← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 158

Sashe 11

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin fushin daya gaza boyewa ya fita, mintina kadan ya dawo tareda wani yaro ya shigo palour ya bar yaron a kofar dakin tareda nuna masa gurin yace ga inda zeyi fitsarin nan yaro kuwa ya tsula abunsa Alhaji ya fita ya nuna masa famfo ya taro ruwa suka sheqe a gurin nan da nan ya wuce daman tiles ne. Ciki ya dawo yace da Abida ta biyo shi yai gaba tana baya se palour Hajia Balaraba.

Tana zaune ta hakimce akan kujera ta sheqa kwalliya ta garari ta kuwa yi kyau sosai dan Hajia Balaraba akwai kyan jiki da gayu kai bazakace tabawa Hamsin baya ba. Tana ganin Alhaji ta miqe da fara’a da nufin tarar sa sedai ganin Amarya a bayansa yasa ta gintse fuska a ranta tana tunanin meya faru kuma dan ita bata ma lura da yanayin fuskar Alhajin ba.

“Balaraba me kika zuba a qofar dakin Abida?” Ya tambaye ta cikin kaushin murya. Qirjinta ne ya fara luguden daka zuciyarta kaman zatayi tsalle ta fito saboda razana, ya akayi ya sani to ko wani ya ganta ne? Ita dai a hasashenta babu kowa a gidan dan Tunda da zata fita seda ta saka muqulli ta kulle haka data dawo dakanta ta bude kofar, koma menene bazata bare a gano ta dole tasan yanda zata kare kanta.

Qoqarin daidaita nutsuwarta tayi tana daure fuska tace “Bangane me kake nufi ba Alhaji wani sharrin kuma aka sake qullomin yau ma? Ni duk yau ma ban fita daga part dina ba bare har naje qofarta na zuba abu”.

Kallon takaici da tsana yake binta dashi, se ya miqawa Abida hannu tayi saurin miqa masa wayarta. Video yayi playing ya miqawa Hajia Balaraba dake ta taraddadin me nene a cikin wayar Abidan, ai seda ta kusa Sakin fitsari a gurin saboda kidima nan danna zufa ta shiga keto mata.

“Wane La’anannen ne ya dauki wannan video” ta fada bakinta yana rawa tsabar yanda ta rikice, zata sakw magana ya miqa mata hannu ta bashi wayar yana cewa

“Kici gaba Balaraba sharri dan aikene ki sani duk nisan indai kika aika shi watarana seya dawo miki, tunda har kin raina Allah ya isar da nayi miki akan in kika sake yimun wani abu ko wani daga cikin iyalaina shikenan na barki da Allah kuma matakin qarshe dazan dauka shine wallahi Balaraba idan kika sake zuwa gidan wani malami kika aikata wani abun sihiri a cikin gidan nan kai na ko kan wani nawa, na sani ko ban sani ba to ki sani a bakin aurenki”

Cikin tsananin razani ta dago ta kalle shi dan bata taba zaton tsaurin hukuncin ze kai haka ba, ta bude baki da niyyar neman sassauci yace “Karma kice komai dagaske nake kuma ba igiya daya ko biyu ba dukka ukun nake nufi idan kuma kika aikata a bayan idona ba tare da na sani ba muka ci gaba da zaman aure dake wannan kuma na barki da Allah shi ze bimin haqqin zaman zina da kika sa nayi ba tare da sani na ba” yana kaiwa nan ya shige dakin sa da yake a part din nata, Abida ma jiki a sanyaye ta juya ta fita aka bar Balaraba da dora hannu aka tama tasa kuka zatayi ko ihu?

Wannan shi ake kira da An bata biyar goma bata gyaru ba (Dama ai duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba tabbas tashi ko dumi kuwa ba zatayi ba).

Lagos
Seda Ma’u ta cike satin nan daya raya cif aka sallameta, da safe bayan Bashir da yara sunzo sun tafi tacewa Dr ya sallameta haka. Da kanta ta karbi Discharging later ta hada yan kayanta kafim ta kira Uber ta cale gida (tsiyar garin da baka da dangi kenan).

Koda ta isa gidan bata zauna ba seda ta gyara ko ina tsaf ya dawo mata yanda take so sannan ta shiga hidimar dora girki kuma, aikin ya jata da yawa dan har bayan La’asar sannan ta kammala komai ta jere akan Dining kafin ta koma dakinta kuma ta fada wanka. Tsaf ta shirya cikin wani hadadden cotton lace Army green da akayiwa dinkin Fitted gown datai bala’in yi mata kyau ta fito mata sauran quruciyarta. Indai gayune dole a cirewa Ma’u hula wannan ko a zamanin yammatancinta babu kamarta a kaf qawayenta tana da kyau ta kuma iya daukar wanka ga farin jini Allah ya mata abinda ya sa ta zama ta daban kenan da sauran.

Daurin nan ta kawo shi gaban goshi bayan ta fake gashinta qasa qasa sannan ta saka cogenta ta qara feshe jikinta da turaruka ta shiga juyi a gaban mirrow dan ta burge kanta da kanta ballanta na Kuma Bashir ya ganta tasan duk yanda yake qyashin ya yaba kwalliyarta yau kam se idanunsa sun fado qasa qilan a garin kallo.

Mint flavored chewing gum ta jefa a bakinta kafin ta fito palour ta samu kujerar dake facing kofar shigowa ta dora daya kan daya tana girgizasu tana danna waya ba koyi minti biyar da zama ba ta jiyo tsayuwar motarsu, seta qara gyara zaman ta dakyau tana sauraron shigowarsu.

Aliyu ne a gaba dauke da Laptop bag din Bashir se school bag dinsa daya goya a baya se ga sauran a bayansa. Gaba daya suka nufe ta cike da murnar ganinta a gidan, Aliyu ne yace

“Mami this house can never be complete without you Allah Mami da baki nan ji nake kamar a kango muke kwana amma yanzu tundaga qofa kawai naji it feels like home again ashe kece kika dawo ciki”

Dukan wasa ta kai masa tana cewa “Oh Ali yammata kam se sun bani da dadin bakin nan naka Allah dai ya nuna mun lokacin” se ya rufe fuska wai shi kunya yana cewa “Kai Mami ki dena kunya nake ji”
Gaba daya suka saka dariya, se a sannan ta daga kanta ta kalli inda Malam Bashir yaci burki tunda ya shigo, seta qara fadada murmushinta tana cewa

“Aa Baban Ali yane ka tsaya ka shigo ka zauna mana ko ka qara sa ciki”.

Bashir
Numfashinsa ne ya dauke na wani lokaci sanda yai arba da fuskar Ma’u, tayi masa kyau matuqa gaya da har ya kasa iya cire idanunsa daga kanta. Maganar da tayi ce ta fargar dashi kamar dama me jiran umarninta kuwa se ya taho, kusa da ita inda Farida ke zaune ya daga Faridan cak ya zauna a gurin tareda dora ta a cinyarsa kafin ya maida kallonsa kan Asma’u yace “to naga ne hankalin ki yana kan yaranki kamar ma ni baki ganni ba” ya fada yana kafeta da kallon nan nasa me saka Yammata fadawa soyayyarsa ba tare da sun shirya ba.

Irin kallon da shi ya ringa qara rura garwashin soyayyarsa a zuciyarta har ya tada gagarumar wuta da hauyau ba’a samu ruwa ko iskar da sukayi nasarar kashe ta ba.

Seta tsura masa nata kyawawan idon tana hango abinda zuciyarta ce kadai take da tafsirinsa, a cikin idanun Bashir kadai take iya hango tsabtatacciyar qaunarta wadda babu Algus ko digo a ciki amma ginshiri da baqar izzar sa suke hana bakinsa iya furtawa. Har gara gangar jikinsa takan gaza bashi hadin kai gurin boye sirrin zuciyar tasa dan a duk sanda suka hadu gangar jikinsa na sarrafuwa ne kawai bisa umarnin zuciyarsa bawai kwakwalwarsa da take nan kamar wadda akeyiwa hayaqin wiwi ba, yanzu yai abin arziqi an jima ya tafka na tsiya.

Ganin irin kallon qudar da Abbi da Mami sukewa junansu ya saka Amna kama hannun twins manyan kuma suka tashi gaba daya kowa suka shige dakinsu, miqewar Farida daga kan qafarsa ta ankarar dashi, seya janye idanunsa cikin son basarwa shima ya miqe yana ce mata

“Zan samu abinci kuwa? Gaba daya yau coffee ne kadai a cikina”

“Ai fa ga Kuku ta dawo dole ka nemi abinci babu tambayar ya akai na taho ni kadai ban kiraka ba balle jin ya jikina” ta ayyana a zuciyarta, a fili kuwa seta ce “kayi wanka first, ga abinci nan yana jiranku” se ta miqe ta nufi dakin su Amna.

Se ya rakata da ido kuwa kamar zasu fado din, yanda take juya qugunta da ya fito sosai saboda yanda rigar ta bawa komai haqqinsa ga qarar takalmin qafarta da yake ji kamar qararrawa a cikin qwaqwalwarsa. Wasu busassun yawu ya hadiye tareda lasar lips dinsa da suka bushe kafin yace “Hmmm” (inji me ciwon haqori 😂😂😂) karaf a kuwa a kunnen Asma’u daidai sanda take tura qofar dakin su Faridan

“Idan baka chanza hali ba Bashir wata rana sedai ka farka ka ganka a kabari Maganganun da kake dannewa sun shaqe maka wuya, ayi mutum bakin na son magana amma baqin rai ya hana shi Allah yai mana magani dai”.

Guri ta nema ta zauna dan ba abunda zatayi a dakin dama ta tashi ne kawai dan ta bashi damar kallon kwalliyar tata da kyau. Ahmad daya fito daga toilet alamar wanka a ka masa ta shiga shafawa mai kafin Muhammmad ma ya fito, tsaf ta shirya su, kafin su gama an kira Sallar Magriba dan haka tace suje suyi Alwala ita ma ta fita dan zuwa tayi a bakin qofa suka kusa cin karo da Bashir wanda da alama shima wankan yayi ya chanza kayansa zuwa Jallabiyya Baqa da tayi bala’in masa kyau duk da kasancewarsa ba fari qal ba, Bashir nada kyau irin na Maza me sanyi daya hadu da kwarjinin da Allah ya bashi.

“Kayi kyau Baban Ali” ta fada da zuciya daya dan ita bata iya munafunci irin nasa ba kuma rashin yabon kwalliyarta be taba sare mata guiwa akan ta denayi ba.
Chapter 11 · 0% Book details