← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 158

Sashe 12

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon ta yayi yana dan Murmushi kafin yace “Koh?”
Seta amasa masa da sarar sa tace “Uhm” tana qoqarin kauce masa a ranta tana mita. A zaman shekara Goma sha shidda baza ta tuna ranar da a karan kan Bashir ya budi baki ya yabi kwalliyar ta ba tun tana qorafi idan tayi se ta tambayeshi tayi kyau sannan ze yaba har ta gaji ma ta dena, yanzu da yaranta suka girma kuwa indai tayi kwalliyarta se sunce Mami kinyi kyau shiyasa ma ta dena damuwa da yabawar Bashir dukda abun da zafi amma ya zakayi (Mazan hausawan Mu Allah ya shirye ku dai 🥺🥺).

Wuce shi tayi ta shiga dakinta itama ta daura Alwala shi kuma ya hada kan yaran suka fita. Data idar da sallah zama tayi ta qara gyara fuskarta dakyau sannan ta fito, sun zauna a Dining da gani ita suke jira dan haka ta qarasa gurin.

Seda tayi serving kowa sannan ta zauna suka fara cin abinci kowa na santi karma Bashir yaji labari dan kunnensa har motsi yake. Besan yawan abincin daya nada ba seda ya qara saka serving spoon ze debo abincin a karo na uku bayan wanda ta zuba masa yaji wayam aiko suka kwashe da dariya suna kallonsa. Seya bata fuska kamar yaro yace

“To ai yunwa nake ji for almost a week fa bamu ci abincin Mami ba, please Mami karki kuma tafiya ki barmu, we are so sorry mun ji jiki wallahi, we missed you alot”.

“Zobon da Asma’u ta kurba ne ya sarqe ta ba shiri ta watso shi tsabar yanda mamakin kalaman Bashir suka nemi kasheta a zaune.

“Bashir dai data sani ne yake wannan maganar?” Kai ita kam badan ciwo ba dadi ba da tace ta ringayi duk wata ko Allah ze saito mata Bashir zuwa abinda ta dade tana fata.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 8

To Aka ce mata da Miji se Allah dan kuwa Ma’u da Basharin ta suna qulewa a daki sukai muqus aka shiga sharafin soyayya dan dama an dade ba’a hadu ba qarshe har makara tashi bacci sukayi. Safiyar ranar duk su biyun da ka kallesu zaka san suna cikin walwala.

Ta cancada kwalliyarta da skirt and blouse na Atamfa komai ya fito se juyi take tana saka kwakwalwar Bashir jijjiga. haka ta hada musu breakfast me rai da lafiya suka ci suka wuce makaranta dukda sam be so yau ta zama ranar aiki ba ya so ace suna gida yau yaci duniyar sa da tsinke ya more amma ba komai ai Gobe Friday zasu hadu.

Suna fita Qarasa yan abubuwan da suka rage mata tayi kafin ta shiga dakin ta ta kwanta dan huce gajiyar da Bashir ya tara mata, “Bashir is too good” ta ayyana aranta. Wato yasan ta yanda duk ze wanke laifinsa ta wannan fanni gwanin malami neda ta tabbatar samun irinsa se an tona.

Tana tsaka da tunanin shauqin daren jiyan ta jiyo qarar door bell da kuma ringing din wayarta. Wayar ta fara jawowa ta duba, Anty ce matar ogan Bashir dake Flat din da yake kallon nasu, seta miqe tareda daukan Qaramin mayafi dan dankwalin kanta ya zame.

A palour suka zube tare da Anty da ta farayiwa Asma’un tsiya tun daga qofa”

“Kai Ma’u kinga wani kyallin goshi da kike daga fitowa daga Asibiti har za’a maida wani kenan”. Daria Asma’u tayi tana cewa

“Haba dai ai na gama nikam wadan nan ma sun isa Allah ya raya mana sisi na kwai zan ci gaba dayi”

“Inafa kika gama kedai ki shirya dan qila wasu biyun ne a tafe”

“Ba amin ba Anty” ta tare Antyn.
Gaisawa sukayi kafin Antyn tace mata

“Shekaran jiya na dawo wlh se dare ma nashigo Honey yake cemun Ai kina Asibiti ba lafiya, har zamu zo jiya da magriba kuma yace sun hadu da Baban Aliyu a Masallaci ya ce masa kin dawo gida”

“Eh wallahi jiya da rana aka sallamoni ai gaskiya Anty kinsha gida kusan 3 weeks fa” Asma’u ta fada.

“Ki bari kedai zama nayi na huta nayi gyara sosai dan anan ba wani lokaci kake samu ka baje yanda kake so ba mutum na saka maka ido” cewar Anty tana bawa Asma’u hannu suka kashe

“Kai Anty a ringa tausayin Baba na dai karki qarasa mana tsohon mu”

“Ke barni fa dole na kwaci kaina sarai kin san Uwargida na bata wasa da gyara dole nima na zage kar a raina ni.

Hira suka shigayi Anty ta shiga fito da abubuwan da tayo wa Asma’u tsaraba tana cewa “Gashinan se a ci gaba da gashi ban ce ki raga masa ko na second daya ba atoh” suka tuntsure da dariya Asma’u tana cewa “Anty baki da dama”. Se wurin 12 sannan ta mata sallama ta tafi bayan ta rakata qofa ta dawo tana tattare kayan zuwa dakinta a ranta tana qara jin qaunar Antyn dan yanda ta dauketa take kula da ita kamar qanwarta da suka fito ciki daya.

Anty Suwaiba matar Engineer Abdullahi Gusau ce ogan Bashir.
Itace Matar sa ta biyu uwar gidan ta ma anan Lagos take da zama amma ba unguwarsu daya ba. Mace ce me tsananin kirki dukda ta dan girmi Asma’u amma yanda take mu’amalantarta kaman qawaye ko shaqiqan yaya da qanwa suke dan tunda suka fara haduwa jinin su ya hadu da Asma’un.

Ita kanta Asma’u tana ji da Antyn dan Ita tunda suka hadu rabon da tace ta siyi wani abun gyara da kudinta, a koda yaushe Anty cikin yo musu aike kaya gangariya daga Zamfara garinsu take kuma duk sanda Asma’u ta tambayeta nawane ta biya seta nuna bacin ranta. Ta kance da Asma’un
“Ni a qanwa na dauke ki, banida kowa a Lagos seke yanzu”.

Wasu daga cikin kayan ta fitar ta fara amfani dasu a ranta tana hasaso haduwarsu da Malam Bash dan tasan yau kam se tafi jiya Armashi. Kafin ta gama an kira sallar Azahar dan haka tayi alwala tayi sallar sannan ta kwanta zuwa La’asar kafin tasan abinda zata dafa musu kuma.

Couscous tayi musu da miyar hanta ganin lokaci ya qure, setayi marinating kifin da zata gasa musu su qara dashi zuwa can anjima kafin a kwanta. Yauma batayi wasa ba gurin cin kwalliya ta daukar magana dan har tafi ta Jiya. Wasu riga da skirt ta saka na kanti Oxblood da suka kama jikinta kamar tanayin nishi zasu yage. Bata daura dankwali ba ta faka dogon baqin gashinta daya sha gyara se qanshi yake yi kafin tabi kowanne lungu da saqo na jikinta ta shafe da hadaddun turarukanta da ita kadai tasan wadanda take mixing da duk bala’in kwakwkwafin mutum baze taba cankar wane turare bane.

Abaya ta fitar Baqa tareda mayafinta ta ajiye a gefe saboda yaranta maza ne, dukda qanana ne tana takatsantsan da irin shigar da zata fita gabansu da ita. Qugin motarsa data jiyo ya sakata saurin dora abayar ta yafa qaramin veil dinta akanta tareda zura slippers din ta ta nufi waje dan ta taro su.

Bashir
Fitowarsa daga mota yayi kyakykyawan gani, Ma’un sa ce kamar wata yar budurwar Balarabiya, tundaga nesa ya fara shaqar qamshin da takeyi wanda be taba jin sa a jikin wata mace ba bayan ita. Tamasa kyau yanda tayi rolling mayafin ya zagaye kyakykyawar fuskarta tareda bayyar da gaban gashinta daya ke nan luf a kwance ya qara qawata kwalliyar tata.

kallonta yake har besan sanda wayar hannunsa ta subuceba. Yana jin yanda yaran suke zuzuta kyan da tayi amma nasa bakin kamar wanda aka sakawa qaton kwado a ka kulle ya kasa koda budeshi se idanu daya zuba mata kawai.

Qarasawa gaban sa tayi ta durqusa tareda dakko masa wayar da ya yar bata miqa masa ba se jinta yayi gaba daya ta rungumoshi, saitin kunnensa ta furta “Welcome home SH (sweet heart)”. Kamar wanda ta tsoma a ruwan qanqara haka ya daskare a gurin yana jin kamar ya shide saboda muryarta da kuma numfashinta daya sauka a cikin kunnensa. Hannunsa ta kama ta zura masa wayar kafin ta juya tabarshi da shaqar qamshinta, batayi ko taku biyar ba taji an janyota ta baya yai mata wata kyakykyawar runguma tareda sauke mata kiss a gefen wuyanta da mayafi be ida rufewa ba.

Zaro ido tayi tana riqe hannunsa, “Baban Ali a waje fa muke” ta fada ganin gogan na neman kauce hanya 😂 se a sannan ya farga dan shifa a lokacin ita kadai yake gani se kuwa yaja hannunta qii suka shige cikin gidan dan tuni yaran suka kama gaban su. Mantawa yayi da batun wata yunwa da gajiya daya kwaso suka shige dakinsa kai tsaye , ai be ida birkicewa ba seda yai arba da ainihin kwalliyar Ma’unsa tuni labari ya chanza 🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️.

Basu fito ba se qarfe goman dare, Babu kowa a palour alamar yaran harsun kwanta. Ma’u da duk tayi laushi ta nemi kujera ta zauna Bashir kuwa Dining ya wuce dan se yanzu yake jinsa kamar ze fadi saboda yunwa. Ya manta sam rabonsa da abinci tun na safe. A Babban plate ya juyo dukka abincin ya sakko da shi inda take ya ajiye sannan ya koma ya dakko kwanon Fish din da Amna ta gasa.

Yana ci yana bata a baki har suka cinye se wani tarairayarta yakeyi kamar kwai, yanda yake rawar jiki da ita se yake tuna mata da lokutan baya a sanda yana Bashir din Ma’u kafin zaman majalisa da sababbin abokai ya sauya mata shi zuwa wani mutum na daban. Tana tuna irin gata da tarairayar daya ringa nuna mata a shekarar farko ta aurensu. A lokacin ya kan sakata taji tamkar tafi kowacce mace dacen miji duk kuwa da bata samu yanda take so ta bangaren kayan more rayuwa ba amma soyayya da tattalinta da ya ringayi yafi mata komai dan dama ita ai dan soyayya ta aure shi bawai kudi ba.
Chapter 12 · 0% Book details