayi mata kaca kaca kafin aka samu sa’ida har ya tafi basu sake haduwa guri daya ba.

Wani rainin hankali data samu ma se ina waya da Bashir din zata zauna ta tasa ni a gaba tana kallo, idan nayi mata magana se tace mun wai

“Wallahi Anty soyayyar ku da Yaya tana bala’in burgeni shi yasa nake zama nayi kwas, Kai Allah nima ya bani miji irin yaya mu kwashi romon soyayya”.

Wani lokacin kuka tace “Dan Allah Anty ki ringa koyamun yanda zan mallake zuciyar mijin da zan aura nima na zama kamar ke a gurinsa ya ringa riritani irin yanda Yaya yake miki” idan ta fadi haka se nayi dariya nace

“Nidin har wani riritani Baban Ali yakeyi kenan, miji kuma ai banga kin dakko hanyar samun sa bama dan ni rabon da naga kinyi waya da wani a gidan nan ko anzo gurinki har na manta man Amirah anya lafiya?”
Chapter 74 · 0% Book details