← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 158

Sashe 86

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To kin ganni yanzu ma dai na taqaita miki tun safe aikin nake, harfa fita mukayi wai ze siyowa Yaran Abu gasu can mun dawo suna palour ni kuma ya saka ni ninkin kaya” ta qarasa maganar cikin tsantsar takaici, badan hudubar da aka mata akan ta kwantar da kai ba da wallahi tun a yau gayyayar zata watse dan ita fa ba aikatau tazo yi ba, zuwa tayi ta mori miji taji dadi a toh.

Dariya Sa’adah ta ringa sheqa mata abinda ya sake qular da Amirah kenan tace

“Wannan ai wulaqanci ne, na gaya miki matsalata kuma kin mayar dani abin dariya shikenan, bari na kashe wayata, barima kiga na gaya masa nifa bazan yi ba dan na gaji wallahi sekace jaka”.

Seda Sa’adah ta tsagaita da dariyar kafin tace “toh ai Amirah dole nayi dariya, nifa bari kiji wallahi na dade banga sakaryar mace irin ki ba amma fa kiyi haquri.

Ce miki akayi a banza kake mallake mijin daman ai se kin zama jakar, a gabansa ki zama kamar baiwa se yanda yayi dake ko takaki yayi kar kice komai shine zaku zauna shiru bame jin kanku ki zama ta gaban goshi yanda ko wani ne ya kawo aibun ki ze tare miki kuma ki more shi yanda kike so tunda yana juya ki shima, ko bakiga ni har wanki nakeyiwa Yallabai ba, idan kuwa ina gabansa biyayya ko ubana Albarka”

“Tab wallahi bazata sabuba kuwa dan ni bazan iya ba. Haka kawai sena zauna kenan na zuba ido se yanda akayi dani ai kuwa bazan iya ba ni indai wannan shine dabarar gara ma nabi ta Addahn kenan a nemi inda za’a kaishi a mallake mun shi ta qarfi amma indai se na zamar masa jaka babu ni a wannan tsarin” Amirah ta fada.

“Ai kuwa indai kina so ki samu yanda kike so a gurin namiji yanzu dayan biyu ne, kodai ki zama kurma makauniya ki sakar masa ragama duk abinda yayi daidai ne bazaki musa masa ba ko kuma ace ke kike wahalta masa da aljihunki to shine zaku zauna lafiya ba tareda an ji kanku ba.

Dan muddin kika ce in ya bada umarni zaki kawo taki shawarar to kuwa kun ringa samun sabani kenan. A cikin Maza yanzu kadan ne suka fita zakka da zaki ga sun bawa matansu haqqin da ya kamace su,

Idan kuma yawon Malaman kikaga yafi miki seki daura aniya, ki dai sani wata rana zanin da zaki daura ma se ya gagare ki tunda kullum kina kan hanyar kaiwa wasu daga zaune kudin ki kuma shi Asiri ko kinyi se kin hada da kissa wallahi randa kuma ya karye se kin fi kare wulaqanta”.

Shiru Amirah tayi dan gaskiya Sa’adah ta fada, yanzu dai gashi tun yaushe suke yawon rabar da kudin daga can inuwar su tsugunna a waccen amma babu biyan buqata, gashi yanzu cikin lumana komai yana tafiya yanda take so to amma kuma ita ai bata zaci haka zaman ze kasance ba.

Cikin sanyin murya tace “Toh yanzu Anty Sa’adah ya zanyi dan gaskiya akwai matsala”

“Yawwa yanzu kika dawo kan hanya” Sa’adah ta fada kafin ta ci gaba da cewa

“Kina ji ko, batun gyaran gida wannan daman ai aiki ne dukda ban san Kishiyar ki ba amma a yanda kuka bani labarinta mace ce data san kanta dan haka yanzu dole ki dage idan baki zarta ta ba toh kuyi kan kan kan.

Tsafta dole ki dage gyaran gida ko ina yayi qal ki saka turare Allah na tuba ma wane aiki ne a gyaran gidan keda ba wani wawakeken Mansion ne dake ba dan Duplex ne fa, sharar palour, Kitchen da mopping dinsu dai wannan dole kullum kiyi.

Haka dakinsa, da kun tashi bacci ki gyara gado, yana shiryawa ya fita ki share ki wanko bandaki kija qofar shikenan fa se kuma gobe. Naki dakin zaki iya ki ringa tsallaken kwanaki tunda ke kadai ce babu me shigar kiki, kwanuka idan kina girki daga kin bata ki wanke idan anci abinci ma ana gamawa ki wanke, dan girki dai cin mutum biyu da safe ne fa se na dare ba shikenan ba duk meye abin wahala a ciki dan Allah.

Sannan ki ringa wanka dan Allah sau biyu dai a rana meye a ciki kayan kwalliyar nan gasu nan kina dasu kar kije ki ringa zama yanda kike a nan kamar wata me takaba da zani da T shirt dan dole ki dauke masa hankali daga kan kowacce mace ta yanda ze manta da tsohuwar matar sa ya shafeta daga lissafinsa tunda yana da ke sabon jini”.

“Toh ai Anty Sa’adah katangar mu daya fa da gidan data koma ga yaran tun jiya na gaya miki suke zuruftu a gidan nan ko tunawa dani ma bayayi” Amirah ta sake fada, se Sa’adah ta danyi murmushi tace

“Dadina dake komai se an koya miki, yo Allah na tuba ko a cikin gidan ku take idan kinsan yanda zaki riqe shi tsaf ai wallahi bata ishe shi kallo ba, yara kuma da dabara zaki janye su, daman karki basu qofar da zasu ringa shigo miki idan baya nan.

In kuma yana gidan sukazo kar kiji kunya ko a gabansu ne kije jikinsa ko kiyita yin abinda zaki ja hankalin sa dakansa ze ce su tashi su tafi, yana dawowa gida ki saka abinki a daki yanda baze ma samu kansa ba bare ya gayyato miki su a hankali se kiga shi dasu se in ya fita sun hadu ne ma ze ringa tunawa da zaman su, ke dai kiyi komai yanda ya kamata zaki sha mamaki wallahi”.

Haka ta ringa yi mata huduna data tsiya data kirki sukayi sallama. Da yake dai quiya a jininta take kayan dai gasu nan haka ta shirya masa dan ma ya sake kaiwa an goge dan haka zuba su kawai tayi. Tana cikin jera masa Suits ya shigo dakin,

“Har kin gama kenan” ya fada yana kallon ta hannun ta wadda kuma ita ce ta qarshe da zata rataye. Seda tayi fari da ido ta lankwashe murya kafin tace

“Na gama fa, duk na gaji wallahi hannuna ya qage kayanka yawa Yaya kamar na mace”.

“Koh?” Ya fada yana wuceta ya bude bangaren da ake zuba masa manyan kaya, Amirah kuwa kumbura baki tayi, a ranta tace

“Ba sannu ba komai ze ce mun wani Ayya, Aa Ayyo mutum dai besan gwaninta ba.” Baya ida tunanin ba taji shi cikin fada fada yana cewa

“Meye wannan kikayi? Haka ake jera kaya daman ji yanda kika loda su se kace wani motar kasuwa, malama sauke su tas ki gyara komai da kika gani irinsa daban zaki jera.
Shaddoji daban kuma kalolin su zaki duba kiyi su a jere sannan dayaj side din ki saka yadi ka, nan gurin Neck tie ake ajiyewa kin wani cusa mun hula baga inda suke can ba

Mtsw komai ke baki iya ba se kinyi wa mutane shirme, kina tsaye ki fara sauke su yanzu ki gyara” ya qarasa da daka mata tsawa.

Amirah da tayi mutuwar tsaye, yanzu duk wannan uban aikin data sha ze ce basuyi ba seta sake aikuwa bazata iya ba, haka kawai me ya hana shi yayi da kansa tunda ba haka akeyi ba, tsawar daya daka mata ya saka ta fara sauko da kayan ba shiri, haka tana ji tana gani da hawayenta da komai seda ta mayar dasu tsaf yana tsaye akanta sannan ya saka ta share dakin ta goge qal ta kuma wanke toilet kafin ya rabu da ita. Tana gamawa kuwa ta wuce tsohon dakin Ma’u inda ya saka mata sabon Gado ta ringa rusa kuka.

Indai kuwa haka zaman Lagos din yake kuwa wallahi bazata iya ba sedai ya maida ita can Gombe ya zauna shi kadai, ta zata da ta ke kukan ma ze bata haquri amma se gani tayi yaja Laptop ya kunna ma ya shiga aikinsa haka data gama ba godi bare na gode ta wuce tana kuka be tankata ba qarshe ma se jin tashin motar sa tayi alamar fita ma yayi.

ASMA’U

Se bayan La’asar yaran suka shigo da ledoji niqi niqi na kayan da suka siyo. Kallo daya nayi musu gaba daya suka shiga nutsuwarsu, karadin da suka fara na bawa su Faridah labari kowa ya kama kansa.

“Wallahi Jafar na sake ganin qafarka ka jasu kunje gidan can sena saba maka, idan banda shegen kwadayi me zakuci da bamu dashi a nan, ina shekaran jiya da kuka Raka Yaya Airport seda ya fara kaiku kuka siyi kayan kwalamar duk ba gasu can kun cika mun Fridge da tarkace ba ko kuwa wani sabo kuke so da ni baza ku gayamun ba wa ma kuka tambaya da kuka dibi qafa kuka tafi har wani guri” Na fada ina tsare su da ido, duk sukayi shiru Yan Biyu har sun fara yar kwalla ganin ina musu fada kuma na daure fuska, Jafar ne ya marairaice yace

“Mami kiyi haquri dan Allah bazamu sake ba, na zata ai tunda Abbi ne bazakiyi fada ba kuma shi yace muje bamu muka roqe shi ba ko Abdallah?” Se Abdallan ya yi saurin daga kai yana cewa

“Seda ma mukace mu baza muje ba Anty Amirah tace se munje Allah kuwa ki ma tambayi Abbin kiji”

“Naji, karku sake” na fada har sannan fuskata a hade. Ni ba fitarsu da Bashir ce ta bata mun rai ba akan me Amirah zata fitar mun da yara shine haushi na.

Waiwaya wa nayi na gansu har sannan a tsaye nace “me kukeyi kuka kun tsaya mun aka, kuje ku ajiye mana idan kuma ci zakuyi to se ku zauna”.

“Toh Mami ai baki ce kin haqura ba tukunna” Jafar ya sake fada, se nace masa

“Na haqura mana Jafar, ku wuce ciki”
“To Mami ai baki saki fuskar ki ba, kuma gashi har wannan Shawarman da kike so na siyo miki, naje na dumama miki a microwave?” Ya sake fada yana marairaice fuska, nasan nacin Jafar yanzu idan ban saki fuskar ba se ya kai dare anan yana mun magiya dan haka nayi murmushi nace
Chapter 86 · 0% Book details