← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 158

Sashe 125

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallama ta sake maimaita masa fuskar ta dauke da murmushi seya dakata daga bude motar yana qare daure tasa fuskar ya amsa ciki ciki yana kallonta.

"Sunana Zulaiha, kayi haquri fa na tsayar dakai, tun dazu naga shigowarka. Alamun ka sun nuna kana tareda damuwa qarara. Idan kana da maganin damuwarka kayiwa kanka idan kuma baka da shi to koma menene yake damunka ka fawwalawa Allah yin tagumi da zama shiru bazeyi maka magani ba" ta fada cikin murmushi tana kaiwa qarshe kuwa ta juya ta barshi a tsaye kamar ta dasa shi.

Jiki a sabule ya shiga motar, harya kunna ta kuma seya kashe cikin dakiya da jarumta ya danna kiran lambar Abubakar dan har seda ya kulle ido kafin ya kira ringin daya biyu uku aka daga Abubakar yayi sallama daga bangarensa.

Cikin faduwar gaba Bashir ya amsa sukayi shiru gaba dayansu kafin can Abubakar yace

"Wayake magana ban gane lambar ba"
"AB goge lambata kayi? Bashir ne fa" Bashir ya bashi amsa a sanyaye dan jij ko lambarsa ma bashi da ita.

"Ayya Yi haquri kasan mutanen da yawa wanne Bashir kenan? Kayi mun bayani yanda zan gane".

Seda yaja fasali a ransa ya maimaita La'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin kafin yace

"Nasan ko baka da lambata ai muryata bazata bace maka ba, Bashir ne dai naka kuma Mijin qanwar ka Ma'u".

"Eh to nawa Bashir din dai ko banga lambarsa ba na haddaceta akai (sunada qani Bashir) sannan cikin qannena babu wadda take auran Miji me suna Bashir gaskiya.
Ok  kace Ma'u ko? To Ma'un dana sani a gidan mu ma bazawara ce bata da miji sedai ko idan tsohon mijinta kake nufi sunansa Bashir" Abubakar ya fada cikin irin lafazin nan na ko a jikina.

Shi kuwa Bashir har wata zufa ce ta shiga keto masa. Toh ta ina ma ze fara masa magana jin irin wannan amso shi da yake bashi yana nuna masa cewar babu sauran wani abu tsakanin su kenan yama manta dashi a babin rayuwarsa.

Daurewa yayi muryarsa har tana rawa rawa yace
"Am Abubakar na sani abubuwa da yawa sun faru a baya da sedai nace kayi haquri laifi na ne kuma na karbi kuskurena in sha Allahu zan gyara dalilin ma daya saka na kiraka yanzu kenan na baka haquri akan komai aya faru sannan na nemi shawarar ka akan yanda ya kamata na gyara sauran kura kuraina".

"Toh a taqaice dai ni abinda zan iya ce maka shine kasan hausawa sun ce yanda aka dama haka za'a sha, to nima sedai na maimaita maka hakan nace maka ka koma gefe kawai ka nade hannu ka karbi duk wani sakamako a yanda yazo maka Malam Bashir, batun laifi kuma ni bakayi mun komai ba.

Idan zan tuna ka gaya mun babu ruwana da sabgar gidanka ko dan kana auran qanwata bashi ya bani damar gaya maka abinda zakayi da wanda zaka bari ba, tundaga sannan na sake tsoka bakina a cikin sabgar gidan ka?
To na menene yabzu zaka sako ni kuma?

Ita abotar ka yanke ta tuntuni, auratayyar ma ka sakar mun qanwa to me yayi saura a tsakanin mu yanzu babu dan haka dan Allah karka sake kirana akan wani shirme naka can idan ba haka ba kaga yau na amsa ka a mutunce ko, ka tabbata idan ka sake a ranar zaka gane kuskuren ka zan sauke maka fushin shekara da shekaru dana shanye ban nuna maka ba" yana gama fadar haka ya kashe wayar sa.

Ajiyar zuciya Bashir ya sauke dan ya tsammaci fiye da hakan ai to tunda ma aka tsaya anan ai ya gode Allah har ya samu kwarin guiwar sake tun karar sa kuwa idan aka kwana biyu.

Hanyar Asibiti ya dauka ko ba komai Ya kamata ya je ya duba yanda ta kwana gashi har rana ta kwale yanzu. Yana isa tun daga farkon ward din yake jiyo tashin muryar Addah cikin masifa ga wata muryar da be tantance ta waye baita kuma ana yarbanci da alama itama masifar takeyi, kansa ya sara masa yaji kamar ma yayi kwana ya fasa shiga.

Ya akayi tazo da wuri bayan ya gayawa Samuel se yamma zeje ya daukota sannan ita dawa take fada a Asibiti kuma? Badan kar taje ta jajibo masa wata fitinar ba da juyawa zeyi ya barsu su qarata amma dole ya qarasa cikin dakin daidai sanda matar da suke fadan ta jefowa Addah irin qaramin flask din shayi na silver akayi rashin sa'a ta goce ya fadi tim akan qafar Bashir daya shiga dakin tsautsayi ashe be rufu da kyau ba kuwa ruwan zafin ya kele masa a qafa ga zafin buguwar da yayi ga azabar ruwan zafi besan sanda ya fasa qara yana sakin wayarsa da muqullin da suke hannunsa ba suka fadi qasa.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 56

“Innalillahi Addah ta qona shi” Amirah dake zaune akan gado ta dora hannaye biyu akai tana fada.

“Kan bala’i kika qona shi To wallahi kin taro ruwan dafa kanki daman ni kika so ki la’anta kenanAllah ya kareni tsiyarki ta fada akan Dana ai kuwa bazamu yarda ba daganan har kotun qoli” Addah ta sake hayayyaqowa matar dake tsaye tana numfarfashi.

Irin shinqimemiyar nance ta gaske, itama cikin masifa da yarbanci ta hayayyaqowa Addahn, wato da gani fadan a duhu akeyinsa dan babu me gane yaran wani a cikin su gefe kuma ga Nurses biyu da suna ta faman bada baki amma ko wacce ta kafe taqi haqura.

Cikin radadin Azaba Bashir ya juya ya fita daga dakin dan har seda ya cire takalmin qafar da ruwan ya zuba. Kai tsaye dakin likitan da yake duba Amirah ya nufa yana dingisa qafa suka ci karo dashi a hanya

“Yawwa Engineer wannan wace irin mata ce ka kawo mana gaba daya tazo ta tayar wa da mutane hankali kamar ta manta Asibiti tazo? Muji ka fita da ita kuma karta sake dawo mana. Kai itama matar taka bari kawai a rubuta muku sallama idan yaso ta ringa zuwa daga gida ana dubata kawai” Likita ya tare Bashir tun kafin shi yayi masa magana.

“Ka taimaka ka fara dubamun qafata farko ruwan zafi suka watsa mun” Bashir ya fada yana zama a kan kujerar dake gaban Office din likita, se likitan yayi saurin durqusawa ya kama qafar yana haskawa, Dakin wanke ciwo suka tafi Allah ya so shi qunar iya sama ce dan haka magani kawai aka saka mishi ya rubuta masa wanda ze siya yasha sannan ya gaya masa ya dan dakata da saka takalmi saboda karya takura fatar ta kwaye.

Saboda baqin ciki ko dakin be sake komawa ba yayi tafiyarsa gida a ransa yana ayyana irin abinda zeyi musu daga Addan har Amiran idan suka dawo masa gida.

Hajia Addah kuwa abinda ya faru Bayan ta dawo daga gidan Ma’u ranta a jagule da irin tarbar da Ma’un tayi mata. Sam bata taba tsammatar haka daga gareta ba saboda yanda tasan Ma’u da haba haba da lamarinsu ada idan suka je gidanta kamar zata goyasu saboda kirki amma yau ita tayiwa wannan korar kai tsaye ba tareda wata shakka ko shayi ba koda yake ada Suruka take a wajenta a yanzu kuwa babu sauran alaqa sedai ta kara kawai ai.

Babu abinda ya qara tayar mata da hankali irin nutsuwa da kyan da taga Ma’un ta qara ga uwar daula data zuba a gidan ta dan yafi na Bashir din sau biyar wallahi jifa wasu kujeru tana zama akai taji ta ta lume qa qamshi ta ko ina duk se taji ta raina gidan Bashir yanzu data dawo ba kamar zuwanta dazu ba da ta ga gidan kamar wadda taje wata Villa yanzu kuwa se taga duk ya zamar mata wani qauye dama ga rashin gyara gaba daya dai abin ya zama se a hankali.

Tana zaune ta zabga tagumi Aliyu nata buga Game dinsa dan be nuna alamar ma yaji shigowar mutum ba sega sallamar Jafar da kwandon Abinci. Bata jira ya qaraso ba ta taro shi dan dagaske yunwa takeji, badan bazata gane ta inda suka shigo unguwar bama da fita zatayi tunda da yan kudinta a jaka ta nemi abinci to Lagos kuma abinci ai se kalar wanda ta zaba zataci.

Haka ta zauna tana ci tana zubawa Ma’u Albarka seda ta cinye kwan nan tas da sinqin biredi ga qaton kofin data zuba shayi tayi gyatsa kafin ta dakko wayarta tana kallon Jafar tace

“Kai Allah dai yawa uwarku Albarka yasa kuma kuji qanta, ungo nan ka duba zakaga wata lamba da aka kira qarshe ta wani qedari ce da ubanku yace ze zo ya kaini Asibiti na duba Antyn ku kirashi maza kace na shirya idan kuma zaka rakani to se mu tafi tare”.

Lambar Samuel Jafar ya nemo ya kira ya gaya masa saqon Addah, yana qunquni ya amsa gashi nan zuwa dan dazu daya dakkota har suka Zo tana zabga masa masifa dukda bajin abinda take fada yake ba amma yasan zaginsa takeyi.

“Kai nima dai Jafaru zaka fara koyamun turancin nan tunda naga garin gaba daya kowa shi yakeyi karna fita wata rana na manta hanyar gida na rasa waze dawo dani” Ta fada tana dariya bayan daya miqa mata wayar yace Samuel din yana zuwa.

“Allah yasa na ki fitan ki bata daman yan yankan kai na garin nan sunfi son irin ki masifaffun tsofaffi ai” Aliyu dake gaban Tv ya fada ba tareda ya juyo ya kalle ta ba, nan kuwa ta hau sababi tana fadar sedai a sace uban sa badai ita ba shege me baqin hali. Dake dangado ne kuwa ya manna mata hauka tayi tayi ba ita ta haqura ba seda Jafar ya gaya mata ga Samuel ya dawo sannan ta fita, tayi tayi su tafi tare yaqi dan yana Tsoron Maminsa haka ta kama hanya tana ci gaba da mitar ta.
Chapter 125 · 0% Book details