← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 158

Sashe 85

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kaje ka kirawo su magriba tayi” na fada kafin na mayar da kaina kan abinda nake yi amma sam ban gane komai ba. Idan nace zancen zuwan Amirah be dake ni ba nayi qarya ta tabbata kenan dagaske saboda ita Bashir ya sake ni tunda ga ta nan ya kawo ta nan din.

“Allah kaine Allah, kayi mana sakayya akan duk wanda ya cutar damu” na fada a fili bayan na ajiye Tab din hannuna dan sam na dena gane abinda nakeyi. Tagumi na rafka, se kuma na janye nace da kaina “Tagumin fa be ganni ba, tun wuri gara na tattara shirgin Baban Ali a gefe na fuskanci abinda ze tun karo ni a gaba” ina fadar haka na miqe na shiga Bayi nayi wanka.

Ina cikin shafa mai Muhammad ya shigo da leda a hannunsa da ban san ko menene a ciki ba.

“Mami wai gashi inji Anty Amirah ta kawo miki tsaraba” ya fada yana ajiye ledar a kusa dani, har ya juya ze fita na janyo shi, se da na zare masa ido kafin nace

“Dauki ka fitar can bola kayar, idan na kuma ganin ka shiga gidan nan idan sena cire maka kunne, wuce kaje ka kirawo Ahmad daman kune masu shegen yawo ai bini bini kun tafi can”.

Haka na cigaba da shiryawa ina mita, seda na sake tara su gaba daya naja musu kunne akan babu su babu zuwa gidan Amirah, idan ma uban suke son gani se su jira ai yana fitowa su ganshi a waje su wuto gida amma ban yarda wani ya sake ya je gurinta ba.

Washe gari da yake Asabar ne bamu tashi da wuri ba se gurin goman safe dan haka kafin muci abinci muyi wanka an fara kiran sallar Azahar.

Aliyu ne ya sa su a gaba suka wuce masallaci da suka tashi dawowa shi kadai ya shigo ba tareda sauran ba.

“Aa Yaya ya naganka kai kadai ina qannen naka” na tambaye shi ina gyara Hijabin jikina dan zan leqa gidan Anty, bata jin dadi kwana biyu itama.

“Mun taho a hanya sukaga Abbi shine ya jasu gidansa” Aliyun ya fada yana zama akan kujera, se nayi qwafa nace “wato basuji abinda na gaya musu jiya ba ko nasan Jafar ne ze jasu za kuwa su dawo su same ni, Faridah taso ki rakani ke kuma Amna idan kin gama cin abincin in zaki zo toh” na fada ina nufar qofa.

Kallo daya nayiwa gidan Bashir shima bisa kuskure na shige gidan Anty, ban zauna ba ganin Baba yana gida dan a zatona yana gidan uwargidansa ne yau dan haka a tsatstsaye nayi mata sannu yana ta in zauna mana nace Aa anjima na dawo muka fito, ina sako qafata waje nayi kyakyawan gani da Bashir tareda matarsa saboda tsabar sabon salon munafunci ta dauki Ahmad se rinjayarya yake kamar zasu fadi suka shiga mota, inajin Ahmad din yana cewa

“Mami, Abbi ga Mami nan ba tareda ita zamu je ba” ko iskar su ban waiwaya na kalla ba na shige gida. Ban kai ga cire Hijabi na ba naji an turo qofar an shigo ga kuma qarar takalmi qwas qwas alamar dai macace se na waiwaya naga waye ido na ya sauka akan Amirah.

Fuskarta dauke da Fara’a ta qaraso cikin palour nidai ina tsaye har ta samu kujera ta zaune tana waige waige. A lokacin Allah kadai yasan abinda nake ji a cikin zuciyata amma na rigada nayiwa kaina fada, badai ni na sake yin wani tashin hankali akan Bashir ba tunda dai yanzu babu abinda muka hada dashi dan haka nima sena fasa cire Hijabin na zaune a kujerar da take kallonta fuskata a hade ba tareda nayi magana ba.

“Ina wuni Anty” ta fada tana wata dariya kamar kwarkwar, seda sake tsuke fuksa kafin na amsa da “Lafiya” a taqaice.

“Tun jiya naso na shigo wallahi na gaishe ki kuma se gajiyar hanya ta hanani ga gidan nazo na tarar dashi duk ba a kintse ba shine fa nayi yan gyare gyare har yau da safe, yanzu ma fita zamuyi wai twins ne suke son Ice cream zamu je a siyo Ina Farida da Amna ban gansu ba su” Amirah ta sake fada tana bin lungu da saqon palour da kallo duk ina ankare da ita, zanyi magana Farida ta fito daga dakinsu, kallo daya kuwa tayi mata ta zumburi baki ta juya ciki ma ta fasa fitowar ita kuwa Amirah se wani murmushi takeyi na ala dole ita ta iya bariki.

Jin bata sake cewa komai ba yasa nace mata
“Zaki iya tafiya tunda mun gaisa ko, amma mu nan bamu saba da shige shigen maqota ba. Kowacce mace a gidanta take zama dan haka karki sake shigowa mana mun gode” nayi maganar raina a sake kai ba kace mun hada wani abu nida ita ba.

Na sani gulma da munafunci ne ya shigo da ita dan ta nuna mun tazo, sannan taga yaya na zama tunda Autan Maza ya sake ni ko? To gani dai garas a cikin hayyacina, sema fari da kyau danayi saboda ni idan na rame ido na da hanci qara fitowa sukeyi ga kuma hutun dana samu kusan kwana nawa ina zaune a cikin Ac sannan da wani hadin ridi da Madara da Anty takeyi mun duk yamushewar da nayi a kwanaki biyun nan na warware fatata ta nuna jin dadi.

“Uhm toh shikenan bari naje nasan Yaya yana ta jira, se mun dawo” ta fada tana miqewa, har ta kusa fita ta waiwayo tace
“Anty gurin nan yayi kyau har yafi can gidan ma wallahi”.

“Allah ko, se ki gayawa Bashir ya zuba miki irin kayan idan kuma nan din kike so se mu baki” na fada ba tareda na daga kai na kalleta ba, itama bata ja maganar ba ta fice tareda ja mana qofa.

Naga qoqarin ya kwarai da tsantsar rashin kunya da har ta iya dakko qafa ta shigo mun gida ko kuwa tana nufin tace mun bata san bana tareda Bashir bane, koma dai yaya yau daya dai na danne zuciyata duk irin abinda ta ringa ayyano mun da nayi mata na daure amma tabbas duk randa ta sake gigin shigowa ban san abinda zanyi mata ba, su kuma dan uban su zasu dawo su tarar dani se sun gaya mun me suka rasa a gurina da suka tafi yawon roqo gurin Bashir.

AMIRAH
Ganin da tayiwa Asma’u lokacin data fito daga gidan Anty sam be gamsheta ba. Bata zata cewa a dan tsakanin abinda be ko kai sati daya ba Ma’un zata iya dangana da abinda ya sameta har ta ganta tana yawo akan qafafun ta kamar babu abinda ya faru.
Mantuwa Bashir yace yayi ya koma cikin gida, yana shiga itama tayi saurin fita daga motar tabi bayan Ma’u.

Ba qaramin girgiza tayi da ganin tsaruwar sabon gidan Ma’un ba tunda dai tasan babu silan Bashir a ciki wato ita wata sabuwar duniya ma ta bude ta qawata gida kamar ba wadda aka saka ba tana walwalarta, ta kuma yi zaton ganinta ze batawa Ma’u rai har tayi fada ko wani abu daga nan ta samu damar da zata sake qunsa mata takaici dan sosai su Addah da Sa’adah sukayi mata hudubobin tsiya tunda suka ji Ma’u tana kusa da gidan.

Sun karanta mata yanda duk zatayi ta uzzura mata ta yanda ita da kanta zata bar kusada Bashir idan taga bazata iya daukar abubuwan da Amiran take yi mata ba amma se gashi ko a kwalar rigarta bata ga alamar ganin ta ya daga mata hankali ba, kai ita se take ganin kamar ma qarya ne babu wani sakin ta da yayi dan daga ita har shi din bata tsammaci ganinsu a hayyacin su ba har gara Bashir ya rame amma Ma’u fa kyau ma taga ta qara abunta.

Haka ta ringa cizon yatsa a mota ga Bala’in da yakeyi mata akan wane dalili ta shiga gidan, ta qudurce a ranta tabbas seta gallabi Ma’u ta bar unguwar nan dan bazata juri haduwarsu da Bashir kullum ba sannan ga wadannan mayun yaran da tun zuwan ta jiya suke zurubtu a gidan, gara suyi can nesa dan in ba haka ba ze zamana an kashe miji ne ba’a sare kansa ba.

Fitar da tayi niyyar warwasawa yau itama gata a gaban motar Bashir a Lagos sun fita shan Ice cream qarshe haka suka dawo kowa yana hada rai yaran ne kadai suke ta jin dadinsu shi kuma ya biye musu har wadanda ba’aje dasu ba seda akayiwo wa tsaraba.

Da suka dawo gidan ma kayan sa yace ta shiga ta gyara masa sukuma suka baje a palour da yaransa suna ciye ciye da buga game baqin ciki kamar ta fashe daga zuwa rana daya za’a fara haka lallai dole a sake sabon lale.

Wayar ta ta dauka ta shiga kiran Sa’adah tunda itace malamar tata, bugu biyu ta daga tana tsokanarta da cewa

“Uwargida Amaryar Engineer, ashe kin kunna waya ai bari nayi ku gurji Amarci kwana biyu tunda an dade ba’a hadu ba daga baya se musha labari”

“Wayake ta zancen wani Amarci yanzu Anty Sa’adah” Amirah ta fada tana jan tsaki, daga dayan bangaren Sa’adah tace

“Bangane me kike nufi ba, kardai ki cemun period din dawowa yayi bana ce miki kisha pills ba ze dauke ko baki sha ba”.

“Duk fa ba wannan bane yanzu, ni kin ganni tunda nazo jiya ma nake aiki kamar jaka. Gida kaca kaca ga gyaran dakina tsabar wulaqanci masu saka gadon a ciki suka bar kwalaye da sauran tarkace, haka ya tasani a daren sena gyara, dan ma na taho da Miya kin gani sefa da na dafa mana taliya mukaci, ga shegun Yayansa sunzo sun tasa mutane a gaba saboda haushi ma nayi bacci na barsu ban san lokacin da suka tafi ba.
Chapter 85 · 0% Book details