← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 158

Sashe 136

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ma'u wata magana naji da hankali na ya kasa nutsuwa da ita wai aure zakiyi" ya fada bayan da muka gaisa. Sena kalle shi yanda gaba daya yabi ya rikita kansa duk ya sukurkuce gayun nan da yakeyi da yanzu babu da alama ko hutawa ma beyi ba yana dawowa ya taho nan dan rigar saman kayan sa kadai ya cire.

"Toh ashe labari ya iso maka a ina kaji?" Na tambaye shi da dan murmushi a fuskata seya zaburo kamar ze sauko daga kujerar da yake yace

"Bangane ba kina so kice mun da gaske ne Ma'u aure zakiyi? Wane irin Aure? ki zauna da wani namiji bani ba ko hada soyayyata da ta wani a zuciyarki?"

Seda na gyara zama dakyau na dora qafa daya kan daya ina girgiza su kafin nace

"Aure kala nawa ne Bashir? Shi din dai wanda ka sani na mata da miji da zasu zauna a qarqashin inuwa daya.
Batun na zauna wani namiji kuma da Mace yar uwata kake so na aura ko yaya? Ita kuma soyayya ai yanzu tashi ce kadai a cikin zuciyata tuni anyi waje road da taka tsohon labari kenan".

Miqe wa tsaye yayi har yana tunkude kayan Lemon da aka kawo masa suka zube a qasa ya nunani da hannu yana cewa

"Qarya kike Asma'u bazaki taba son wani Namiji a duniya ba bayan ni idan ma zakiyi aure da gaske sedai kiyi kawai amma badan so ko jin dadi ba ina kuma tabbatar miki da cewa duk ma inda kike tunanin zakije sekij dawo dan zuciyarki bazata taba aminta da wani bayan ni ba wannan alqawari nayi miki"

Ko a jikina na miqe tsaye nima ina kallonsa cikin ido nace
"A lokacin dana nuna maka kaine rayuwata Bashir ka dauka shirme nake ban san kaina ba a sannan, a yanzu kuwa ka bude mun ido ka kuma bani damar da nayi karatun sanin matsayina da abinda ya cancanta dani.

Oh wai fata kake mun nayi aure na sake dawo maka? Toh ai tunda na iya zama da kai da halinka Bashir ni kuwa wane kalar miji ne zan gagara yin haquri dashi zance ma kawai kake yi wannan" ina gama fada nayi gaba zan bar gurin yayi saurin shan gabana tareda riqo hannuna, kallon dana jefa masa na kayi hauka ne yasa shi saurin sakina yaja baya yana cewa

"Kiyi haquri naji koma menene ki gaya mun duk abinda bakya so zan dena wallahi nidai kiyi haquri ki dawo dakinki muci gaba da zama kinji wallahi bazan iya rayuwa babu ke ba".

Ni kuwa kaga yanzu ma na daura danbar rayuwa ba tareda kai ba, kai ni ai yanzu bama zan iya maimaita zaman da nayi a baya dakai ba Bashir kaje kawai ka zauna da matar da Allah ya zaba maka ka barni nima na gwada wata rayuwar haba karka zama me son kanka mana"

"Ma'u dan Allah..."
"Dan girman Allah Bashir ka fita, da nasan wannan maganar ce zata kawo ka ma da tun da safen munyita wallahi base kazo ka tasani gaba da magiya ba ko da dole ne nace bana so bazan koma ba ka qyale ni mana idan kuma kana da qarfi seka dauke ni aka ka maida ni gidanna ka haba" na fada a hasale dan ya ishe ni kuma.

"Shikenan seki shirya ganin gawata dan duk ranar da kika auri wani bani ba nasan daga lokacin rayuwa ta zata zo qarshe".

"Allah ya jiqanka, karka damu su Aliyu bazasuyi maraici ba" na fada ina wuce shi. Ina ji a jikina yanda ya bini da kallo harna shige daki.

BASHIR

Jiki a sanyaye ya kama hanyar gidansa yana tunanin wai shi mezeyi Ma'u ta dawo masa?
Ya gwada duk yanda akace masa yayi nasa dabarun amma duk a banza kullum ma sake botsarewa takeyi a maimakon ta sakko. Yanzu mutum biyu suka rage masa da yake ganin zasu iya shawo kanta daga Babansu se Alhaji Qarami.

Kai shi yana kunyar Alhaji Qarami wallahi abinda ya masa a rayuwa ko darajar wannan yaci ace ya dagawa Ma'u qafa koda ita ta takaleshi yaci ya dauke kai. Baban dai ze kira tunda dai ai duk tsiya ubansa ne bakuma ze zabi Ma'u akansa ba kuma ai shima yana son zamansa da ita dan haka ze saka baki ta dawo masa.

Wayar Baban ya kira amma Dada ta daga take gaya masa yana bacci saboda jikinsa ya matsa kwana biyu. Shi se sannan ya tuna da zancen kudin maganin da ze tura musu gashi account dinsa yayi qasa sosai saboda hidimar sallah da yayi kuma wata ya raba balle ya saka rai da zuwan Albashi.

"Kai komai ma ya rikicewa mutum kudin kansu sun dena Albarka kamar wanda ake kwashe su" ya fada a fili bayan da yayi wa Sa'ad transfer abinda ya samu na siyan maganin, dan abinda ya masa saura baya zaton ze rufa masa watan gashi za'a koma makaranta biyan school fees kadai ya ishe shi yana ganin dole seya karfi wani abu a kudin super market saboda biyan kudin makarantar dan da wuya ya taba kudin idan an hada lissafi ribar sake mayar da ita ake se idan ta qure masa ne yake taba wani abun a ciki.

Yana shiga gida ya tarar da Amirah na murqususun ciwon ciki kuma, kai Jama'a haka suka kwasa se Asibiti likita ya ringa fada akan wai wani abun tasha irin magungunan Hausa, daya matsata qarshe take gaya masa wai magani Addah tasa aka aiko mata daga Gombe a qaryar su na zaqi ne tunda cikinta ya shiga kusan wata Bakwai yanzun shine ta karbo mata zancen gaskiya kuwa sabon malami ta samu ta hannun Anty Talatu ita tayo musu aiken saboda sun gaya mata sun rasa kan Bashir din zaman dai se a hankali.

Ya kuwa ringa bala'i kuwa yana cewa Idan wani abu ya samu cikin ita ta sani babu ruwansa tunda ita bata tausayin kanta haka suka dawo bayan da aka bata magunguna su kansu seda ya kashe kusan dubu Hamsin a daren.

Kwana biyu a tsakani aka kirasu a waya cewar Ummi ta haihu ta samu ya Mace amma ta koma murna Addah ta ringayi tana hamdala da  akace yar ta mutu sedai murna ta koma ciki jin wai an daurawa Ummin aure da dai shi mijin da bata so ta aura din dan daman seda sukayi yarjejeniya da iyayensa akan tana haihuwa za'a daura aure suka yarda dan haka ana kiran Alhaji Murtala daga can Katsina inda ya kaita gurin wani Amininsa cewar ta haihu ya tashi ya tafi gidan su saurayin ya gaya musu. Ana sallar Azahar kuwa a masallaci aka daura musu aure se saka ranar da zata dawo ta tare.

Kusan Sati guda gaba daya Bashir ya zama gashi nan ne, abubuwa sun rikice masa duk yanda ya dauki shawo kan Ma'u da sauqi abinya shallake haka nacin yake roqon yake amma kamar wanda yake shika dusa dukda shima dai da tasa irin wautar.

Wani irin biko yakeyi me kamada fin qarfi saboda a duk sanda ya tashi yi mata magana nuna mata yake kamar ya zamar mata dole bazata oya rayuwa babu shi ba dan haka ta haqura ta dawo masa wanda sam shi be dauki hakan da wani laifi ba gani yake kamar yana tuna mata da girman soyayyar da take tsakanin su ne wanda ita kuma wannan abun shi yake wara qona mata rai take jin dole ta barshi ko dan ta nuna masa cewar ba tare aka dauro rayukansu aka aiko duniya ba.

Ana saura sati daya a koma makaranta kamar yanda aka saba suka tura mata da Takardar biyan kudi saboda daman lambar wayarta ce akai in an turo mata seta turawa Bashir din ya bada kudin.

A yanda aka saba an samu qarin kudin makaranta ga kudin littattafai saboda sabuwar shekara aka shiga za'ayi canjin aji ga kudin jarabawar WAEC da NECO da JAMB na Aliyu da ze shiga aji shida dan haka da aka hada lissafin sega kudi sun tasarma kusan Miliyan biyu.

Ita kanta seda ta jimanta wannan al'amari ta rasa abinda yasa makarantar suke haka basa bada notice na qarin kudi sedai kawai idan an kawo maka teller ka gani kamar wadanda suka bawa iyayen yaran ajiya koda yake makaranta ce ta yayan masu dashi suma karanbani ya saka suka kai yayansu ai.

Ta Whatsapp ta tura masa da takaddun lokacin yana zaune a Office be dade da gama waya da Amirah ba da take masa zancen kudin siyayyar haihuwa gashi jikin Alhajin su ya qara zafi dan shirin kaishi Kano akeyi ma Asibitin Malam nan ma dai duk wani lissafin kudin ne dai yanzu ga wannan ubannin kudi na makaranta kuma sun taso masa duk a ina ze qwaqulosu?

Wai to ta yaya da duk yake hidimomin sa har ya samu rara a asusun sa ba taredaya girgiza ba? Albashinsa Miliyan daya ne duk wata saboda babu Fansho babu garatuti idan ka gama banda sauran alawan da suke samu kala kala musamman yanzu daya samu qarin matsayi packages harda na banza basu ake dan haka yake facakarsa baya ma lissafi bare ya ajiye na buqatar kota kwana tunda kudinna shigo masa koda yaushe daman Super markets dinsa Gombe sune tanadin Bayan Ritaya wanda se a yanzu yake hango tarin gatan da Ma'u tayi masa data saka shi a harkar kasuwanci nan dan yanzu ba qaramin habaka jarinyayi ba tunda ba'a tabasu duk ribar da  aka samu ciki a ke maidata.

Text ya tura mata akan ayi masa haquri kafin a koma ze bayar nan ya shiga hado ta inda zasu fito, dole dai ya karbi kudi a gurin Sa'ad din idanyaso daga baya ya mayar dan su makaranta babu ruwansu ba jira zasuyi ya samu ba shawarar daya yanke kenan a take kuwa ya kirashi akan yana san ya karbi miliyan uku se Sa'ad din yake gaya masa sunyi sarin kaya, kudin da suke dasu a qasa ko Miliyan daya bazasu kai ba na banki kuma ze dauki lokaci dan yamamta account din ya samu matsala ta yanda sedai kudi su shiga amma bazasu fita ba dan haka dole sedai idan zeje Gomben da kansa ya gyara tunda shine signatory din.
Chapter 136 · 0% Book details