← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 158

Sashe 37

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A qofar gida ya tarar da Bala da yan majalisar sa kamar yanda yayi tunani, kashe motar yayi tareda jan kujerar baya sosai ya tokare qafarsa da stiyarin motar , zafafan numfashi yake saukewa a jere a jere zuciyarsa jinta yake tamkar ana soyata a mangyada.

Me yasa meye dalili daya kasa samun nutsuwa tunda ya auri yarinyar nan? A shekara biyu an tafi ta uku da qara auransa be sakeyin sati daya na cikakken farinciki ba wai dama haka qarin auran yake ko kuma shine beyi dace ba.

“Me yasa baka nemi wata ba me yasa se Amirah zaka aura Bashir? Yau da ace wata daban ka aura wallahi ko mata uku ka auro lokaci daya bazan damu kamar wannan auran da kayi ba amma shikenan haquri ko nayi haquri. Idan dan Allah kayi Bashir Allah ya bamu zaman lafiya ya bani ikon cinye jarabawar da yayi mun, idan kuma kayi ne dan kaci mutuncina to Allah baze bari na tozarta ba ba kuma zaka samu nutsuwar da kake iqirarin samu ba” kalaman Ma’u na qarshe wanda daga su bata sake tayar masa da hankali ko wata magana ba sanda ya auri Amirah.

To wai alhakin nasa ne ko nawa shidai Allah ya sani beyi auran nan da wata manufa ba yayi ne kawai dan yana ra’ayi bakuma dan ya tozarta Matarsa ba kamar yanda take tunani amma gashi nan shi yake karbar sakamakon sa da Hannun hagu wai ta ina toh ya kuskure?”

Glass din window da aka kwankwasa ya dawo dashi daga tunanin daya tafi, se ya dago yana gyara zamansa. Seda ya saita yanayinsa sannan ya bude qofar ya ziro dogayen qafafunsa yana sake kokawa da dacin ransa kafin ya fito gaba daya.

“Kaga Na Ma’u Angon Amirah uban Aliyu ko dubu ta taru” Bala daya gaji da jiran fitowar Bashir din ya zo ya kwankwasa masa glass ya fada cikin sigar tsokana sedai yana yin fuskar Bashir din tasa ya gintse maganar tasa.

“Lafiya kuwa Engineer kaga idanunka” Balan ya sake fada, se Bashir yaja tsakin da ya aure shi ya bude murfin motar ya koma ciki yana cewa Balan ya zagayo. Cikin zaquwa Bala ya shiga motar dason jin meya faru, dan Bala irin mutanen nan ne masu son bin kwakwkwafin duk wanda suke tare se sun san komai nasa.

Shiru sukayi na kusan minti biyar, Bala da gulma take cinsa har ya gaji ya ceda Bashir din “Engineer wai yane kodai akan climax kake ne kaima ka fara busa eh yane”

Wani mugun kallo Bashir ya jefe shi dashi kafin dakyar ya bude baki yace “Abinda banyi da quruciyata ba shi kake mun fatan yi yanzu insha Allahu har na mutu nida hayaqi sedai na murhu balle na kai ga shan wata kwaya kai dai da ka riga ka illata rayuwarka shikenan amma ka ringa tunawa Yaranka Mata ne kodan su ya kamata ka dena abinda kake yi”.

Hade rai Bala yayi dan yasan dama qarshe seya jefe shi da maganar, tun suna secondary Bala ya fara bin wasu Sa’anninasu a unguwa har suka koya masa dabi’ar shaye shaye, babu yanda basuyi dashi ba akan ya dena amma ina qarshe har yaso koyawa Sadiq da taimakon Allah da jajircewar Iyaye beyi nisa ba ya bari amma shi Bala ya rigada yayi nisa dukda abun nasa harda daurin gindi daya samu gurin Babarsa dan shi kadai ne danta Namiji.

Lokacin da aka ringa ankarar da ita akan ta ringa masa fada seta nuna an takura mata Da ba’a qaunar sa seda yayi nisan da baze ji kira ba sannan tazo tana kuka da idanunta akan dabi’ar tasa dan seda takai kayan maye har a cikin gida sha yake babu abinda baya ta’ammali dashi in banda Giya da Cocaine har kuwa ta mutu da wannan baqin cikin toh yanzu dai yayi sauqi saboda girma da iyali daya tara amma fa ko yanzu ba abin kunya bane a gurinsa ya murza wiwi yasha ko a gaban waye su kansu su Bashir dan dai babu yanda suka iyane suka ci gaba da zumunchi dashi musamman Bashir da Yake ganin Balan na bashi shawarwari daidai da ra’ayinsa.

Shiru suka sakeyi kafin can Bashir ya mula dan yana buqatar abokin tattaunawa, idan so samune Sadiq ya kamata ya gayawa dan yafi Bala hankali amma tun auransa da Amirah alaqarsu taja baya dan a lokacin gani yake Sadiq din ya goyi bayan qanwarsa dan haka ya zage ya masa rashin kyautawa shi kuma da zuciya ya fita sabgarsa sam yanzu babu wata kwakwkwarar mu’amala tsakanin su daman ga banbancin gari yanzu ga aiki yasha kan kowa.

Labarin duk abinda ya faru da hukuncin daya dauka da wanda Baba ya dauka shima ya bawa Balan, Bala dayai zuku di kamar gaske yana sauraronsa ya jinjiga kai yana cewa “kai Engineer kafa debo da zafi wallahi, nifa daman wannan Addan taku kasan yar bala’i ce tun duniya na kwance bazan manta sanda muke zuwa gidanta ba lokacin tana kiwon kajin nan in muka kwamusu daya haka zata biyo mu har layi tana sababi, amma ai ita Amiran tayi fa. Ka jure kawai tunda ka samu yarinya me kyau duk abinda ze zo ai daga baya ne”.

Baki bude Bashir yake kallonsa, wai ma wannan ya gane kan matsalar sa kuwa yake masa wannan soki burutsun koda yake shima da laifin sa wani sa’ilin ina shi ina shawara da dan wiwi? Tsaki ya buga kawai tareda yaiwa motar key yace masa “Malam sauka seda safe”

Bala ya kwashe da dariya yana cewa “ah da wuri haka kodayake gara kaje ka lallashi yar Babynka wallahi baka san wahala suke yanzu ba ko kodan kai Allah ya baka zuqa zuqa har biyu ka ajiye a gida baka san yanda kan gayu yake gwaruwa yanzu kafin su samu wadannan kalolin ba”

“Bala sauka ko na tafi da kai” ya sake fada a fusace, se Bala ya balle murfin motar ya fita yana ci gaba da yi masa dariyar qeta yace “Haba Engineer ai daman ba’a samun abu biyu ka hada kyau da zaman lafiya ai baze yuwu ba mu dai da muka auri munanan ba gashi muna qalau ba wayake jin kanmu...” fizgar motar Bashir yayi Allah yasashi ya matsa gefe ya koma majalisarsu yana ci gaba da dariya a ransa yana cewa “Ai baka ga komai ba wallahi, yanda ban samu abinda nake so ba kai ka samu, a baya dai kaji dadi amma bazaka sake samun kwanciyar hankali ba”.

Bayan Barin Bashir gurin yawo ya ci gaba dayi a mota dan baya so ya koma gida ko waccensu haushinta yake ji, seda sha biyu ta buga sannan ya kama hanyar gida bada ban ba ma Hotel zeje ya kama amma yanda duniyar nan take yanzu abu qalilan seya jefaka a masifa wani ya ganshi be san meya kaishi ba a canza masa manufa, gidan ya dawo masu gadin layinsu na zazzaune suna hira mutum biyu suka taso suka bude masa get bayan ya aje motar ya koma yayi musu dan ihi sani ya koma ciki.

A tsakiyar part biyun ya tsaya ya riqe qugu yana balla musu harara kamar masu dakin ne a gabansa, fitilun palour Amirah a kunne suke, daga inda yake yana hango cikin palour tarwai ta window saboda babu labule kamar ya share sedai tunawa da Maganar chanza key da Asma’u tayi masa ya saka shi dosar gurin dan be san ko an sace din ba da gaske.

Da key din hannunsa yayi amfani ya bude qofar tana kwance akan kujera ta duqubqune ya isa kanta ya tsaya ya, ganin yanda ta bar kwanuka ya sa ya fara kiran sunanta. Amirah kuwa Kamar a mafarki taji muryar Bashir yana kiranta, tana bude ido kuwa ta ganshi akanta ai ba shiri ta buga wani uban tsalle tayi gefe sedai kafin ta kai qasa yai azamar riqota dan shi kansa ya tsorata da yanda ta miqe din ba shiru suka zube qasa, a tare suka saki qara shi ta zafin buguwar rashin tsammani data same shi ita kuma ta azabar da taji cikinta ya dauka danji tayi kamar dinkin ze bare.

Kuka riris ta saka gana tsoron abinda ze mata gana azaba abinda ya hadu ya qara qular da Bashir qoqari yake ta tsaya tabar mutsu mutsun amma ita se qara zillewa take tana ihun yayi haquri a zatonta dukanta zeyi, ganin tana bata masa lokaci yasa ya daka mata wata uwar tsawa yana ce wa “wallahi ko ki rufe mun baki kona make ki a gurin ki tsaya mu gani ko kinjiwa kanki ciwo”.

Tsit tayi se shatato kwalla take hannu ta akan cikinta dayan kuma ta rufe baki, yanda take matsa cikin ya tabbatar masa da tana jin zafi ya saka shi cewa ta tashi ta biyo shi yayi gaba tana binsa a baya a dudduqe, seda ya kashe fitilun ya kulle qofa kafin suka shiga motarsa, wallahi badan yana tsoron kar wani abun ya sameta Allah ya kamashi ba da barinta zeyi jikinta ya gaya mata. Haka ya sake fita daya saura suka nufi Asibiti shi yana jera tsaki ita tana kuka qasa qasa.

Basu bata lokaci ba dan an tabbatar musu babu komai motsawa gurin yayi amma dai ta kiyaye irin hakan, Allurar kashe zugi suka mata kafin suka kamo hanya kamar abokanan gaba har suka zo gida yana tsayawa ta wuce sedai tuna bata da key ya sakata rakubewa tana satar kallonsa. Har ze shige part din Asma’u shima ya tuna da bata dakko key dinba dan haka ya qarasa ya bude mata qofar be amsa Nagode din da take ce masa ba ya wuce abinsa.

Kitchen ya fara tsaya wa ya dauki Yoghurt me sanyi kafin ya hau saman, beyi zaton samun Ma’u a dakin ba amma yana budewa qamshin Airfreshner dana turarukan baccinta suka masa sallama besan sanda ya fara sauke aji yar zuciya ba dan har ga Allah qanshin sun san yaya masa rai.
Chapter 37 · 0% Book details