← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 158

Sashe 102

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bansan yanda suka qare ba, munfi kusan minti sha biyar da shiga kafin na hango su sun shigo Amirah na bayansa fuskar nan kamar ka tsira mata Tsinke ta fashe tsabar yanda ta kumbura, acan kejerun yan regular naga ya sama mata sit ta zauna, ya dan duqa da alama magana yake gaya mata kafin a fusace naga ya taho inda muke zaune.

Na zata masifa ze zo yayi na qara tamke fuska ta tsaf se naga yana zuwa yaja kujerar da tayi saura ya zauna ya gaida Anty ta amsa masa sama sama nidai na mayar da hankali kan cultural dance da akeyi ina jin yanda idon Bashir yake kaina amma naqi kallon barin da yake.

Wayata dake ajiye akan teburin ce ta dauki qara, yanda kasan shi aka kira ya bi wayar da kallo na kai hannu na dauka, Yusuf ne da nayiwa saving da Abban Takwara, saboda qarar kida banajinsa dan haka na tashi nayi tacan baya gurin inda kujerun su Amirah yake, ta kusa da ita na wuce ina giftawa naji ta saki tsaki ban kulata ba na wuce na amsa wayata.

Gaya mun yayi yana waje nace ya jirani gani nan zuwa, na sake zuwa na wuceta dan banida lokacin da zan tsaya ina kula wannan yarinyar. Seda na koma sit dina, jakata na bude na ciro ragowar kati daya dan Ma'u Jafar ne ya dagata da yake ta sangarta ta lankwashe a jikinsa yanda kasan wata yar Yaye dan haka basu karbi katin taba muna shiga ya bani na saka a jaka.

Ina kallon yanda Bashir ya bini da kallo ganin na ciro wani katin daga jaka, se na juya na cewa Anty ina zuwa na wuce ta saitin Bashir ya shaqi qamshij da nakeyi kuwa kafin ya ajiye numfashi na wuce shi ina juya mazaunan da Allah ya hore mun shi kuwa Ya bini da kallo da baki a sake har na qulewa ganinsa.

A qofar gurin naci karo da Yusuf, wani dace shaddar jikinsa yanda kasan tare muka siya da kayan jikina sunyi bala'in dacewa.

Cikin mutuntaka muka gaisa da wani dana gansu tare babban mutum ne sosai wai shima Sanata ne akwai yaransa biyu a yan Graduation din, ba'a ma karbi katinan mu ba muka shiga tareda Yusuf din kai tsaye teburin da muke zaune na wuce gaba yana bina a baya.

BASHIR
Tunda yaga Asma'u a gurin gaba daya ta sake kwance masa notin kai. Kwalliyar ta tayi bala'in tafiya da imaninsa ga wani kishinta daya taso masa Ganin yanda maza suke binta da kallo.

Tana bashi katin nan da ta juya haka ya rakata da ido gani yake kamar qara mata quruciya akayi dirin jikinta ya sake fitowa, yana can aikin kallonta tsakin da Amirah tayi ne ya dawo dashi hayyacinsa se ya kalleta sanda take cewa

"Yanzu kana kallo ta tafi bayan kaji abinda tace wato nice ma gayyar sodi ko kuma kayi shiru baka ce komai ba"

"To so kikeyi na kamata da kokawa nace seta baki ko kuma nawa zan baki? Daman ai ba gayyatarki ki akayi ba gayyar sodin kika zo.

Kinga ki kama kanki wallahi karki sake kice zakiyi mun shirme a gurin nan zan bata miki rai" Bashir ya fada cikin bacin rai, wallahi da a Gombe nema tafiyarsa zeyi ya barta idan yaso ta koma gida dan dai kawai nan bata san hanya  bane.

Amirah data shaqa iya wuya, dakyar ta danne bacin ranta tace
"To yanzu a waje zaka barni ka shiga ciki kenan" ta fada kamar zatayi kuka

"Seki koma mota ki zauna dan dai ni ban san a inda zan samo miki kati ba kuma nan ba irin taron da kika saba zuwa bane ko ba'a gayyace kuba ku shiga su komai a tsare sukeyinsa" Bashir ya fada yana hararar ta, se kawai ta saka masa kuka tana cewa

"Da kasan wulaqanci zaka mun idan nazo tun a gida se kace bazaka dani ba amma yanzu kace na tafi mota bayan ga katuna can a hannunta harda wasu daban ta gayyato se nice baza'a bani ba"

Tsaki Bashir yayi ganin tana neman tara masa Jama'a dan har an fara kallon su yace mata yana zuwa ya tafi Gurin securities din bakin gate.

Seda yaci wuya dakyar ya samo mata regular card shi kansa dubu goma aka siyar masa, daya bata a maimakon ta gode seta hau sabon qorafi wai ba irin nasu bane dan ko a kala katin ya banbanta.

Banza ya mata suka shiga ya rakata kujerarta se raba ido take ganin Jama'a kala kala yanzu da wannan shagalin za'a mata buqulun zuwa tab, Allah ya kaimu Na Aliyu wannan ai dan mijinta ne itama dole tana teburin gaba tunda yanzu ance mata gayyar sodi.

Hakata zauna wani mugun kishi ga kyashi da hassadar Ma'u na dukanta. Duk abinda ta gani a jikinta ji takeyi dama itace, simple lace me Azabar kyau ga zobuna da awarwaron gwal suma qira mara hayaniya sun qara fito da kwalliyar ta sosai qarin baqin cikinta yanda Bashir ya kasa dena kallon Ma'un ba daban ba da se tace su tafi kawai amma ina setaga kwal uwar daka sannan idan sun koma gida se ayi uwar da za'ayi.

BASHIR
Kwarewa yayi da ruwan da yake sha a daidai sanda Ma'u da Yusuf suka ratso dakin taron kamar wasu shaqiqan masoya fuskokinsu dauke da murmushi. Ba Bashir kadai ba, da yawa mutane seda suka bisu da kallo haka suka qarasa har teburin Yusuf ya daga Ma'u qarama data fasa ihun murnar ganinsa ya zauna a gurin suna fuskantar juna da Bashir.

Fuska a sake ya miqawa Bashir da yayi suman zaune hannu dukda can qasan zuciyarsa bazeyi qarya ba daurewa kawai yayi amma sosai yake Adawa da Bashir din daya rabashi da macen da yake so sama da kowace mace a rayuwarsa.

Ya wargaza masa mafarkin shimfida rayuwar aure me ciki da aminci da qauna qarshe ya barshi da gantalewa da zama macen da bata dauki aure a bakin komai ba.

Malam Bashir kuwa bin hannun Yusuf yayi dake daure da wani shegen Agogon diamond a tsintiyar hannunsa, kai Cufflinks dinsa kadai abin kallo ne wani irin tuquqin baqij ciki da kishi suka taso suka shaqe masa wuya kawai ya mayar da kai gefe ba tareda ya karbi musabahar ba, ko a jikin Yusuf ya maida hannun gurin su Aliyu duk suka gaisa yana tambayar su sunayensu dan ko shine Bashir din akan Mace kamar Ma'u zeyi abinda yafi haka shi yama ga qoqarin sa daya zauna teburi daya dashi ai

Gaisuwa me kyau sukayi da Anty Halima nan da nan suka shiga hira kamar sun san juna dan shima akwai faran faran da mutane halinsu yazo daya dukda da ita da gayya ta qara sakewa suke hirar saboda ta turawa Bashir takaici se gashi kuwa Hira ta barke tsakanin Yusuf da sauran Yaran Ma'u qarama na qara maimaita masa sunayen su se dariya suke mata dan bata iya fada ba ya kalli Asma'u yace

"Gaskiya kin iya bida yara kiga yanda yarinyar nan ta sake lokaci daya anya bazan bar miki ita ba kuwa"

"Ai na yara kadai ba har manyan in gaya maka ta iya tafi dasu ta kowacce hanya me sauqi ko me daci, ka bar mana ita kawai mun samu qarin ya" Anty ta fada tana dariya ta gefe kuma tana hararar Bashir da ya kumbura dan har kamar yafi Amirah kumbura yanzu.

Shigowar yan Graduation ce ta dakatar dasu daga hirar, nan da nan aka shiga gabatar da abinda aka je yi, an raba musu kyututtuka sosai Amna ta samu lambobin Yabo dan ita ta lashe Best Student ta shekarar aka kira Iyayenta, Ma'u na miqewa Bashir shima ya tashi daga kan stage ta hango Amna na tsalle tana nuna mata bayanta tana waiwayawa se ganin Alhaji Qarami tayi tareda Matarsa ta biyu da daya daga cikin Yaransa Abdullahi da suke cewa Baffa.

A tsakiyar Mu nida da Bashir Amnan ta tsaya akayi mana hoto se wani washe baki yake shi ala dole ga Baban Amnah, ganin Alhaji Qarami da Yah Muslim da shima bamu san da zuwan sa ba sun qaraso gurin se Bashir ya dan matsa yana shafa kai amma Alhajin ya sake mayar dashi gefen Amnan su kuma suka tsaya daga gefe da gefen mu aka sake daukar hoton.

Haka sauran yaran dukka suka shiga akayi ta hotuna harda su da Anty. Hoto daya muka dauka tare da Yusuf ya mana sallama ya fita saboda kiransa da akayi.

Amirah tana daga can qarshen tana hangomu baqin ciki kamar tayi bunga dan securities ne ma suka tare hanya kar su yan regular su shiga gurin VIP.

Har kwalla seda tayi saboda baqin ciki, tana gani muka gama hotunanmu cikin farin ciki muka sauka kowa ya koma mazaunin sa kafin taro ya koma na ciye ciye da maqulashe.

Abubuwa ne gasu nan birjik se wanda kake so a ka ringa ajiyewa, ita kanta Amirah ba qaramar gara aka ajiye mata ba amma saboda qalata idonta nakan teburin su Bashir har seda ta kasa daurewa ta zaro wayar tavta rubuta masa text tace

"Yaya naga abincinku ba irin namu bane, ka rage mun zanci nima"

"Ai se kici idan ke mayya ce ko kuma daga yunwa kika fito" Bashir da ransa yayi bala'in baci ya mayar mata da Amsa. Tsabar haushi gaba daya ma ta saka abincin ya fita daga ransa ya ringa zabga tsaki su dai yan gurin ba wanda ya kulashi abincinsu suke loda kawai.

Qarfe sha biyu taro ya tashi, bayan abincin da aka ci a ciki harda wani Take away aka sake binsu dashi, Su Ma'u na tsaye aka kai mata nasu ta bude boot aka zuba Anty ta kama baki tana cewa

"Duk wannan abincin da muka ci a ciki qara raba wani suke yi lallai se a gaishe su"

"Yo ba dole ba wannan uban kudade da suka caji iyaye banda contribution da suka samu daga sauran mutane ai dole kiga sunyi bushasha" shiru nayi lokacin dana hango Amirah na cacar baki da daya daga cikin rabon Abincin da alama hanata yayi se na nunawa Anty gurin yanda kasan da Bashir nake shima ya bita da kallo.
Chapter 102 · 0% Book details