← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 158

Sashe 2

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanciya nayi kan gadona ina replying whatsapp messages daga nan muka shiga hira da yayata Alawiyya da muke Uba daya, tamu tazo daya nan na shiga bata labarin abinda Baban Ali ya tsiro dashi kuma. Dariya tayi tana cewa "kedai da Engineer Miskili kafi mahaukaci ban haushi" nan muka ci gaba da firar mu ban san lokaci ya tafi ba seda naji ana kiran La'asar.

A dakin nayi sallata ina idarwa na shiga wanka, daidai na fito naji Knocking nasan yaran ne basa shigomun daki sena basu izini koda kuwa Ahmad da Muhammmad da suke qanana. Bayan na amsa Abdallah ya shigo, sak kamanninsa da yanayin Miskilancinsa irin na Bashir ne sedai duk cikin yarana ya fisu haquri wannan kuma halin takwaransa wato mahaifina ya gado. Cikin sanyinsa Yace "Mami Wai Abbi yace kiyi masa text na abinda zamu taho miki dashi".

Se naji wani dus kamar yaya na masa text? Ba tare zamu tafi ba? Har na bude baki da niyyar tambayarsa se kuma na fasa nace masa " Kacewa Abbi ya leqo ina son magana dashi". Da toh ya amsamin kafin ya fita ya barni da mamakin wannan sabon rainin hankalin.

Abbi
Lokacin da yaron ya gaya masa saqon har sun shiga mota ya ma kunnata, ganin idon su ya sahe cewa yana zuwa ya fito yana qara daure fuskar sa. Tana shafa wa santala santalan cinyoyinta mai ya sameta, yaso ya shagala da binta da kallo dan a duniya ASMA'U takai duk inda mace ake so takai, Asma'u mace ce guda harda Rabi wallahi ta ko ina ta hadu bakuma ze taba manta halaccinta a rayuwarsa ba shikansa ya kasa gane dalilin da yasa yake mata wasu abubuwan. Waiwayowan da tayi tana qoqarin sakin towel din jikinta dan sam bata ji motsinsa ba yau saurin juya fuskarsa dan a wannan bangaren baya taba iya tsallake tarkonta. Jikinta tamkar Magnet yake ga idonsa, a kullum gani yake kamar qara mata kyau da sura akeyi Ma'u bata tsufa.

"Au Abbi ka shigo ashe, Ban gane me Babana yake fada ba yau kuma danwaken zagaye zakumin kenan" na fada ina cigaba da zura rigata dan nayi sauri na shirya nasan Bashir baya son jira sam a zatona ma dalilin daya sa zasu fita su barni kenan.

"Nop banyi niyyar fita dake bane, kiyimun text din abinda zaki ci mu taho miki dashi in kuma beyi miki ba shikenan" kawai yasa kai ya fita.

Se na raka bayan sa da kallo kawai kamar wata doluwa, " tofa Baban Ali kodai gamo yai da Aljanu ne" na tambayi kaina ina qara cika da tsabar mamaki.

Share
Share
Sharehttps://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM

Page 2

WATA KISHIYA(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Ni kadai tsuru kamar mayya a gida har qarfe 10pm ga gyangyadi inayi amma na kasa shiga daki na kwanta saboda tsoro gashi har sannan basu dawo ba. Tsayuwar motarsa da naji ta sani miqewa daidai lokacin da Ahmad ya kwaso da gudu yana kwallamun kira "Mami Mami"
"Na'am Ahmad meya faru" na fada ina tare shi, labarin inda sukaje ya fara bani, gurin wasan da ya kaisu, Favorite restaurant dina sukaje suka ci abinci daga nan suka tsaya Cinema sukayi kallo abinda ya saka su yin dare kenan.
Saboda gajiya kowa dakinsu suka nufa, dakaina nayiwa Twins wanka na shirya su kafin 11pm gida yayi tsit duk sunyi bacci sannan na shiga dakina raina yana suya,
Tsabar bacin rai ko takan take away din da sukamun ban bi ba nima wankan na shiga ina sake danne zuciyata na shirya na nufi dakin Baban Ali.

A kan gado na sameshi yayi daidai yana amsa waya fuskarsa dauke da wani shegen murmushin da bazan iya tuna rabonda yayi mun shi ba ko ba'a fada ba nasan da Amira yake waya dan Baban Ali bashida kwashe kwashen yammata, Ada ni kadai ce a rayuwarsa kafin ya kwaso min Alaqaqai.

Wayar dana tarar yana yi ita ta qara bata mun rai saboda wannan ai wulaqanci ne ko? Nasan matar sa ce amma ya kamata nima ya mutuntani idan zeyi wayarsa se ya nemi kebantaccen wuri bawai cikin dakina akan Gado na ba, wannan sabuwar ta'asar da ya samu ta fara kaini bango dan haka ban san sanda na saki wani wawan tsaki ba ina janye ido na daga kansa bayan mun hada ido.

"Ke dawa kike tsaki?" Ya tambayeni still wayar na kunnensa.
"Ni da waye a dakin" na fada raina na qara quna.

"Anty ce ko" na jiyo muryar Amira na tambayar sa daidai sanda na duqa kusa dashi dan na dauke Safar daya ajiye akan gadon sena daga sauti yanda nasan zata jiyo nace "Nice din yar iya ko kina da magana ne"

"A ko yaushe ina gaya miki ki ringa jan girmanki ko? Amma shikenan" ya fada yana miqewa daga kan gadon ya nufi qofa. Wani baqin ciki ya tokare mun wuya, kawai na haye gadon na kwanta tareda fashe wa da kuka.

Duk yanda nake daurewa se Bashir ya qure ni tunda ya auri yarinyar nan ban sakeyin sati ba tare da nayi kukan baqin ciki ba shikenan ni a haka zan qare? Bansan sandaya dawo dakin ba na dai farka cikin dare naji mutum ya kwaqumeni aiko na ingizashi da qarfi har seda ya farka na tashi daga gadon na shige toilet. Fitsari nayi na dauro Alwala, hijabina na zura na fara jero Salloli tare da dogayen Addua.

Kamar kullum a duk sanda muka samu sabani na fara sallar dare nan haka ze zabga tagumi yana kallona in ya gaji shima ya to Alwalar ya tada Sallah (bawai dan banayi ba Aa nafi tsawaita Idan mun yi fada dan karna kwanta kusa dashi dan duk bala'i bama raba gado 😂😂) nasan me yake tunani qila qarar sa nake kaiwa gurin Allah ko 😂😂 wallahi ko daya duk abinda Bashir yake mun ban taba yi masa Allah ya isa ba sedai ma in roqi Allah daya yafe masa ya kuma bashi ikon Yin Adalci a tsakanin mu ya ci gaba da bashi yanda zeyi ya kula damu. Ko ba komai nasan Bashir yana sona nima kuma ina sonsa to ban rabu dashi a lokacin Matsi ba se yanzu da dadi ya samu se in tafi in barwa yar taka haye?? ina ba wannan magana.

Ban sallame ba har seda aka kira sallar Asuba, ina kallonsa ya fita masallaci kafin nima na tashi nayi Raka'atanul fajir sannan na bada Farillah. Rashin samun bacci cikin dare yasa ina idarwa ko Azkar ban samu yi ba na koma bacci, sanda na farka goma harta gota dan haka anan dakin nayi wanka na shirya kafin na fito palour.

Ko ina qalqal sun gyara dan ko kadan banyi wasa wurin koyawa yarana aikin gida ba komai nidasu mukeyi bani da me aiki tunda har kuma yanzu dana ke fita aiki da safe kafin mu fita mukeyin komai tunda kuma ba wuni muke a gidanba baya yin datti. Babu kowa a palor se Baban Ali yana aiki a system dinsa ya dago yai mun kallo daya tareda mai da kai ya cigaba se na qarasa kusa dashi ciki ciki nace masa ina kwana dan har yanzu haushin sa nake ji, se ya amsa ba tareda ya kalleni ba.

A dakin Boys najiyo hayaniya da alama PS sukeyi tunda suna da Tv a dakin nan suke yin Game dukda lokaci da yawa yana dauketa saboda karsu shagala da wasa a qi karatu amma Weekend dama aikin kenan wani sa'in hardashi zasu hada anan palour suyi.
Kitchen na nufa dan naga sun kwashe kayan kan dining, a roba na tarar da dankali ciki ruwa an yanka su, nasan Amnace ta ajiyemun tunda tasan nafison dankali da an kwashe daga wuta nan da nan na maida man da sukayi suya na zuba kafin na debo kwai guda uku na fasa tareda zuba abubuwan da nake da buqata a ciki, ina kwashe dankalin na maida wani pan din na soya kwai, scramble nayi dan ban fiya son me fefe ba na juye akan plate din chips na zuba Ketchup a gefe na fito. Ta gabansa na wuya ina juya jiki tareda baza masa qanshin turarukan dana fesa aikuwa naji yanda yaja numfashi da ajiyar zuciya ina kuma jin idanunsa akaina har na zauna a dining amma kafin na juyo ya dauke idonsa, girgiza kai nayi ina sake cika da mamakin Bashir a raina haka naja kayan tea na hada ina ci ina dan kallon drama da akeyi a Tv.

Har na gama ci babu wanda ya leqo a yaran Gogan ma anata latsa laptop kamar besan Anyi digona a palour ba sena taso na dawo cikin palour na nemi 1 sitter dake facing nashi na karkace ina latsa wayata nima. Whatsapp na shiga group dinmu na Secondary na bude aikuwa na tarar da chats bila adadin, ban samu damar bi ba saboda wasu ne suke qara shigowa se kawai na fara bi daga nan. Ban karanta message din mutum hudu ba na fuskanci dalilin ubannin messages din dana gani ashe Labor zaayiwa kishiya (Labor prefect dinmu da muna school kuma abin dadin qanwar daya daga cikin yan ajin namu qawarta ta hannun dama zaa auro mata, tasan mijin zeyi aure amma bata san yarinyar ba se yau da taje karban lefen Qanwar Qawarta taga dangin Mijinta ne yan kawo lefen 🤣🤣😂😂🤣🤣😂)

Wata muguwar dariya na sheqe da ita har ina kwarewa da ta saka Baban Ali dagowa ya zubamun ido, yasan Ma'u sarai tabbas mugunta ta gano shine dalilin wannan Dariyar. Be gama tunanin kuwa ba na fara voice note still ina dariyata nace "Alhamdulillahi layi ya fara ja ashe? To Allah ya qarawa mazajenmu budi suyi ta auran mana qannemu" na tura ina sake sheqewa da wata dariyar ganin yanda Safiya Sani Labor keta kumfar baki da daukan Alwashi kala da kala ita ma yayar Amarya Zulaiha Balarabe tana aiko da nata.

Masifar da Safiya takeyi seta tunamun da lokacin da za'ayimun tawa kishiyar mun hadu gurin gate together dabanyi niyyar zuwa ba saboda a lokacin bana cikin nutsuwata. A kallo daya zaa gane damuwar da nake ciki duk na hargitse, na tuna yanda ta sakani a loko tana mun wa'azi.
Chapter 2 · 0% Book details