← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 158

Sashe 17

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fita Amirah ta shiga kiran Addah a waya tana dagawa ta sakat mata kuka tana cewa “Addah kin gani ko nace miki bazan iya ba kince sena mata magana gashi yanzu na bata komai”

“Dan ubanki me kika ce mata a garin yaya? Rashin hankalin naki kikayi ko ni wallahi na rasa wace Asararriyar yarinya ceke da komai baki iya siyaya da kissa ba se wauta da rashin hankali kika saka a gaba yanzu me kika ce da ita?”

Tsaf ta gaya mata yanda sukayi da Dadan, Ajiyar zuciya Addah ta sauke kafin tace “Ni na zata ma wani babban abu ne rabu da ita na lura Nafi so take ta kware mana baya amma bata isa ba wallahi yanda ta saba tursasashi yayi abu yanzun ma haka za’ayi. Ki kwantar da hankalin ki ki rabu dasu muna zaune se ya dawo ya dauke ki wallahi in sun san wata basu san wata ba kedai yi qoqari ki amshi wani abu a hannunsa a turawa Malam a qarasa aikin nan Idan muka samu yanda muke so ko ita Nafin se mun so zata ganshi” fanfo ta cigaba dayi mata da bata dabarun yanda zata wanki Bashir din kafin sukayi Sallama.

Gajia tayi da zamanta zame takwanta akan kujera bacci ya kwasheta, Bashir kuwa se qarfe goma ya dawo gidan, seda yaje sukayi sallama da iyayensa kafin ya shiga palour ya ganta harta fara bacci. Tashinta yayi suka tafi basu koyi sallama da Dada ba. Da suka isa gida ma kwanciya tayi dan baccin yaci qarfinta.

Washe gari tun Kafin a kira Assalatu ya tashi Amirah, tana qunquni tana komai seda yasa ta gyara ko ina dukda beyi datti ba tunda kwana biyun tana kula da komai. Qarfe 6 suka sauketa a qofar gidan Addah, be shiga ba dan haushin Addan yakeji haryanzu dama basu sake haduwa ba tun waccen ranar dukda har kasuwa yaje ya gaida Baban Amiran kamar yanda yakeyi duk sanda ya shigo gari, duk yanda Amiran taso ya shiga wi yayi yace ta gaisheta kawai sauri yake qarfe 7 jirginsu ze tashi sannan ya kawo 50k ya bata sukayi sallama Naziru ya kaishi Airport ya juyo da motar.

Murna gurin Addaha kaman wanda ya basu 50M. Shi dama bame kyautar kudi bane idan ze tafi dai komai ze ajiye mata na amfani sanda tana zama a gidanta Ummi taje ta tayata zama. Da ta koma tafiya gida ma be fasa ba duk qarshen wata ze sa akai Buhun shinkafa carton din taliya, macaroni da Indomie harda Mai da Maggi ga Kayan Tea sannan in ze tafi ya bata 10k kuma duk sati yana saka musu Katin waya na 1k ita da Asma’u Idan kuma zataje Asibiti Nazir ne ya ke kaita ya dawo da ita.

“Yanzu cire Goma ki riqe a hannunki bari na kirawo Malam ya turo a karba in kuma A Akawun za’a saka masa toh. Nidai Alkahiri ya hada mu da Me Keken nan shekara da shekaru muna yawon rabar da kudin mu a banza babu biyan buqata kinga rana daya mun tsinci dami a akala” Addah ta fada tana qoqarin kiran wayar Malam Wizy, kira Daya biyu ana ce mata Switch off amma bata lura bama se sake kira takeyi, wayar ta miqawa Amirah tana cewa

“Ke jimin me matar nan take cewa be wayar taqi shiga”

“A kashe take Addah” Amirah ta fada bayan ta sake kira.

“To bari mu saurara zuwa anjima na sake kira dan bazanyi wasa ba gara ayi wuta wuta a gama aikin nan bari ma Babanku ya fito inaga yau ze bamu ribar mu duk na hada a tura masa kawai a qarasa”.
Ita dai Amirah neman guri tayi ta kwanta dan bacci ne fal idonta.

Har kusan Magriba Addah na gwada layin wizy baya shiga, seta kalli Amirah dake cin Abinci a gefenta tace “Bari kiga na kira Hajia Balaraba itama tunda muka dawo ba waya da alama ta samu kan gidan se muji idan ta kama gobe mu koma kawai ko da abinda ze qara bamu ma” kai Amirah ta daga mata kawai nan ta maida akalar kiran kan Hajia Balaraba sedai itama kamar Wizy waya a kashe harta gaji ta bari akan Gobe idan Ummi ta dawo zata karbi Number Ruqayya a gurinta (Ummi tana gidan yayarsu da suke uba daya ta haihu).

Gidan Hajia Balaraba

Waccen ranar yanda suka watse suka barta ta dade a zaune a gurin tama rasa tunanin me zatayi, wai itace bata da Sa’a ne ko kuwa aikin Malam ne beyi ba? Tana zaune tana tunanin me zatayi, wannan hukuncin da Alhaji ya dauka yayi mata tsauri da yawa ta yaya ma za’ayi ta zauna bazata fita neman taimako ba? Dole da sake idan dama taqi se a kona hagu ai saqesaqen yanda zata wanke kanta ta farayi a zuciyarta har zuwa sanda taji Alhaji ya sake fitowa daga dakinsa. Cikin qarfafawa kai guiwa ta miqe tana cewa

“Alhaji kayi haquri wallahi sam ba abinda kuke tunani bane, kafin gida ne na karbo mana ba kuma iya dakinta na saka ba wallahi kaga kwana biyu unguwar nan anan fama da sace sace shi....” kallon da yake binta dashi ya sakata hadiye sauran maganar ta. A tare suka juya Gurin Dining da Ruqayya ke qoqarin zuba tuwo abinta dan tana wanka bata ma san wainar da aka toya a gidan ba.

“Mayar da miyar nan Ruqayya ki miqomin harda na shayun” ya fada murya a dake dan dukda be gani ba ya tabbatar ta saka wani abun aci ba kuma ze bar kowa yaci ba dan ba yau ta saba ba ita idan ta tashi abun tana ma ba kansa kadai yake tsaya wa ha kowa da kowa take hadawa na gidan.

Karbar flask din yayi ya shige kitchen dasu Hajia Balaraba naji tana gani ya kwarara miyar a sink din ya bi da ruwan Tea kafin ya dauraye ya kora ruwa. Idon sa ne ya sauka kan wani flask daban a ajiye ya janyo ya bude, murmushin takaici yayi zargin sa ya tabbata duk sanda tayi irin haka seta ware nata daban be bata lokaci ba ya dauka tareda sabon plate da spoon se koma Dining.

Tuwon sa ya diba ya zuba miyar ya miqawa Ruwayya ragowar yai shigewar sa daki ya bar Balaraba a tsaye da baqin ciki goma da ashirin, abincin ne sauran taqamarta taso ta lallashe shi yaci gashi yanzu ya zubar da miyar wadda ta ajiyewa kanta kuma ya kwashe duk wuyar da taci tayi girkin nan me kyau amma bata da rabo sena baqin ciki bata san sanda hawaye ya fara zubo mata ba kamar yarinya.

Dakin ta ta shige tayi kukan ta me isarta ta share, ta kuma quduri niyyar ko bataje da kanta ba se tayi aike daga yanzu ma bazata qara karbar aikin da zatayi dakanta ba gara ta samu wanda ze yi mata komai da kansa bate ma har ta kuskure asake kamata.

Washe gari tana zaune Alhaji ya shigo dakinta, wayar ta na hannunta tana shirin kiran Addah ta gaya mata yanda akayi su kuma yi shawara ya shigan. Hannu ya miqa mata ta bashi wayar cikin mamaki ta miqa masa tana tunanin to me kuma ya fatu yanzu? A gaban ta ya cire layin ya balla, kafin ya kalleta yace
“Wallahi ko da wayar wani kika karba kikayi amfani da ita ki kira wani Boka Ban yafe ba” ya sa kai ya fice ya barta da baki a bude.

Matakan tsaro na gaske ya saka mata ba waya ba fita ita ma kuma ya hana kowa zuwa gurinta har kuwa da Yayanta da suke gidan aure. Ruqayya kanta cewa yayi ta tattara ta koma Hostel haka me aikinta yace karta dawo ta zauna ta qara hutawa na wani lokaci duniya fa tayiwa Hajia Balaraba zafi Raba zafi inuwa quna gashi babu abokin shawara ita da Alhaji kuwa sedai tajiyo qarar bide qofarsa ko rufewa.

Seda Addah ta jera kwana biyu tana kiran Hajia Balaraba da Wizy dukka bata samu ba, ranar Talata ta yanke shawarar zuwa gidan nata ta gano ko lafiya.

Dakyar da sidin goshi Me gadi ya barta ta shiga shima seda tayi masa qaryar Ita Yar uwar Hajia Balaraba ce suna ta kiran wayarta ba’a samu shine tazo taji ko lafiya, be barta ba seda ya kira Alhaji ya shaida masa sannan yace ya qyaleta ta shiga.

Halin da taga Aminiyar tata ya girgiza ta nan ta shiga tambayar ta meya faru, Hajia Balaraban na kuka ta shaidawa Addah komai harda sharadin da Alhaji ya gindaya mata.

Addah tayi buqwi tana sauraronta kafin tace “Ikon Allah kinga dama akace magani dace ne to ni kuma kinga dai mun dace wallahi dan yanzu lafiya lau abubuwa suke tafiyar mana. Kema din nasan akasi aka samu wannan shegiyar ta ganki amma da abubuwan sun kammalu na tabbatar yanzu wani zancen ake ba wannan ba Allah dai yajiqan Malam na kan tufu shine Maganin Fitinannen Alhajin nan naki mtsw” taja tsaki kafin ta dora da cewa

“Yanzu dai ai cewa yayi idan kika qara zuwa ko a sharadij nasa shikenan kiyi zamanki ni zan koma insha Allahu za’a gyaro komai base kinje ko kunyi waya ba”

Cikin jin dama dama Hajia Balaraba tace “Yawwa Aminiyata shiyasa nake qaunar ki wallahi yanzu to zaki gane gurin? Dan Allah idan kinje ki gaya masa so nake ayi mun maganin Alhaji yafi da kamuwa yanda ko kara na ajiye ba ze tsallake ba ke ko magana in banace ya bude baki ba karya yi”.
Da haka sukayi Sallama Addah ta kama hanyar zuwa Gurin Malam Wizy.

Tiryan tiryan ta nunawa Me Adaidaita hanya har qofar gidan Malam dan Addah akwai gane hanya, da dan mamaki ta kalli shagon na Malam Wizy da ta gani cike da kayan provision ana siyar wa. Gaba tacewa Me Adaidaita ya qara ko basu zo gidan ba sedai har suka kai qarshen layin suka jiyo babu wani gida me kama dashi ma.

Fitowa tayi ta tsaya dason tabbatar da nan din ne gama dakalin da suka ga yaran nan a zaune ranar, qarasawa tayi gurin me shagon suka gaisa kafin tace
Chapter 17 · 0% Book details