← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 158

Sashe 49

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bashir kuwa Yana shiga ya zube akan kujera, yunwa, gajiya da bacci sun hadar masa gaba daya. Kallonsa yaran suka shigayi kamar sunga baqo kafin suka gaishe shi ya daga musu kai dan baze iya bude baki ba.

Yanda Asma’u tayi kamar bata san da wanzuwarsa a gurin ba yayi bala’in bashi mamaki, shirinta ta ci gaba daya yi. Yana kallo suka qarasa cinye abin karin su yaran sukayi masa sallama suka fice gurin mota ita kuma ta shiga daki ta dakko jakar ta.

Ina sane nayi tamkar na manta dashi a gurin, yana ganin nayi hanyar qofa yai saurin dakatar da ni da muryarsa a har dashewa tayi saboda yunwa yace “Ma’u baki ganni ba zaki tafi kuma”.

Seta na dakata na kalle shi, da dan guntun murmushi a fuska ta nace “Na ganka Baban Ali ai nayi maka sannu da zuwa tunda ka shigo ko baka ji ba?”

“Hmmm” ya fada kafin ya yunqura yana cewa “Nagaji wallahi a mota na taho, gashi qarfe goma ya kamata inje office ki taimaka mun da abinda zanci bari nayi wanka”.

Se da na saki wata dariyar takaici, ina kada key din hannuna nace “wato ka rantse dai se ka biyo mota toh ai gashi dai kaji abinda ake ji. Abinci kuma akwai komai na buqata a Kitchen se ka nemawa kanka kaga mun makara ma se mun dawo” na juya nayi tafiyata ina jin yanda ya raka ni da kallo har na kulle qofar.

Wato daga dan rainin hankali se Bashir, Allah ya qara. Abinci kuwa babu komai a Freezer mun cinye kwana biyun nan kuwa ban zauna ba bare nayi ko miya ce na ajiye.

Malam Bashir kuwa dakyar ya iya miqewa ya shiga Kitchen din, ya zata ze samu ko ragowar abinda sukaci ne ya tarar da wayam, ya bude Freezer nan ma danyun nama ya tarar babu ko guntun abinci.

Cike da takaici ya bude Fridge din shima babu komai se tarkacen ruwa da lemo se wani guntun nama ya samu a foil paper ya dauka da sanyin sa da komai ya cinye.

Ganin fa babu mafita ga yunwa ga lokaci na sake qure masa yasa ya kunna Fanfon Kitchen din ya tari ruwan zafi, Madara da Milo ya zuba sosai ya dagawa daya ya kwankwade ya sake hada wani yasha rabi ya hango bread ya dauka ya hada, seda yaji cikin sa ya dan farfado sannan ya haqura yaja kafafuwansa ya tafi daki.

Wayar s ya fara sakawa a chaji dan tun a hanya da dare ta mutu, Yau daya se be ji haushin abinda Ma’u ta masa ba, idan da haka kawai ne tayi masa wannan wulaqancin yasan me raba su se Allah amma yau daya tuna girman nasa laifin se yaga ai ba komai tayi masa ba.

Kamar me maye haka yana layi yayi wo wanka ya fito, badan ba kwanciya zeyi ya dan rage bacci amma yasan tabbas ya kuskura ya kwanta a yanda yake jin baccin nan qila sedai ya farka yaga magriba tayi.

Bayan ya saka kayan sa ya tattara abinda ze buqata kafin ya kunna wayarsa yayi order Bolt, se ya fito qofar gidan ya zauna kamar wani Almajiri, yunwa yake ji dan ba wai ya qoshi bene kawai haqura yayi idan ya fita se yaci abincin sannnan ga bacci har ji yake kamar zazzabi ze rufe shi, haka ya hau motar suka kama hanya.

A cafeteria office din su yaci abinci, Patrick abokin aikin sa da suka shiga tare ya ringa kallonsa da mamaki ganin yanda yake lodar abinci kamar wanda ya shekara be ci ba, kasa daurewa yayi yace masa

“Bash lafiya kuwa ji yanda kake cin abinci?”

“Bazaka gane ba, rabo na da abinci tun shekaran jiya”.

Dakyar ya iya kaiwa qarshen meeting din, suna gamawa suka fita sallar Juma’a. Bayan sun dawo Office din sa ya koma ya kwanta ya ringa bacci ba shi ya farka ba se qarfe bakwai shima Security da suke bi office office ne bayan an tashi suka ga fitilar sa a kunne dan haka sukaje su duba ko lafiya tunda be saba kaiwa dare a gurin ba.

Haka ya tattara a gida ya wuce gida, da murnar sa ya shiga dan tun daga waje ya jiyo qanshin tuwo da miyar kuka harda man shanu abinka da me jin yunwa.

Ya bude qofar ya shiga, fuska a sake Ma’u tayi masa sannu da zuwa harda tambayar ya akayi yau ya dade yace bacci ne ya kwashe shi.

Da zumudinsa yai sallar magriba da Isha ya sako jallabiyya ya dawo palour aka kame akan kujera yana jira ayi masa tayij abinci ya kwashi gara amma har kusan minti goma da zaman sa yaji shiru sema harkar gaban su kawai suke.

Gyaran murya yayi yana kallon Ma’u dake dannan waya yace “Akwai abinci ne yunwa nake ji”

Seta dakata ta dago ta kalleshi da murmushi tace “ai kuwa babu dan ban san zaka dawo ba”.

“Kamar ya baki san zan dawo ba ce miki nayi zan tafi wani gurin ko yaya, sannan nida gida na ayi abinci ace baza’a a jiye mun ba saboda me? Haka fa dazu da safe kika ce mun akwai abinci na duba ko ruwan zafi baku ajiye ba” ya fada a hasale, dan ya rigada ya gama saka rai da Tuwon.

“Ko ajikina na sake gyara zama nace “Aa abin bana zafi bane bafa Baban Ali, gani nayi yanzu ai Idan zakayi tafiya baka fada seka isa inda zakaje toh gudun kar mu ringa asarar abincin yasa mukeyi dai dai cikin mu, idan kace zaka ci se a dafa dakai”.

Abubuwa sun sha kaina, idan na samu sarari zaku jini gobe idan kuma ban samu dama ba se Monday In Sha Allah 🙏🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 28

Washe Gari Asabar tunda nayi sallar Asuba na koma bacci ban farka ba se goma na safe. Ko yaya Bashir ya qare jiya oho dan tunda na gaya masa babu abinci naji ya fara jan kwafa da tsaki na kwashi qafafuna na bar musu gurin, dan karma a biyo ni a dameni seda na murzawa qofata key sannan na kwanta.

Tsaf na shirya cikin wani Material baqi doguwar riga bayan nayi wanka, tundaga dakin nake jiyo kaya kaya alamar Game suke ko ana musu akan wani abun ina bude qofata Yan biyu na suka taso da gudu suka riqe ni.

“Kai ni yunwa nake ji karku kadani me kuka ci ne” na fada ina kama hannayensu, se Ahmad yace “Indomie Yah Amna tayi mana da Tea Abbi kuma gashi can yanzu aka soya masa Irish”.

Kallon inda yake nuna mun nayi muka hada ido da Bashir daya watso mun wata harara kamar idonsa ze fado, duk yanda naso na basar seda dariya ta kufce mun dan haka na wayance ina nufar inda yake nace “Baban Ali barka da safiya, kace kaima yanzu ka tashi? Bari nazo muci dan Allah yunwa nake ji idan bamu qoshi ba se a qaro wani” nayi maganar ina jan kujerar da take kallonsa na zauna.

Ban damu da shirun daya mun ba na fara hada Tea na ina masa surutun da na tabbatar sake qular dashi nakeyi, na gama naja kwanon dankalin, sena bude baki ina kallonsa nace

“Kai Duk wannan da kai kadai zaka cinye shi?”
Can qasa kaman an fuzgo maganar daga bakinsa naji yace “Banci abinci da daddare ba jiya da yunwa na tashi”.

Kallonsa nayi, naji tausayinsa kadan dan nasan Bashir da abinci ci ne dashi kamar dan kwallo, cikin jimamai nace “Ayya meyasa ka kwanta da yunwa da ka saka Amna ko Spaghetti ce ta dafa maka ai”.

Shiru ya sake yi mun, nima ban sake magana ba na fara cin abinci na, ya rigani gamawa, seya miqe ya shiga dakinsa ba dadewa ya fito ya chanza kaya ya saka Caftan na Yadi kansa babu hula. Key din motarsa ya dauka, be mun magana ba ya fice yara suna masa a dawo lafiya.

Harya tada motar se gashi ya shigo, ko me ya tuna oho se ji nayi yana cewa “zan fita amma ba jimawa zanyi ba saura yauma karku ajiye mun lunch”.

“Wa ya isa yaqi ajiye maka, jiyan ma aka si aka samu baka ce zaka dawo ba, amma yanzu tunda munsan kana nan ai zamu girka da kai” na fada ina dan murmushi. A raina nace “da bakayi magana ba wallahi yau ma dakaga Akuya sedai ka siyo ko kayi wunin yunwa.

Jellop rice nayi da pepper soup din tarwada, sena yiwa Bashir pepper meat dan baya cin Tarwada shi se gasashshiya.

Muna cikin yin lunch Amna ta kalleni tace “Mami idan mun gama muje gidan Baba?”

“Za kuje ku dame su ko kunsan dai yau Weekend Baba yana nan zaku hana shi hutawa”.

Bashir ne yace “Baya nan Ya tafi Zamfara tun jiya, idan kun gama kuje dama yau baza mu fita ba sedai ko gobe”.

Muna gama cin abincin kuwa bayan sun tattare kwanukan suka tafi ita da Farida dasu Ahmad, Aliyu da sauran kuwa Ball suka dauka suka tafi Filin da suke bugawa gidan ya rage daga ni se Bashir.

Qin zama nayi na shiga qaqale qaqalen ayyuka dukda na fahimci nufin Bashir, ganin da yayi bani da niyyar saurar sa, ina tsaye ina goge show glass din farantai a Gurin Dining kawai naji anyi sama dani, duk yanda naso nayi tawaye a dole fushi nake amma yaqi bani dama, daman abin be kai zuci ba kuma nima nayi kewar sa nan da nan nima na bada kai bori ya hau sosai kuwa na gigita Bashir.

Ina zaune a gaban mirrow ina Busar da kaina bayan nayi wanka ya shigo dakin yana waya, ta cikin mudubin muka kalli juna murmushi me kyau da narkar da zuciya ya sakar mun kafin ya qaraso ta bayana yana taba Gashina yaci gaba da maganar sa be jima ba ya kammala seya ajiye wayar akan mirrow ya karbi Dryer yana cewa “Dama baki wahalar da kanki ba dan ba’a gama ba”
Chapter 49 · 0% Book details