← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 158

Sashe 64

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karba nayi ina cewa “In sha Allah za’a dace, Alah ya bada nasara”.
“Amin” ya amsa mukayi sallama ya tafi ina juyowa mukayi kicibus da Fahad sun taho shida Anwar yayan Alawiyya da take bi.

Fahad qanin Hajia Anjin ne shine auta a gidansu, Fari kyakykyawan saurayi me qirar larabawa ga iya soyayya dan da ace da Fahad na fara haduwa kafin Bashir inaga da yayi nasara akaina saboda iya tsara zancensa.

Hararar sa nayi ta gefe ganin irin kallon da yake mun yana murmushi kafin nace “Uncle Fahad ina wuni”

“Karma ki wani ce mun Uncle, yau dai naganshi daman akan wannan Kika qi ni Asma’u gaskiya kin fado da yawa, har naji sauqin radadin da nake ji tunda nafi wanda ya kasanin sau dari wallahi kuma har yanzu ban cire rai akanki indai ba gani nayi an daura miki aure ba bazan cire ran zaki zama mallakina ba” Fahad ya fada yana kafeni da idanunsa masu kama dana mage, sena fizgi hannun Mimi nayi gaba ina cewa

“Se kayi ta saka ran ai kar Allah yasa ka cire, wai ace ba’a san mutum amma su kamar mayu sun nace kuma ahakan dai shi yayi mun baku ba”

“Indai akanki ne ki kirani sarkin Mayu ma qarewa kenan Asma’u dan sena cinye ki hankalina ze kwanta”.

“Daga murya nayi yanda ze jini nace “sedai ka ci kanka dan kurwa ta daci ne da ita” na murguda masa baki harda fari da ido kafin na shige inajinsu da Yah Anwar suna mun dariya.

Haka kawai duk wanda yaga Bashir seya kushe mun abuna, su kyau da kudi yake a gabansu ni ba matsala ta bace ba.

Sannu sannu watanni naya shidewa harya rage saura wata daya bikin mu kuma a daidai lokacin muka gama jarabawar semistar farko a ND1 zamu shiga hutu.

Sosia hankalina ya kwanta tunda zancen auren mu da Bashir ya kankama nayi fresh abina na qara kyau da haske musamman ga gyaran jiki da tuni Hajia Umma ta fara tsuma nan da nan jikina ya sake mudewa ko ina ya cika bazaka taba iya mun kallo daya ka dauke ido ba se ka qara.

Bashir kansa wani lokacin idan ya kalleni yakan ce “anya Ma’u banyi zari ba kuwa ki kalli kanki ki kalleni ai se ace dan aiken ki ne ni” in ya fadi haka se nayi dariya nace
“Kai dai ka godewa Allah kadai dan shi yake yiwa bawa kyauta irin wadda beyi zato ba.

Ana biki saura sati uku aka kawo Lefen Junaidiyya daga Birnin Tarayya Akwati na dukan Akwai saiti hudu masu shida shida. Kaya kam sedai ace masha Allah dan komai yaji harda danqareriyar sarqar gwal dinta yar dubai ga kudin da suka doro akai dubu dari haka dangi a ka dauka ana ta murna yarinya tayi Goshi sati daya zagayo aka kawo na Yah Fati da Yah Bilki rana daya suma bangaren kowanne sunyi Bajinta akwatinan su Dozen Dozen da dubu hamsin hamsin akai.

Na Alawaiyya ne qarshe ana saura Sati daya suma suka dunguma masu algaita nayi maroqa nayi aka kawo sha tara ta arziqi kai komai dai se sambarka mutane anata yabawa kowa fadi yake saura Na Ma’u kowa naso yaga Lefeen ama’u yasan ba qaramin Miji na fallo ba nidai a raina nace kwaji dashi idan ma gulma ce ta qare muku dan ni banji komai ba da ganin Lefen su na taya su murna kuma ban damu ba dan tuni Baffa ya gaya mun yacewa Bashir ba se yayi lefe ba ya nemi gidan da ze sakani kawai, dan haka ma ya bayar da kudi masu yawan gaske yace aje Kano a hado mun duk abinda Amarya zata buqata sannan duk wata hidima zanyi ta biki Alhaji Qarami yace na gaya masa ze bani kudin to me ze dame ni kuwa.

Har satin biki Bashir nata fafutukar neman gida, duk yan gidaje masu kyau idan ya tambaya se yaji kudin ya shallake Aljihunsa gashi kuma a qalla dai yana so ya samarwa Ma’u muhalli me kyau kodan halaccin da akayi masa a zamanin nan adauki Mace kamarta daga irin gidansu a bashi babu lefe ai wallahi an gama masa komai.

Dakyar ya samu wani gida anan unguwar su babu nisa sosai, gidan dukda tsoho ne amma fasalinsa nada kyau 2 bedroom flat ne se babban palour harda Gurin Dining ga Kitchen da dan qaramin store sannan daga waje akwai wani dan palour haka qarami ga bandakin baqi a tsakar gidan se dan fili da ze ci mota daya.

Da yake ginin tsohone sunyi dakunan manya a wadace duk girman gado zasu iya dauka kuma da akwai bandaki a kowanne daki matsalar da babu tiles sumuntine a dakunan palour kadai suka sakawa tiles din.

Tareda Aliyu suka sha buga bugar neman gidan, bayan sun samu bayan ya biya Aliyun yace masa ya kamata ya gayawa Ma’u tunda tun wancan satin take masa maganar gidan dan tuni anje anga na sauran har ma jiya an tafi kafin Abuja da Bauchi na su na cikin Gomben ne yayi saura, da za’a siyo kaya ma da farko Anty Saratu Babbar Yayarsu Mace itace akan yin order kayan daman tafi kowa jin takaicin auran Bashir da za’ayi cewa tayi baza’a siya musu iri daya da Asma’u ba dan tasan Bashir bashida gidan da za’a zuba su, seda Hajia Babba tayi mata kaca kaca tace kuam karta kuskura ko cokali abanbanta in yaso idan an rasa inda za’a zuba a bawa Ma’un kayanta ko siyarwa ne tayi tasan dai an mata yanda akayiwa yan uwanta.

Ita dai Goggo nata Ido, ko Suhaima data kira tayi qorafi cewa tayi babu ruwanta matar mutum kabarinsa kuma ita bata ga aibun Bashir ba da za’a ce baza’a aure shi ba.

Washe gari sukaje da ita da Bashir din da Aliyu se Alawiyya yar uwa ta rai da rai. Ita kam gidan ma ya mata a haka, bandaki ne matsalar dan duk ya dafe nan take a cikin kudaden data karba ta ware ta bawa Bashir din dakyar ya karba tace a canza kayan bandaki har tiles din qasa dana bangon a cire, ya hada da abinda yake hannunsa ayi sauran gyare gyare da fenti idan yaso dakunan se a saka carpet kawai a ciki,

Haka kuwa akayi a cikin kwana biyu se ga gida ya dawo sabo dan gyara aka masa gangariya kai bakace tsohon gidan nan bane, ana i gobe kamu kuwa aka je aka jera mata kayan ta sega gida ya fito shar yaji kaya yan order. Gadajenta biyu Yan Turkey masu kyau da tsada ga kujeru na alfarma da kayan kallo kai duk wani abu da ake siyawa yar gata an sakawa Asma’u haka kayan Kitchen sosai Goggo ta gwangwaje su da kuloli tunda duk Baffa ne yake siyan Electronics iyaye mata su saka abinda babu ai kuwa tayi qoqari kai baka ce auran Yaya uku take ba.

Tsaf aka shirya gida har yan jere na cewa wai daman qaramin guri yafi kyan kwalliya se suka ga kamar jerenta na neman yafi na masu manyan gidajen kyau.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 34

Ranar Juma'a aka daura aure na da Bashir, Juma'ar data shiga cikin jerin rana kun tarihin rayuwata na farin ciki da bazan taba mantawa da su ba. A qa'ida ranar da aka daura aure a gidan mu ake kai Amare amma mu ba'ayi haka ba saboda Dinner da manyan Yayyenmu suka shirya zasuyi a daren ranar sauran Yayyen mu mata se tsiya sukeyi wai an fi son mu su kuwa kamar ana jira da an daura ake kwashe su.

Da yake tun ana sati daya da biki muka san da shirin Dinner, nasan dole sauran Angwaye zasu gwangwaje suyi shiga ta alfarma tunda suna dashi dukda Bashir ma nasan ze yi iya qoqarinsa amma baze iya kamo su ba saboda tattalin arziqinsu ba daya bane su duk masu dashi ne.

Haka na samu Baffan mu na tasa shi da naci seda ya bani shadda yadi goma cikin irin wadanda yake dinkawa ni kaina bansan kudinta ba kawai dai nasan suna da kyau kuma ko cikin Mutane ina dadewa banga wanda ya saka irinta ba sefa manyan irinsa.

A gurin Yah Mustapha  na samu hula harda takalmi daya siya dan daurin aure saboda duk gidan mu ya fisu gayu, dakyar ya bani wai order su yayiwo takanas seda mukayi ma zan biya kudin rabi nidai dana samu suka zo hannuna nace a gudunmawar sa, yana ji yana gani na masa fin qarfinsu se na bawa Yah Abubakar shaddar nace ya kaiwa Bashir dinki tunda abokinsa ne yasan Size dinsa na roqeshi dan Allah karya gaya masa ina so na bashi mamaki ne.

"Ma'u kenan, yanda kike son Bashir kike tattalin sa Allah yasa kar wata rana yayi miki halin mu na maza" abinda Yah Abubakar ya gaya mun kenan a lokacin da se naji jikina yayi sanyi.

Gaba daya daman na lura dashi kamar hadi na da Bashir beyi masa ba na rasa dalili dan har tambayarsa na tabayi yace mun babu komai, da yake daman shi ba mutum ne me yawan magana ba se na bar maganar kawai nasan idan da Bashir nada wani mugun abu baze barni na aure shi ba.

Tsaf na hade kayan nan bayan an dawo daga daurin aure angwaye sun shigo aka dauki hotuna, masha Allah gaba dayan mu munyi kyau kuma ko wacce ta dace da zabin ta se fatan Alkahiri dangi da abokan arziqi suke yi mana. Suna shirin ta fiya nayiwa Sadiya qawata rada dan daman ita na bawa ajiyar Kayan tayi maza taje ta dakko su, seda suka fita tabi bayan Bashir din ta bashi.

Muna zaune a bangaren da qawayen mu anan ta hira irin wadda ko wanne qawayen Amarya sukeyi idan ana biki, hayani ya na tashi wayata dake hannuna tayi qara, Bashir ne daman zaman jiran kiransa nakeyi sena miqe da sauri na shige bandaki na kullo qofar ko naji maganar sa dakyau.

"Ma'una kayan menene wadannan, ina kika samo shadda me bala'in tsada haka?" ya tambayeni bayan dana gaishe shi.

"Kamanta an jima akwai Dinner da za'ayi, kalar kayan da zan saka ne zamuyi Anko".
Chapter 64 · 0% Book details