Sashe 119
Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Seda sukayi dagaske kafin bacci ya dauke shi dan fizge ruwan da aka daura masa ya ringayi seda Likitan ya sake gayyato wani suka hadu suka danne shi Akayi masa allurar baccin a jiki kafin ya kwanta lakwas yana kiran
"Asma'u karki rabu dani, wallahi ina sonki Ma'u karki zabi wani a kaina"
Cikin dare ya farka cikin ikon Allah jikin ya masa sauqi nauyin da qirjinsa yayi masa dazu ya sauka, kulolin daya gani suka tuna masa da yunwar da yake ji nan da nan ya janyo kwanukan ya bude.
Tuwon shinkafane da Miyar danyar kubewa dataji naman rago da manshanu.
Ba maganar wanke baki ya zuba ya fara ci loma biyu yayi kamar qaramin yaro ya fashe da wnai irin kuka irin wanda yake bayyanar da quncin da zuciya take ciki ya kifa kansa a qasa ya ringayi.
Likita ne ya shiga dakin dan yayi hasashen yanzu ya farka dan yaga jininsa nada qarfi Allurar bata dadewa take sakinsa yana shiga ya tarar dashi yana kuka ya isa gurinsa da sauri ya dagoshi yana cewa
"Subhanallahi meya faru badai jikin bane? Wane guri yana maka ciwo ne?"
Saitin zuciyar sa ya nuna masa, likita ya kamashi ya koma kan gadon kafin ya shiga hada na'urar dake jikin gadon ze sakawa Bashir din sw ya dakata jin Bashir din yana cewa
"Ina sonta Dr, bana so na rasata na rasa yanda zanyi ni na bata komai yanzu kuma bansan ya zan gyara ba".
Zama Likita yayi a kusa da shi ya zare farin gilashin idonsa yana kallon Bashir yace
"Daman Mace ce damuwarka, Wacece ita?"
"Asma'u, mata ta ta farko kuma uwar yayana. Likita banaan ya akayi shedan yayi mun kururuwa ba nabi rudinsa na rabu da ita wallahi ina son matata amma duk duniya kowa ya kasa fahimtata".
Shiru Likita yayi yana kallon Bashir na wani lokaci kafin ya dakko kwanon da ya saka abinci ya miqa masa yana cewa
"Kaci se muyi magana, ina zuwa" ya tashi ya fita ya barshi.
Tura abincin kawai yakeyi, wani bangare kuma yana jin kamar ya sauke nauyi daya furtawa wani cewar yana Son Asma'u. Amma me yasa likita ya tafi ko dai shina be yarda yana son nata ba kamar yanda kowa yaqi yarda dashi?
Haka ya ringa tura abincin har ya gama yasha ruwa sega Likitan ya sake shigowa hannunsa riqe da wata farar roba da gani ta magani ce.
Robar ya bude ya debo kwayoyi qanana guda biyu ya miqawa Bashir yana cewa
"Kasha, ze taimaka maka ka samu sauqin ciwon qirjin".
"Likita kaima baka yarda ina sonta ba ko? Kaima kana ganin bada gaske nakeyi ba" Bashir ya fada ganin Likita na qoqarin sake fita bece masa komai ba, se ya waiwayo yana murmushi yace
"Bani zaka gayawa ba Malam Bashir, shawara daya zan baka In dai kana so kaci gaba da rayuwa me dadi ka sauke duk wani girman kai ka nemi abinda kake so. Ita mace ba'ayi mata gadara ka hanzarta kafin lokaci ya qure maka, gobe da safe zamu sallame ka in Allah ya kaimu tunda na fuskanci ciwon so ne yake damunka mu kuma bamu da maganinsa sedai mu baka shawarar yanda zaka sauqaqawa kanka indai ba kana so ka saka kanka a hatsarin kamuwa da ciwon zuciya ba".
Haka ya kwana yana juya maganganun Likita a ransa, qarfe goma na safe aka bashi sallama, kamar mara galihu haka ya tattara Samuel yazo ya dauke shi ya kaishi gida sanda ya isa yar gasken da alama ko tashi daga bacci ma batayi ba se ya wuce dakin sa shima ya kwanta akan gado yana ci gaba da saqe saqe.
Kiran Bala ne ya shigo wayarsa, kamar ya share sedai ya daga dan haushinsa yakeji tun ranar daya katse masa kira be biyo baya ba se yau.
"Allah ya taimaki Engineer Allahh sa ban katse maka aiki ba" Bala ya fada yana yar dariya.
Shiru ya masa be damu ba yaci gaba da cewa
"Gani a Lagos na shigo yanzu, idan anjima ka tashi aiki se na shigo nan ta gurin ku"
"Banje aiki ba ina gida yau" ya fada a cunkushe
"Oh dan Allah? Ta bari yanzu naje na kama daki idan na ajiye kayana se na shigo gidan, a sanarwa Madam dam ko Karyawa banyi ba na taho" Bala ya fada daga daya bangaren, se Bashir ya ajiye wayar yana cewa
"Seka iso toh".
Wa ze gayawa tayiwa wani girki ko ya manta da wacce take a gidan sa ne yanzu yake wannan maganar. Wanka ya shiga yayi, yaji dadin zuwan Balan dan yana da buqatar wanda zasu tattauna akan lamarin Ma'u, baya so ya sake yanke hukunci ba tareda shawara ba.
Se daya Bala ya iso gidan yaciyo uwar kwalloya kamar me zuwa daurin aure. A palour suka zauna Amirah ta kawo masa ruwa da lemo daga nan ta shige daki basu sake jin duriyarta ba.
"Mutumin wai Ina Ma'u ne banji labarinta a Gombe ba ko kun daidaita ban sani ba?" Bala ya tambaya yana shan Lemo.
Bashir yaja tsaki yace
"Tana gidanda yake kusa da namu, kasan wai har Ma'u ta manta dani ta fara sabuwar rayuwa tareda wani mutum daban bani ba" ya qarasa cikin jin zafin abinda ya ke fadar.
"Dagaske kai amma naji dadi" Bala ya fada cike da murna se kuma daga baya ya gano shirmen da yayi saboda yanda yaga Bashir ya zuba masa ido yana kallonsa se yayi saurin wayancewa yana cewa
"Ina nufin naji dadi da kace tana kusa daku kaga yanda zaku fi samun daidaito da wuri kenan"
"Bazata saurare ni ba Bala, idan ta ganni nunawa take kamar bamu taba hada komai a rayuwa ba Ka bani shawara ya zanyi na dawo da Ma'u rayuwata Bala kai kafi kowa sanin ina son Matata"
"Na sani Bashir amma yanzu yayi wuri da ka nuna karayarka, kafi kowa sanin irin son da Ma'u takeyi maka na tabbata bazata taba iya rayuwa da wani namiji idan ba kai ba. Ko kaganta da wani is sedai tayi dan ka gani rabka ya baci amma na tabbatar badan wai tana son sa ko akwai wani abu a tsakanin su ba.
Ka qara haquri mutumina karka manta fa laifi tayi maka ka hukuntata idan ka karaya yanzu ka bata qofar da a gaba zata taka ka yanda take so".
"Laifin me tayi mun Bala? Nifa nayi mata laifi na tirsasata yin abinda yake son raina saboda taqiyi na yanke hukunci ba tareda tunanin abinda hakan ze jawo mana ba.
Da bakina na saketa nace ta barmun gidana kana zaton zata manta wannan ta sake dawowa gareni? Bafa abinda tayi mun son zuciyata ne kawai ya kaini da dana sani" Bashir ya fada a matuqar karye.
Bala da yake faman antaya masa harara yayi saurin tareshi yana cewa
"A wata hudun shine har ka karaya haka kake nema ka zubarwa da kanka mutunchi haba Bashir, kai kana zaton Asma'u zata iya zaman aure da wani ba kai ba wallahi ko bayan shekara dari nasan kai zata zaba.
Kai duk duniya fa babu wanda besab irin son da take yi maka ba dan haka ka kwantar da hankalin ka mutumina, in banda kai ma yanzu ga yammata nan a gari birjik basu auruba se bazawara me yaya shida kake zaton daga rabuwarta dakai zata samu miji?
Ka saki jiki mutumina ka ci gaba da harkokin ka muna nan wallahi zata zo har cikin gidan nan ta nemi ka mayar da ita".
Kallonsa Bashir yake har ya gama magana. Ko kusa bega alamar abinda Bala ya fada a wannan karon me yuwu ba bane amma idan ya tuno tarin qaunar da takeyi masa a baya fa se yaga kamar hakan zata yuwu.
Amma ze gwada koda na wata dayane ya gani amma fa daga haka baze iya qara haquri ba, in har bata sakko ba to shi ze ajiye girman kanya nemi sulhu da ita kamar yanda likita ya bashi shawara.
A gidan Bala ya wuni har dare, abinci kuwa se siyowa sukayi dukda har sannan ba wai ya ji garau bane.
Haka ya qarasa cinye satin kafin ya koma aiki yayi iya qoqari gurin rage damuwarsa amma abin ya faskara akullum cikin tsoro da fargaba yake kwana da tunanin rasa Asma'u. Sam ya kasa samun kwarin guiwar da Bala yake ta nanata masa yana ganin lokaci yayi da zeje ya zube guiwoyinsa a gabanta ya roqesta koda kuwa zata sake koda masa marine indai hakan ze sakko da ita daga fushin da take dashi ya amince ta tsinko darbejiya ma ta dake shi son ranta.
Ayi manaji da wannan please na shiga hidimomi ne 🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 54
Washe garin ranar tun goman safe Bala ya sake zuwa, yau ma wuni sukayi dai suna ta tattaunawa duk dai akan Asma'un ne har kuma yamma Bala beyi shirin tafi ba seda Bashir da kansa ya tambayeshi wai ba yace aiki ne ya kawo shi ba yaushe ze fara.
Cikin kame kame Balan yake ce masa
"Eh daman aikin na kwana daya ne mun gama kawai dai ina so na huta ne. Ni na gaji da zaman gida ma mu fita waje mu sha iska kuma ita wannan matar daman haka take bata dafa abinci ne?"
Shiru Bashir yayi masa harya qaraci surutunda yayi shiru, be haqura ba bayan wani lokaci ya sake ce masa su fita waje dole ya takurawa Bashir din seda suka fita wajen suka saka kujeru suka zauna.
Basu jima a gurin ba motar makaranta ta sauke yara, gaba daya suka gaishe su, Bala ya kamo hannun Abdallah yana cewa
"Abdallahn Mami an dawo kenan. Ya naganku a school Bus ina Mamin taku?"
"Daman a school bus muke dawowa" Abdallah ya fada yana shigewa cikin gida yabi bayan yan uwansa.
"Wai mutumin ta dena dakko yara daga makarantar kenan?" Bala ya fada yana yar dariyar nan irin ta wanda yaso munafunci akayi sa'a ko kallonsa Bashir beyi ba hankalinsa yana kan wayarsa da yake dannawa.