← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 158

Sashe 124

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan mun gaisa Amnah ta tafi kawo mun abin kari se Farida ta dawo kusada ni tana cewa
"Mami kin san me?"

"Meya faru sarkin labari?"

"Mami, Addah ce fa tazo yau, gasu can se fada suke da Abbi yace seta tafi shi bece a turota ba ita kuma tace ba inda zataje. Nidai Mami na dawo nan gidan da kwana dan Kinsan halin Addah fada ne da ita har da dadddare nasan hana mu bacci zata ringayi".

"Ikon Allah" na fada ina karbar Kofin shayin da Amnah ta hadamun, hankali kwance na shiga cin abincina har na gama ba tareda na bawa Farida amsa ba can qasan raina ina mamakin dalilin zuwan Addah.

Ina shirin tashi daga gurin naji an doko sallama bana buqatar qarin bayani nasan wacece lokaci daya na hade fuskata tsaf yanda kasan ban taba dariya ba a duniya ina kallon qofa daidai sanda ta shigo cikin palour fuskar ta dauke da wannan dariyar tata dana kira data qeta tana cewa

"Ga baqin Asuba ko da yake rana ta daga ai. Se kuka ganmu babu sanarwa ko?"

Ban amsa ba sema harde hannu da nayi a qirji ina qare mata kallo har ta zauna akan kujera. Idan ba ido na ba se naga ta zabge babu wannan qibar kuma tayi baqiqqirin kana ganinta kasan tajin qari matuqa.

"Asma'u ina kwana?" Maganar ta ta katse ni, daga tsayen na amsa mata da
"Lafiya" na qara daure fuska. Ina kallon yanda ta bini da ido alamar mamaki qarara akan fuskarta kafin kuma ta waske tana cewa

"Uhm daga dayan gidan naku nake, kinsan qanwar taki bata da lafiya an kwantar da ita a Asibiti ciki ne da ita shine fa nazo zaman jinya ashe u Asibitin naku ba'a kai musu me jinya.

Jirgin Asubanci muka biyo ko karyawa banyi ba, ga Bashir da baqin hali wallahi ko ruwa be bani ba in gaya miki ya ma fice ya barni a gida ni kwal kamar mayya ni ba iya amfani da kicin din ku na zamani nayi ba shi kuma wancan me kama da uban nasa ko kallon arziqi be mun ba shima daya.

Shine fa na fito waje sena ci karo da dan kirki Jafaru yace na shigo nan na samu na sakawa abakin salati".

Tsam nayi ta gama rattabo jawabin ta kafin na juya dakina ina cewa

"Ayya gashi kinyi rashin sa'a fita zamuyi muma. Koma ba haka ba baki sanar mana da zuwanki ba dan haka ba'a dafa dake ba".

Sena waiwaya na kalli yaran da sukayi tsuru suna kallon mu nace
"Ku tashi ku shirya fita zamuyi"
"Mami ina?" Abdallah ya tambayeni, sena harare shi nace

"Inda ka aikeni ubana".
Ina shiga dakin na kwalawa Amnah kira ta biyo ni da sauri.

"Ko ruwan fanfo ku ka bata senaci uban mutum wallahi ku wuce ki shirya Yan biyu ku jirani a waje" na fada cikin sigar umarni.

Harna fara qoqarin chanza kaya wata zuciyar tace mun to akan me zan fita ma ta koma inda tazo meye hadina da ita toh? Se kawai na kwanta akan gado na sake kwalawa Amnah kira nace mata

"Kije ki ce mata ta fita zaku rufe gida ne" jim naga tayi alamar bazata iya ba, na ja tsaki ina miqewa nace "matsa mun daga nan"
Na bi bayanta muka fito har sannan Addah na zaune ta rafka tagumi kamar wadda akawa mutuwa.

Fuska a daure ba tareda na kalleta ba nace
"Ki koma can gidan ina so mu rufe qofa saboda baqi masu shigo maka ba tareda iso ba".

Allah sarki se kuwa ta miqe tsam da natacviyar qatuwar pos dinta dana rasa uwar datake durawa a ciki tana kallona tace

"Toh bari naje, amma dan Allah ko gayan biredi idan kuna dashi ki bani sena hada shayi koda ruwan sanyi ne nasha tunda naga madara a can din".

"Kije za'a kawo miki" tayi mana sallama kuwa ta fice.

Kwai na saka Amnah ta soya mata guda shida nace su hada mata da biredi sinqi daya me yanka yanka ta bawa Jafar idan yaje ya jona mata ruwa a kettle seta sha shayin na sake komawa dakina ina shiga wayata dake kan mudubi ta fara qara.

Yusuf ne, na daga da sallama ya amsa yana cewa
"Amaryata barka da safiya" Yusuf ya fada daga daya bangaren

"Wacece Amaryar ka?" Na tambayeshi ina gyara zama se ya bani amsa da cewa

"Wata ce, yau zan shigo Lagos nayi kewar ki da yawa da naso na bari se sati na sama amma naga bazan iya ba ke din kawai nake so na gani dai"

"Wancan satin fa kazo" na fada se yayi saurin katse ni da cewa

"Idan kika ce na zauna sena haqura ya zanyi girmanki ne amma wallahi dagaske nayi kewarki ni kadai nasan yanda nake azabtuwa da rashin ganinki din nan. Ki taimaka mun ki zama mallakina dan Allah ko hankalina ya tattaru a guri daya na dena raba shi".

"Uhm" na fada kawai dan ban san me zance masa ba.

Sosai ya kwantar da murya yana cewa
"Asma'u bana so na sake yin saken da zaki kufce mun, ki amince dani na miki Alqawarin bazakiyi dana sanin bani amanar kanki ba. Na yarda ko bakya sona wallahi zan zauna dake qaunar da nake miki kadai ta isa ta riqe auran mu nidai kawai ki amince mun dan yardar ki kadai nake nema.

Tunda na rasa ki ban sare ba, a kullum cikin Addu'a nake idan harda Alkahiri a tsakanin mu Allah ya tabbatar dashi gashi yanzu bayan tsahon shekaru da har na sare na cire raina akan ki Allah ya karbi Addu'ata ya dawo min dake cikin rayuwata dan Allah Karki sake jefa zuciyata a cikin quncin da ta rayu dashi tsahon shekaru".

"Yusuf wai ka manta da da yanzu ba daya ba, waccen fa Asma'un daka so budurwace me qarancin shekaru yanzu kuwa kana magana ne da Asma'u da ta zama uwa haihuwa biyar fa Yusuf yaya shida a hakan kake sona?"

"Wallahi ke nake so Asma'u kedin nake so ba wata suffa taki ba. Ba aure daya ba ko haihuwa biyar ba idan mazan duniya dukka kika aura kika haifa musu Yaya zan zauna dake saboda ke nake so ba wani abu naki ba.

Yayanki kuma yayana ne Asma'u ko ban aureki ba ni zan iya riqe miki su idan har buqatar hakan ta taso ballantana ace ina auranki ai basu da wani uba kuma sama da ni. Dan girman Allah ki tausaya mun naci darajar tarin qaunar da nake miki ki bani dama na shiga rayuwarki in Allah ya yarda bazakiyi dana sani ba".

Gaba daya yabi ya daureni da jijiyoyin jikina, magiya yake mun akan na amsa zan aure shi ni kuwa na rasa me zan ce masa a lokacin.
Idan na Amsa Yusuf anya banyi gaggawa ba? Meye tabbacin da nake dashi akan zan samu banbancin rayuwa a gidansa sama da irin wadda nayi tareda Bashir?

Idan na auri wani daban yaya makomar Yayana zata kasance tunda nasan ko dama da qasa zasu hade Bashir baze taba bari dan sa yayi agolanci a wani guri ba sannan na tabbatar shika mijin da zan aura baze yarda da zama na a kusada Bashir ba idan na bar nan to yaya makoma da tarbiyyar yarana zata zama?

Kamar ya shiga zuciyata se ji nayi yace

"Nasan me kike tunanin Idan kika aureni zan dauke ki daga kusada Yaranki da aikin ki tabbas zanso hakan saboda zan buqace ki a kusa dani amma in har kinfi son zama anan din zan iya haqura na lamunce miki in har hakan ze faranta miki rainya baki nutsuwar zuciya".

Sosai ya bude mun wuta, na rasa dalilin daya sakashi ma taso mun da wannan maganar a yanzu, duk yanda naso na zille yaqi bani dama gashi ita kanta zuciyata a yau taqi bani hadin kai gurin furta kalaman da zasu saka Yusuf din ya haqura da qudurinsa akaina daga qarshe a dole muka rabu akan ya bani sati daya nayi tunani na yanke shawara akan makomar tarayyar mu.

Acewarsa mu ba yara bane da zamu zauna muna jan lokaci idan har na yarda na aminta dashi a matsayin abokin rayuwata a shirye yake  daya zamemin bangon jingina.

Wannan maganar ta mantar dani batun Bashir na shiga Sabon lissafi da komonton hukuncin da zan yanke akan Maganar Yusuf.

Harga Allah idan har son zuciyata ne zan zabi na koma dakina na zauna da Bashir amma ina tuna cin zarafi da wulaqancin da yayi mun ya sake ni akan yar uwata mace se naji sam koda na koma gidan sa bani da sauran wata qima ko mutunchi a idanunsa. Idan har ze iya tsinka igiyoyi biyu na auran shekara goma sha bakwai akan macen daya aura shekara uku bayana to tabbas qarasa dayar bazata yi masa wahala ba.

Amma zan miqa komai ga Allah zan nemi zabinsa duk kuma abinda yafi kwanta mun a rai zan karbe shi a matsayin zabin da Allah yayi mun wannan na qudurce a raina babu kuma bata lokaci na tashi da kaina na shiga Kitchen, ina da tukunya babba da nake girkin Sadaka a ciki nan da nan na dora Jalof din shinkafa me kyau ban dauki lokaci ba na gama na zuba a robobin take away masu murfi.

A qatuwar roba muka jera su, dakaina na dauka a mota muka fita can kan wata hanya inda daman muke kai abincin na ringa rabawa mutane Musulmao harda wadanda ba musulman ba duk wanda na bawa zance kayi mun Addu'a Allah yayi mun zabin Alkahiri a cikin rayuwata nayi hakan kuma da kyakykyawan yaqinin amsuwar Addu'ata.

BASHIR

A wani gidan abinci ya karya, rashintakamaiman gurin zuwa ya saka yayi zamansa a gurin kawai yana kallon masu shigowa suna fita.

Kusan awa daya yana zaune shidai baze ma iya cewa ga abinda yakeyi ba can dai ya miqe ya fita yana qoqarin bude motarsa yaji anyi masa sallama daga bayansa.

Waiwayawa yayi, Macece budurwa a qallah zatayi shekara Ashirin da biyar zuwa sama ba fara bace amma fatarta bata da duhu kuma ba wata shahararriyar kyakykyawa bace sedai yawan Fara'arta ya taimaka gurin fito mata da kyau me sanyi.
Chapter 124 · 0% Book details