← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 158

Sashe 18

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Dan Allah tambaya nakeyi me shagon nan”
“To hajia ai gani”
“Aa ba kai ba Malam nake nufi” ta bashi amsa.
“Malam kuma Malam wa?”
Wata sabuwa inji yan caca ita ai se yanzu ta tuna da ko sunan sa bata sani ba, cikin ta ne ya bada qululu ta daure tareda korar abinda zuciyar ta take hasaso mata tace

“Malam dai wanda yake zama a shagon nan Mijin Maimuna me wannan gidan” ta fada bayan ta tuno da sunan matar malam din.

“Toh gaskiya hajia ban san wanda kike nema ba, hasalima nan shagona ne nafi shekaru goma ina saida kaya a ciki gida kuma da kike magana ba gida bane kangone da Almajiran waccen makarantar suke kwana zaki iya leqawa ki gani” me shago ya fada yana nuno mata makarantar daga nesa.

Addah bata qi ta tashi ba ta leqa gidan, kamar yanda ya fada kuwa incomplete ne ta cikin ga kayan Almajirai nan tsubi tsubi, wata hajijiyace ta kwasheta jin zancen da wani saurayi da yazo siyya shagon yakeyi

“Tab Malam Musa Allah dai yasa ba itama tafada komar Wizy bane dan a satin nan mata sunfi Goma da suka zo neman Malam” yana kaiwa nan ya karbi kayansa yayi gaba yana wa Addah dariya.

Allah sarki Addan mu Allah maida Asara 😂😂😂https://chat.whatsapp.com/DpZYwM6HCjs7WDTCBPkyj0

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 12

Lagos

Asma’u bata tsammaci dawowar Bashir a yau litinin ba ganin tun ranar Asabar din be ko sake bi ta kansu ba dan haka koda ta tashi aiki ta biya ta dakko yaranta suka wuto gida.

Bayan Sallar Isha suna baje a palour, Dan wake sukayi abinsu sunaci suna kallo sukaji tsayuwar mota. Basu kawo shi bane dan baya haura 6pm a waje tsananin hold up ne ze riqeshi zuwa Magriba yanzu kuwa har 8 ta gota shiyasa ma suka fidda ran dawowar sa a yau dukda dai tasan akwai aiki to qila excuse ya dauka.

Bude kofar da akayi ya saka su juyawa gaba daya , Bashir din ne hannunsa dauke da rigar coat din sa se waya a kunnensa. Da gudu yaran suka nufe shi suna murna, taso ta basar amma wata zuciyar tace “ki tura masa aniyar sa” se itama ta miqe tana gyara zaman hular kanta ta nufeshi.

Side Hug ya mata tareda pecking goshinta bayan yaran dukka sun ruga mota debo kayan daya bari dan sun saba in dai ze dawo se yayiwo musu tsara ba ita kuma ta karbi rigar hannunsa tayi gaba ya rakata da ido bayan ya zauna a daya daga cikin kujerun palour ya ci gaba da amsa wayarsa.

Ruwan wanka ta hada masa kafin ta fito masa da duk abinda ta san ze buqata. Sanda ta fito ya gama wayar yana tsakiyar yaran da suke zuba masa surutu se murmushi yakeyi Muhammad na kan cinyar sa yana cin Pizza.

“Oh bama za’a jira ni ba kenan ko” ta fada tana daga Muhammmad din kafin ta ci gaba da cewa
“Oya kowa ya kwashe nasa duk kunyi scattering palour,ga plates din nan ma ba’a kwashe ba”.

ledojin suka shiga tattarewa kowa ya dauke tasa suka shige kitchen su ajiye seta juya ta kalleshi shima ita yake kallo. Murmushi me kyau tayi masa tace “Yallabai ai mun zata se gobe, ga ruwan wanka can na hada maka”

“Jazakhillah” ya fada yana miqewa dan a gajiye yake sosai, tunda ya diro be huta ba aiki sosai yau yasha a office din ba. Sanda ya fito daga wanka tana zaune akan kujerar dake dakin sa. Ita ta taimaka masa ya shirya kafin ya tada Sallar isha ita kuma ta fita hado masa Tea da yace ta kawo masa.

A babban Mug ta hada ta saka masa madara da Ovaltine sosai banda sugar se Cake din da tayi musu na makaranta ta zuba masa a bowl ta hado akan dan Try ta fito. Sun gama ciye ciyen an tafi yin Brush se Jafar kadai dake tsaye yana jiranta.

“Ya akayi” ta tambayeshi
“Gurin Abbi zani na tambaye shi abu”
“Muje toh” ta fada tayi gaba yana binta a baya.

Suna shiga dakin ta ajiye masa ta shiga toilet yin fitsari shi kuma Jafar ya zauna, ba abinda yake son ya tambaye shi ta sani qulafucin uba ne da Jafar dan gani takeyi yafi son Bashir akanta. Indai yana gida tofa yana nane dashi in ko tafiya yayi ya ringa kiransa a wayarta kenan shi kuma haka yake.

A dakin ta barshi ta tafi nata tayi wanka, seda ta shirya sosai tabi dakunan yaran ta tabbatar sun kwanta har Jafar din ya dawo sannan ta kashe Fitilun palour ta tafi dakinsa.

Yana zaune da waya a hannunsa yana juyawa Asma’u ta shigo, tunani yake ya kira Amirah ko yaya tunda ita Allah besa tayi hankalin jin ya ya sauka ba yauma. Yanayin walwalar da ya gani a fuskar Asma’u yasa ya fasa sema ya kashe wayar gaba daya ya ajiye kafin ya miqe ya fita.

Seda ya leqa ko ina ya tabbatar da komai lafiya ya tofe ko wacce kusurwa da falaqi da nasi kafin ya koma Dakin har Ma’u ta kwanta taja bargo zuwa rabin jikinta. Kwanciya yayi shima yana jawota jikinsa, hannunsa ya tura cikin gashin kanta ya zame band din data daure shi dashi, Bashir nason Gashi sosai yana daga cikin abubuwan da suka sake jan sa akan Amirah yanda take kwalliya da gashi.

“Madam ya akayi ne da alama ko missing dina bakiyi ba tunda na tafi bako waya”.
Gajeran murmushi tayi tace

“Qalau fa kawai dai mun barka ne ka huta sosai ka kula da Amarya, ya ka baro su suna lafiya ko?”

“Lafiyar su qalau suna gaishe kuma”
“Muna amsawa” daganan taja bakinta tayi shiru, shima shirun yayi tana jin sa yana jagwalgwala gashinta kafin bacci ya dauketa. Da Asuba ta rigashi farkawa, harta dauro Alwala be tashi ba dan haka ta shafa fuskarsa da sauran lemar ruwan hannunta jin ana qoqarin tada sallah. Kafin kuwa yayi Alwala an shiga, dole se a palour suka hadu da yaran dukka ya jasu sallar.

Bayan sun idar ma bacci ya sake komawa tayi mamaki dan da wuya Bashir ya koma bacci da Asuba kai ko ba zashi aiki ba ze zauna yayi ta lazumi har se rana ta daga yayi walaha sannan yake komawa bacci. Tana wanka tana gulmarsa a ranta wato yaje ya gama kashe Arnansa ze zo yana baccin gajiya a nan ko.

Tsaf suka shirya, tana jira taji shi ze tafi dasu ko kuwa ita zata ci gaba da jigilar har suka fita yaran suka shige motarsa taga ya kunna beyi magana ba , Hamdala tayi a zuciyarta kafin ta kunna tata motar suka hau hanya seda suka je junction din da suka saba rabuwa tayi musu horn ta shige kwanar office dinsu.

Bayan tayi parking tana qoqarin Daukar jakarta da system Ilhama Abokiyar aikin ta ta qaraso gurin motar,
“Aa Maman Farida yau da wuri haka” Ilhama ta fada bayan sunyi musabaha.

“Wallahi fa Maman Khairi Allah ya ceto ni daga yawo kai yara makaranta” tare suka jera suna yar hira har suka isa 3rd floor inda anan office din Asma’u yake ita kuma Ilhama tana 4th floor ne.

Tana isa office dinta ta tarar da takaddun da zatayi aiki a kansu kamar koda yaushe. Seda ta kintsa komai sannan ta fara duba su daya bayan daya kafin wani lokaci ta gama har ta shiga replaying mails da suke jiranta.

Asma’u nada hazaqa sosai ta kuma qoqarin aiki gata Allah ya bata fasahar harshe, duk baqin abu Idan Asma’u ta tsara ka tace Fari ne bazaka san sanda zaka yarda ba dalilin da ya saka ta karantar Business Administration kenan dukda a farko taso ta karanci Law ne yanzu haka tana aiki ne da wanni babban company hadahaar ma’adanun qasa (Mineral resources) tana matsayin Sales Manager (manajan siye da siyarwa).

Yanda take qoqari gurin janyo musu customers yasa take samun cigaba da Alkahiri sosai a kan aikin nata ga damammaki da suke shigo mata saboda yanayin aikin yana bata damar hulda da manyan mutane sosai masu siya ko wadan da suke kawo hajar su company ta siya.

Tana tsaka da aiki Kiran Fainusa ya shigo mata
“Tauraruwa me wutsiya” ta fada a fili dan ita dai duk kiran wayar Fainusa ba Alkahiri bane a gurinta, seda ya katse ta sake kira sannan ta dan dakata ta daga.

Cikin sabuwar girmamawar da Fainusan takeyi mata tunda ta fara zaman gida suka gaisa Fainusan ta ke tambayarta yara tace suna makaranta itama ta tambaye ta ya Dada tace tana lafiya.

Shiru ne ya biyo baya tana jiran taji dame tazo yau kuma can kuwa ta nisa kafin tace

“Anty jiya har dare mutuniyarki suna nan gidan da yaya”

“Uhm” kawai ta amsa mata, ita tarasa wannan abu kamar wadda take biya ta kawo mata rahoto kuma duk sanda ta tashi kawowar ba masu dadi bane.

Fainusa kuwa bata damu ba taci gaba da cewa “wai fa in gaya miki ta samu Dada wai tayiwa Yaya Magana ya tafi da ita Lagos, to wai ke take so ki dawo nan ko kuma hadaku dukka ze yi anan?”

Shiru Asma’u tayi tana so tayi tana sauraronta, jin tayi shiru alamar ta gama kenan yasa tace mata
“Toh Nagode ina office ne ki gaida su Dada” taa kashe wayar.

Duk yanda taso ta ci gaba da aikin seta kasa, ita sam ta manta da maganar da yai mata ta komawa Gombe se yanzu wato Amiran ce take Son dawowa nan kenan shine ita za’a tarkatata ta koma gida tunda tasan bazasu barshi ya debo su su dukka biyun ba dole ya bar daya acan Gombe. Lallai ma tayi yaya da aikinta toh? Bama wannan ba makarantar yaranta fa ko kuma yanzu Amiran ta shirya zama tayi mata rainon Yayan kamar yanda suka ce a lokacin da ya nemi su ringa karba karba
Chapter 18 · 0% Book details