← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 158

Sashe 21

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ayi duk abinda ya kamata kafin nazo yanzu zamu taho insha Allah” taji ya fada kafin ya kashe wayar ya shiga diban wasu daga cikin filea din daya zubar. Ita ya miqawa yace “Joseph na waje please ki bashi zamu yi waya”

Karba tayi ta fita a ranta tana tunanin meyake faruwa ne toh, haka ta miqawa Joseph files din tana shirin kowa se gashi ya fito bayan ya kulle gidan gurin wutar gidan ya nufa ya kasheta gaba daya, seta kalleshi tana cewa “akwai kaya a freezer fa zasu lalace”

“Please muje kawai” ya fada yana bude motar ya shiga itama seta bude gaban ta shiga kawai ya tayar suka tafi. A Airport din ya ajiye motar suka tashi zuwa Gombe gaba dayan su Asma’u nata mamakin wai me yake faruwa ne dan dai ba dashi suka shirya tafiyar ba yanayin data ganshi kuma bata zaton ze iya mata wani bayani, koma dai yaya ne Allah ya kaisu lafiya zasu gani Allah dai yasa Alkahiri ne.

Gombe
Daga Airport direct Asibitin da suke zuwa Naziru ya wuce da Bashir da Asma’u yaran kuma Sa’ad wanda Nazirun yake bi ne ya kwashe su a tasa motar suka wuce gidan Dada.

“Hasbunallahu wani’imal wakeel” ta furta lokacin da tayi Arba da Amirah dake kwance tayi wani irin kumburi kamar zata fashe, cikin tashin hankali ta kalli Bashir da shima ganinta a hakan yai bala’in tayar masa da hankali.

A yanda akayi masa waya beyi zaton abun yakai haka ba. Yana Office da Safe Isma’il yayanta da suke Uba daya ya kirashi wai Tana tsaye ta yanke jiki ta fadi dama dai tun Kwana biyu take yawan yi masa qorafin ciwon kai da jiri, ya cewa Naziru ya kaita Asibiti ya kuma je amma taqi zuwa Nazirun ya gaya masa. Beyi mata magana ba dan dama bashine karo na farko ba da zata ce bata da lafiyar in yace akai ta Asibiti taqi zuwa sedai ta karbe kudin ta kashe kawai yanzun barinta yayi se yazo sannan ze kora mata warning se kuma ga wannan abun ya faru.

Da aka kawota Asibitin likitan yake gaya musu jininta ne ya hau sosai da sosai ga kuma alamun preeclampsia tare da ita (jijjiga) kuma daman tuntuni ya gaya mata duk sanda taji wani sauyi ko alama tazo a dubata tunda cikinta ya shiga wata na 7 toh awon ma seta ga dama take zuwa gashi yanzu abinda ba’aso ya faru se fatan Allah ya kawo sauqi kawai.

Suna tsaye jungun jungun Bashir ya tafi office din Dr, acan yake gaya masa dole sedai suyi mata aiki in dai ana so a ceto rayuwar ta dan barin ta da cikin ze zamar mata hadari.

“Toh Dr ai kuma cikin be isa haihuwa ba” Bashir ya fada a sanyaye

“Wannan ba matsala bane Engineer idan an cire shi zamu sakashi a kwalba ne mu cigaba da kula dashi har sanda ze isa dauka amma yin aikin yanzu shine kadai maslahar mu, bansan wace irin yarinya bace ita da bata damu da lafiyar jikinta ba ta yaya ma akayi tana zaune har takai wannan stage din batazo Asibiti ba tunda ba abu ne da yake faruwa lokaci daya ba”

Shidai Bashir bashi da ta cewa, takardar da likitn ya bashi yasa hannu, yace su kwantar da hankalin su babu komai insha Allah zasu ci gaba da monitoring nata su samu jinin ya sauka kafin a shiga da ita aiki suyi ta yi mata Addu’a kawai.

A reception daya fito can lungu ya hango Addah ansha kuka an gode Allah se yan idanu kawai take kiftawa se sannan ya samu suka gaggaisa dasu kafin yacewa Asma’u da tuni jikinta ya mutu tabi Naziru ya kaita gida ta hutu jinawa ze taho. Fatan samun sauqi tayiwa Amiran ta bi Nazirun suka wuce gida.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 14

Seda Amirah ta kwana daya a daren rana ta biyu akayi mata aiki cikin ikon Allah aka ciro mata yar qaramar yarta bakwaini me tsananin kama da Farida, sosai Bashir yayi murnar samun mace sanda aka nuna masa babyn kafin aka sakata a kwalba, tun cikin daren kuwa ya ringa buga waya yana gayawa mutane haihuwar.

Ya kira wayar Asma’u lokacin harta fara bacci dan basu dade daga dawowa daga Asibitin ba suna can ma aka shiga da ita aikin, ganin dare ya fara ga yara yasa ta tafi gida.

“Masha Allah, Allah ya raya ita kuma ya bata lafiya, kace Farida tayi yar uwa Abokiyar shawara” ta fada bayan data daga wayar.

“Wlh fa sema kinganta kamar su daya kamar sanda kika haifi Faridan girma kawai ta fita” Bashir ya fada cike da doki kafin sukayi sallama. Baccin ta ta koma dan dama tunda suka dawo ta rufe gida tasan ba dawowa zeyi ba dan jiya ma can ya kwana seda safe yazo yayi wanka ya chanza kaya bare yau da ya samu ya ai ba batun zuwa gida kuma.

Washe gari da wuri ta tashi ta hau shirye shirye dan tana so taje gidan su yau ga zuwa Asibiti. seda tayi girki tayi musu farfesun Kaji ta soya doya sannan ta damawa Amirah kunun gyada dukda bata san ko zata faracin abinci yau din ba sannan ta dafa Tea suka shirya gaba daya ita da yaran suna ta murna data gaya musu sunyi qanwa. Se gurin goma sannan ta hada komai suka tafi.

Dakin danqam da yan dubiya yan gidan su Bashir da kuma Dangin Amiran se hayaniya sukeyi dan ta farfado tun da Asuba. Ba yanda Likita beyi dasu ba subarta ta huta amma sunqi qarshe haushi yaji yai tafiyarsa ya barsu ya kuma gayawa Nurse kar wanda ya nemeshi in wani abu ya faru dan ya gaji da halinsu kuma.

Aliyu da Jafar ne a gaba sunyi kama kaman kwandon da ta zubo Abincin su kuma suna binsu a baya suka shiga dakin da Sallama. Fuskarta dauke da Fara’a suka shiga gaisawa da mutanen dakin tayi musu barka kafin ta juya kam Amirah da tun shigowar Asma’un ta daure fuska tam taqi koda kallon sashin da take.

“Amirah sannu ya jiki?” Ta tambaye ta idan ta amsa ta to ku da kuke karatu kun amsa abin yai bala’in bawa Aisha Babbar Yayar su Amirah da suke uba daya haushi har seda tayiwa Amiran magana tace “Kina ji tana miki magana saboda raini da wulaqanci bazaki amsa ba”

Bata ko motsa ba kuwa sema cuna uban baki gaba da tayi dama fuska duk a kumbure tana qunquni. Asma’u kam ko a jikinta, yo ita bata ga abin da zesa Amirah tace bazata kulata ba idan kishin nema ai ita ya kamata tayi tunda aita aka aurewa miji, Allah ya raya ta sakeyi musu kafin ta juya da niyyar fita dan dama yaran tunda suka gaishe su sukayi waje abinsu, dab da zata fita ta jiyo muryar Addah na tambayar waya kawo abinci ashe tana bandaki seta juyo ta dawo cikin dakin.

Har qasa ta durqusa ta gaisheta, fuskar Addah kuwa a washe ta amsa mata tana tambayarta ina Mazajen nata tace suna waje
“Au shine suka fita ba su bani kudin cefane ba ai kuwa su dawo dan bazan yarda ba” Addah ta fada cikin sigar wasa. Murmushi kawai Asma’u tayi ta miqe tana musu sallama ta fice.

Wato Yanda Addah ta wanke idanunta bata taba nuna wani abu akan auran Amirah da Bashir na bala’in daure mata kai, mutum, ka kalleshi kawai. A reception ta hadu da Bashir daya je gidansu ya dauko Dada dan Naziru yana makaranta yau, cikin mutuntawa ta gaisheta tareda yi musu barka Dada ta wuce ciki Bashir kuma yabi bayan Asma’un.

“Har kun qaraso kenan, yanzu nake so dama na tafi gidan nayi wanka na huta wallahi duk na gaji” ya fada yana jingina da motar da tuni su Jafar suka shige bayan sun gaisa da Dada.

“Ya kamata kam, abincinka na nan ma na ajiye maka nayi zaton kafin mu fito zaka dawo kuma naji shiru, mu zamu wuce Babban gida qila idan zamu dawo da dare mu sake shigowa mu duba su” Asma’u ta fada tana qoqarin bude motar,

“Bazaki je kiga babyn ba?” Ya tambayeta
“Ai bazasu bari ba ka sani ba komai Allah ya bata lafiya idan lokacin fito da ita yayi zamu ganta ai mu da zata dawo gidan mu da zama ma”

“Eh kuma haka ne, bari na shiga na fito to nima na wuce ku gaida mutanen gidan ban samu na shiga ba wallahi Yanzu ma da zamu fito naga Kamar Alhaji Qarami dasu Yaya Mudassir a qofar gidan ashe yana gari”

“Eh yazo daurin auran yarinyar Amininsa ne jiya saurin da nake tayi kenan ma mu tarar dashi ance yau ze koma” da haka sukayi sallama ya shige ciki ita kuma taja mota suka nufi gidansu.

A can dakin kuwa bayan fitar Asma’u dayawan su sukayi wa Amirah caa akan abinda tayi bata kyauta ba, Addah ce ta tambayi meya faru Anty Aisha ta gaya mata.

“Ai ni na rasa kalar wannan yarinyar dan barikin nan ma na mata bata iya shi ba ke se baqin kishi quru quru meye amfanin sa”

“Wallahi fa Addah in nice ita yanda Anty Asma’u ta mayarda komai ba komai ba ake gaisawar mutunchi ai wallahi sake wa zanyi mu ci gaba da yanda muke amma kin zauna kina quntatawa kanki ita kuwa kina ganinta cikin walwala ji jikinta dan Allah wannan shegen Lashin nasan wlh yafi 100k ga zobuna a hannunta ji qanshin turare dan Allah har yanzu be bar gunnan ba” inji Samirah qanwar Bashir da suke Sa’anni da Amirah.

Hirar su suka ci gaba dayi aka shiga da take qonawa Amirah rai dan duk yabon Asma’u sukeyi ga dabgen kaji suna ci abinsu a haka Dada ta shigo ta same su ta kuwa ji dadin Abincin da ta tarar Asma’un ta kawo dukda ita ma ta taho musu da abinci amma tasan ba lallai ya isa ba tunda kusan duk yaran suna nan.
Chapter 21 · 0% Book details