Sashe 118
Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Madam yame jiki? Allah ya qara sauqi toh".
"Amin" ta amsa can qasa dan gani tayi ya mata kwarjini kafin ta wurga ido gefen da Ma'u take tsaye kaman anyi mata dole tace
"Anty Ina wuni?"
"Lafiya lau, ya me jiki?" Asma'u ta amsata ba tareda ta kalle ta ba.
"Baban Ali ya qarfin jiki? Allah ya qara afuwa" Ma'u ta fada tana kallon Bashir daya zubawa Yusuf ido ganin yanda shi Yusuf din ya kafe Ma'u da wani mayan kallo kamar ze cinyeta.
Ji yakeyi kamar ya tashi ya shaqe Yusuf din kowa ma ya huta, yanzu da wannan kwalliyar ya dakko ta suka taho yana shaqar qamshin turaren? Abinda yake mallakinsa yanzu suke rabawa tareda Yusuf din.
"Asmy muje ko? Dare yana yi kuma kinga ko zama bamuyi ba muka taho" Yusuf ya fada cikin kwantar da murya kamar me magana da yaro, murmushi Ma'u tayi masa ta fara tafiya tana cewa
"Allah ya qara sauqi, Aliyu ku debo kwanukan safe ku taho dasu" tayi gaba abinta ba tareda ta sake kallonsa ba se yaran suka miqe suna yi masa seda safe suka fice gaba daya banda Aliyu.
"Zoka kwashe wannan abin daya shigo dasu" ya fada yana nuna masa ledar Fruit da kajin da Yusuf ya siyo ko yaya akayi ya gane shi ya siya se Allah.
Juyawa Aliyun yayi ya kalli Uban kafin ya bankawa Amirah harara ya juya ya fice abunaa ba tareda ya dauke ledojin ba.
"Kana kallonsa yana hararata ko? Wallahi sena ci uhan yaron nan zamu koma gida ne. Daman jiya ni kadai suka bari na kwana a gidan ka kirasu ma ka gaya musu..."
"Tashi ki fita" ya fada a tsawace har seda ta zabura ta miqe, har tayi gaba ta koma ta dauki ledar kazar tana cewa
"Idan bazaka ci ba ni na dauka dan daman banyi girki ba dazan fito" tayi gaba abinta tana ci gaba da qunquni.
Samuel da tuntuni yake jiranta a reception ya miqe rai bace ya fita tana binsa a baya, a kusan tare suka isa gida dasu Ma'u, saboda bala'in sa ido a qofar gidan ta tsaya.
Tana hangen Ma'u da Yusuf suna magana kafin sukayi sallama ya shiga motarsa Driver yaja suka wuce.
A kan kujera ta jefar da dankwali da jakarta ta zauna, gaskiya bazata sabu ba, ta yaya za'ayi ace daga rabuwar Ma'u da Bashir har ta samu madadinsa kuma dan gayu me kudi da take ganin kamar yafi Bashir din komai da komai wai me yasa a duk sanda take ganin ta taddo Ma'un seta sake tsere mata ne?
Dole ta tashi tsaye, bazata zuba ido tana kallo Asma'u tayi gaba ba, tunda har ta rabu da Bashir tana fatan ta qare rayuwarta a haka tana kallonta a matsayin da da ita take kai(Fata na gari lamiri Amirah )
ASMA'U
A qofar gida muka tsaya bayan da yara duk suka shige ciki, Kallona kawai Yusuf yake yana murmushi har seda na gaji nace
"Ni zan tafi dare yayi kuma gobe ina da aiki"
"Toh agogo, ni ban gaji da kallonki ba ai" ya fada yana gyara tsayuwa.
"Ai kuwa an kusa rufe gate kaga kwanan mota ya kamaka yau a cikin Estate" na fada ina juyawa kamar zan tafi yayi saurin shan gaba na yana cewa
"Haba hajjaju ki barni mana na kalleki, gobe fa zan tafi se nayi sati daya ban sake ganin fuskar nan taki ba".
Kamar yarinya haka na tura baki ina hararar sa qasa qasa, se ya faramun dariya yana cewa
"Kinga Asmy ta tana dawowa yanda na santa a hankali, shikenan ki shiga ki kwanta kiyi bacci amma fa kiyi mafarki na".
Murmushi nayi masa na kauce ina cewa "seda safe mun gode da zuwar mana dubiya kuma"
"Dole na dubashi dan kinsan yanzu banida masoyi sama dashi, tunda ya iya sako mun ke ai ni ya gama mun komai a rayuwa. Ina ga gobe ma zan koma na sake dubashi kafin na tafi"
"Allah ya yafe maka" na fada ina bude qofa se yayi saurin dakatar dani ya koma gurin motar sa, wata yar qaramar leda ya miqo mun na karba ina mamakin meye wannan a ciki dan qanqantar ta tayi yawa".
Godiya nayi masa na wuce, ina jin yanda yake bina da kallo har na shiga gida na kullo qofar kafin ya shiga motarsa suka tafi.
Ban tsaya ba na wuce dakina dan yaran da alama sun kwanta ma, ian shiga na zare rigar jikina ya rage Doguwar riga ta roba me siririn hannu da na saka a ciki na fada kam gado na zazzage ledar da Yusuf ya bani.
Yan qananan akwatuna ne suka fado guda biyu, na dauki na Farko na bude, wani hadadden zobe ne a ciki tsabar handa ya burgeni ban san sanda na ciro shi na zura a hannuna ba yanda ya zauna seka rantse an gwada ni kafin aka qera shi, juya hannun na ringayi ni kadai ina murmushi.
Kamar ya sani ina son zobe musamman wannan ya tafi dani, dutseb da yake ka sa ma se na ga kamar Diamond wallahi amma ya za'ayi Yusuf ya siya mun Diamond ring.
Dayan akwatin na bude shi kuma yan kunnene qanana sosai maqale dan kamar zallar dutseb nema akayisu dashi, ban bata lokaci ba na cire na kunnena na saka su.
Qanana ne sosai amma idan kaga yanda suka yi kyau a kunnena seka dauka wani babban dankunne na saka. A daren nan na ringa daukar hoton kunnena da zoben, na rasa wa zan nunawa ina shiga whatsapp naga Alawiyya a online ban bata lokaci na kuwa na tura mata da hotunan se gashi ta kirani ina dagawa ta fasamun ihu a kunne tana cewa
"Ma'u Allah ya bamu ya taki, kin shiga zawarci da qafar dama. Ashe ina da rabon ganin Diamond ido da ido a duniya ai kuwa zanzo kallo a cikin satin nan".
Dariya sosai na ringayi, indai tsokana ce ka samu Alawiyya ka gama, ban gama dariyar ba ta sake cewa
"Gobe idan zaki aiki ki saka hannun nan a gaba yanda kowa zega menene a jiki su san fa Yar uwata ta faso gari wallahi"
"Aa cire hannun zanyi nakai Museum kawai kinga afi zuwa kallo dakyau" na fada mata.
"Ke tsaya ma wai waya baki ni inata murna ban tambayeki ba, ko da yake qila nasan Yarabawan Lagos din nan ne ko kin san daman ance sun iya kashewa Mata kudi kamar hauka, nidai dan Allah ina daga gefe ki ringa tunawa da yar uwarki kinji"
"Allah ya yafe miki Alawiyya, ni seda safe wai ina Baban Dija kiketa wannan ihun a daren nan?"
"Ni ki gaya mun dan Allah wa kika samo mana" ta fada tana marairaicewa, kamar an fizgo maganar daga bakina se ji nayi nace mata
"Yusuf Wunti ne"
Ta buga ihu har seda nayi saurin cire wayar daga kunnena ina jiyo yarinyar da take goyo Afifa ta fasa kuka da alama itama ta tsorata.
"Wallahi a satin nan se nazo Lagos wannan maganar bata waya bace kai Allah na gode maka Allah na gode maka, kwanta kiyi bacci yar uwa qila gobe ki ganni kawai dan bazan iya jira ba" Ta fada cikin tsananin murna kamar wadda akayiwa kyauta kafin ma nayi magana ta kashe wayarta, murmushi nayi a fili nace
"Allah ya shirya ki Alawa"
Har na ajiye wayar se kuna na janyota na shiga rubutawa Yusuf saqo
"Nagode kwarai amma da baka wahalar da kanka ba"
"Zan iya kira?" ya dawo mun da amsa, kamar nace Aa se kuma zuciyata ta ce mun baze ji dadi ba dan haka na mayar masa da amsa
"Eh" se gashi kuwa ya kira din.
"Bana so na kira ki fara mun qorafin bacci zakiyi amma da bamuyi magana ba nasan ni yau sedai nayi kwanan zaune kawai" ya fada a hankali.
"To ai yanzu seka kwanta tunda munyi magana"
"Yanzu kuwa ranki ya dade, karki manta kiyi mafarkina zan kiraki da safe ki bani labari".
Haka mukayi sallama na kwanta rigingine ina tunani, yanda Yusuf yake yi mun tamkar wasu saurayi da budurwar da suke kan ganiyar soyayya ganai nakeyi kamar ma ya manta da na taba aure harda tarin Yaya.
Ian daga kwance ina ta faman saqa da warwara, idan naji kamar zuciyata zata karbi tayin Yusuf se kuma dayar ta bijiro mun da Bashir, ganin kaina na neman yayi ciwo yasa na tattara su duka na watsa gefe na gayyato baccin dole ina ta kallon zoben hannuna da yake qyalli a cikin duhuj dakin.
Zumbur na tashi na zauna na kunna fitilar wayata na haska cikinzoben sosai, tunawa nayi a jikin akwatin naga wani Rubutu kamar Letter A da Y anyi musu wani irin design daya ta shiga cikin daya kuma kamar na hango hakan a cikin dutsen ma ina haskawa kuwa sega wasu qanann rubutu da seka nutsu sosai zaga gansu cikin dutsen
'Yusuf loves Asma'u' aka rubata, kamar yarinya haka na qanqame hannun nan nayi bacci dashi.
BASHIR
Wani irin zafi da ciwo zuciyarsa ta ringayi masa, a da tuna kalmar saurayi da Aliyu ya gaya masa kadai take tayar masa da hankali a yanzu daya Gansu a tare bashi da buqatar qarin bayani fuskokinsu kadai sun isa shaidar alaqar da take a tsakaninsu, yanzu daman Asma'u zata iya son wani namiji a rayuwarta bayan shi??
Yanzu harta manta da rayuwar da suka gina tsahon shekaru a yan kwanaki ta iya mantawa dashi ta karbi tayin wani Namiji bayan shi abinda ko a mafarki be taba tunanin faruwarsa sannan har ta iya zuwa gabansa dan ta nuna masa cewar a yanzu fa baya gabanta ta tigada ta gama da shafin rayuwarsa gaba daya.
Dafe qirjinsa yayi saboda azabar ciwon da yake masa, tun yana zaune har seda ya kwnata saboda yanda wani ciwo ya masa rubdugu lokaci daya ya shiga numfarfashi kamar me shirin mutuwa, hankali tashe Likita da Nurses suka rufu akansa domin ceto rayuwarsa.