← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 158

Sashe 9

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amirah ma jiki a sanyaye taja jug ta fara bankawa cikinta ruwan magani dukda qasan ranta bata jin Bashir zezo wannan satin amma dai gara tasha saboda tsaro se sannan ta tuna bata gayawa Adda yanda a ka qare da Indo me kaya ba, ta cicciba zuwa dakin Addan ta tarar tana sallah se itama ta wuce nasu dakin dan yin Sallar.

WASHE GARI
Qarfe bakwai a qofar gidan tayiwa Indo ta shiga biga gate baji ba gani dan ta rantse wallahi yau ko ita ko Fatu a garin nan ita zata rainawa hankali lallai bata san wacece Indo ba. Alhaji Murtala da fitowarsa kenan ze tafi wata Jana’iza ya qarasa ya cire sakata ta hankado qofar saura qiris ta bige shi tayi ciki abunta se kawai ya girgiza kai tareda juyawa ya kunna motarsa, Aminu daya daga yaran gidan ya qarasa bude masa gate yai ficewarsa dan bama ze tsaya yaga yanda zata kaya ba.

Adda Fatu da tunda tajiyo bugun ta janyo abinda Malam Wizy ya bata ta bantara se taga kaman Namijin Goro amma kai bashi bane qila kama ce ita dai ta afa baki ta hau tauna harda guara zama akan kujera tana jiran shigowar Indo se kuwa gata kaman an jefota ta fado.

“Fatu bani kudina kafin na yaga miki rigar rashin mutunchi a unguwar nan” ta fada tana huci, se Adda ta miqe tana qara bantarar magani ta tauni ta nufo Indo tana cewa
“Ke Indo fita ki tafi karki sake dawo wa gidan nan ki manta da zancen bashi a tsakanin mu har abada idan ma da wasu kudin a jakarki yanzu cirosu ki bani”

“Fatu hauka ne ya sameki ko to bari kuwa yanzu zan sauke miki shi wallahi ina batun ki bani kudina kina min wata maganar banza harda in qara miki wasu to bari kiga” Indo ta fada tana ja baya ganin Adda ta nufo ta tana sake maimaita kalamanta se zare ido takeyi ai bata yi aune ba se Ji tayi Indo ta dauke ta da wani gigitaccen mari daya sakata furzo da goron ba shiri ta kife gurin tana kururuwa dan ji tayi kunnenta, indo bata haqura ba ta sake kai mata Mahangurba a hanci aikuwa take ya fashe ya fara bulbulo da jini sannan ta bita ta turmushe ta hau duka, Adda ba hakin kwace wa se ihu take tana neman dauki.

Kishiyoyinta uku duk suna tsaye a bakin kofa da yayan su mata ransu qal akan wannan abu se Ummi da Amira a gefe suna taya ta ihun ba damar kai mata dauki 😂. Se da tayi mata lilis sannan Samarin gidan suka kawo taimako dakyar aka kwaceta Indo na jaddada mata wallahi ko kudinta ko kuwa kullum seta zo ta nada mata na jaki dan ta bar maganar police ma da kanta zata kwaci kudinta sannan ta fice daga gidan.

Adda fuska tayi luhu luhu se hawaye da ajiyar rai take ga hanci ya fashe a ranta Allah ya isa take jerawa Malam Wizy akan wannan abu daya bata gashi nan ba biyan buqata se bugu data sha a banza, bari Suga na Bashir idan taga ba nasara dole ta koma ya biyata kudinta dan bazata dauki asara biyu ba. Ita se yanzu ma taji wani tsautsayi ya kaisu yarda da Dan Napep din nan? Anya ma ba hadin baki bane shida Hajia Balaraba suka kaita a cinye mata kudi amma ai itama Balarabar ta bayar. Bari tayi ta kanta yanzu zata kirata taji yanda akayi. Ummi ce ta kamata ta kaita daki ta hada mata ruwan Me zafi a toilet ta shiga dan gasa jikinta, dakyar ta iya watsawa ta samu dai Habon ya tsaya ta dauro towel ta fito ta haye gado kan kace meye wannan zazzabi ya rafke ta se rawar sanyi take.
(To Adda Allah ya qara lafiya ya kiyaye na gaba 😂😂😂😂).

Kafin yamma dai jiki ya qi dadi dole suka kaita asibiti tasha Allurai suka dawo da magunguna gashi har sannan babu Bashir babu labarin sa kuma ta kira Dada ma wayarta a kashe, kukan baqin ciki ta fashe dashi da tsoron haduwarsu da Indo gobe.

Mu koma Lagos

Qiri qiri Asma’u ta qi bari a sallameta acewarta se tayi sati, Dr beqi ba tunda sabga ce ta kudi qaruwar su ce dan haka yace wa Bashir dole ta zauna suyi monitoring Bp nata na wani lokacin kafin a sallame ta. A kwana biyun nan idan kaga Bashir se ya baka tausayi yanda yayi wurjanjan dashi har a office an gane bashi da nutsuwa dole suka bashi leave na 1 week saboda ya samu ya kula da yaran kafin a sallami Asma’u, sauqin sa daya yaran sun rage kokekoken tunda kullum yanzu da safe ze kai su da daddare ma su koma.

Shi ya ma manta da wata Amirah sam bare zancen zuwa Gombe yau ranar Sunday kaman yanda ya saba bayan ya kawo yaran, suna gurinta Abokinsa Abdurrahman da Matarsa suka zo dubata, su suka tafi da yaran gidan su akan da dare idan ya gama se yaje ya dauke su su tafi gida ya dan rage zirga zirga.

Suna zaune kamar kurame bame cewa komai, ita tana chatting a wayarta shi kuma ya tasa ta a gaba yana kallo ganin yanda ta sake wani mugun fresh tayi kyau alamar ta samu hutu ba abinda yake damunta shi kuwa banda uwar rama da baqi da yayi to ga Damuwa ga babu abinci me kyau daya saba kwasa dan yanzu suma yaran mata yassara kawai suke ci dama Mami ce take tsayawa ayi abinci me kyau to bata nan dan haka baya iya ci ko sun dafa in yunwa ta dameshi ne ma zeci Indomie yasa tea in ba haka ba Snacks da lemo ne rabin abincin nasa.

Dagowar da Asma’u tayi tana dan murmushi tareda tsare shi da ido tace “wannan week din bazakaje Gombe bane”
Se a sannan manAmirah ta fado masa ya tuna rabonda suyi waya tun ran Laraba be kiratan ba yasan kuma itama bazatayi gigin kiransa ba tunda ya mata warning. Numfashi yaja kafin yace “Wallahi na ma manta shaf kuma ko waya banyi nace bazan shigo ba gashi har yau Sunday, ya kamata kam na kirata”.

Kishi ne ya dan tsikareta ta wani fannin kuma tana yabawa Bashir dan ba laifi yana kaman ta Adalci wani Sa’ilin. A farko farko se sati biyu yake zuwarwa Amiran ze tafi Friday ya dawo Monday da safe to da aka samu qarin kudin jirgi dole ya chanza tsarin zuwa Qarshen wata, daga bayannan kuma bata san dalili ba wani Sa’in se ya jera sati uku hudu ma duk weekend se yaje duk kuwa da ayanzu kudin jirgin ma yafi da ita dai bata taba tambayarsa dalili ba haka nan ko tare sukaje Gombe ko kwana na wa zasuyi bata da Kwana a yanda suka tsarawa kansu shida Amaryar sa kuma da taimakon Adda to ita hakan be dame ta ba tunda daman idan taje ba zama take ba a lokacin take samun ziyartar yan uwa da sauran abubuwan da akayi bata nan.

Tana kallonsa ya zaro waya ya shiga kiran Amiran ringing biyu kuwa ta daga tana fashe masa da Kuka, kallon Ma’u data juya baya ta kwanta yayi ya tabbatar ta jiyo kukan Amiran se ya miqe ya nufi qofa yana ce mata “kukan kuma Na mene kinsan bana so”

Wani qululu ya tsayawa Asma’u, wato itace banza a wajensa da in zata mutu tana kuka baze ce ta bari ba kenan ashe ita ta zata so ne yasa yake barinta ta fitar da damuwarta ashe tsabar be damu bane kai Anya kuwa Bashir ya taba sonta a ransa??
Abubuwa da yawa da ada take daukar haka yaje se a yanzu take ganin banbance banbance ko kuma dama Haka Mazan suke ko wacce Mace da yanda halayyarsu taje a wajen ta? In kuwa haka ne Sun Amsa sunansu na Hawainiya.

AMIRAH
Sanda Bashir ya kirata suna zaune da Addah da har yau fuska bata daidaita ba ko jiya Indo ta dawo Allah ya taimaketa Alhaji na Nan, shi ya kashe rigimar cikin Kudinta da yake hannunsa yake juya musu da a qalla sun kai 2 Million yau ta kirbi dari gobe Hamsin a wayonta kudinsa take ci da yaga fa da gaske Fatu ba hankali ne da ita ba dole ya saka akayi rubutu kowacce cikin Matan da kudinta dake hannunsa ya kuma gaya musu duk wadda ta nemi kudi indai ba abinda ya zama dolensa ba to a cikin kudinsu suka ce sun yarda kowa ta saka hannu to ita Adda a nata baqin wayon da ganin tasha kansa bata dena ba ta ci gaba dacin kudinta hankali kwance ba tareda ta sani ba shi kuwa yana lissafe da komai ga kuma takaddu saboda Adar rai. To tun jiya daya fita ya yanke shawarar cikin 500 din data rage mata ze biya mata bashin nan dan ba ita kadai ba harda shi take zubarwa mutunci maqota kullum na jiyo an zo karbar bashi gidansa bayan Allah ya rufa masa asiri.

Jiyan Indo na zuwa ya fito a gaban Fatu ya zaro kudi ya bata ta qirga su cif sun cika tace mata “Allah ya taimakeki wallahi da dukan yau se yafi na jiya kuma wallahi ko da wasa karki kuskura naga qafarki kinzo neman abu gida na dan ance ba kunya ce da ke ba se ki dawo” ita dai tayi muqus harda yiwa Alhaji godiya yace mata
“Godiyar me zakimun a cikin kudinki na biya miki ai ba nawa ba tunda haka kika zaba se kiyi tayi wata ran idan ba kiyi hankali ba suturar da zaki daura se ta gagare ki indai baki dena cin bashi ba.

Yana fita wayar Bashir na shigo wa Adda ta zabga Hamdala tace kin gani ko a sannu a sannu komai ze daidaita maza ki daga ki rushe da kuka duk kibi ki hargitsa shi ki samu yazo ko ya turo mana wani abun, haka akayi tana dagawa ta saka kukan.
Seda ta tsagaita ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta jikinta tace da sauqi.
Chapter 9 · 0% Book details