← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 158

Sashe 60

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sena juya ina cewa “ka gaya masa bazan bayar ba idan ya takura kuma seadi kotu ta raba mu” nayi shige wata gida.

A waje kuwa Asma’u na wuce kafin ma Abubakar ya fara magana Bashir din ya katse shi da cewa “Ka gani cikin lallama ka gaya mata ta bani yarana dan wallahi bazan bar mata su ba ballantana ta koya musu dabi’ar raini da kafiya irin tata”.

Seda Abubakar ya qare masa kallo kafin yaja qwafa, ba qaramin danne zuciyarsa yayi ba yace “Naji, zata baka amma kayi haquri kabarsu yau. Nayi maka Alqawari gobe za’a baka yayan ka”.

Shiru Bashir yayi kamar me tunani se yace “Shikenan, Amma wallahi goben idan ba’a bani ba se anyi tashin hankali”

“Babu da wanda zakayi tashin hankali Bashir dan babu wanda yake da lokacin ka, kuma kayi a hankali idan ba haka ba seka rufta kanka a inda duk ihun ka bazaka iya fitowa ba” yana gama fada masa haka ya shige motarsa ya bar Bashir da cizon yatsa.

BASHIR
Ko kusa beyi nadamar abinda ya aikata ba dan a ganinsa yayi irin abin nan na ya tauna tsakuwa dan Aya taji tsoro. A tunaninsa dole Asma’u zata bishi ta roqe shi ya maida ita dakinta, shi kuma ya qudurce se ya gama wanata son ransa tukunna ta gane muhimmancin sa sannan se ya mayar da ita. A lokacin yasan ta biyu ta yanda ko kara ya ajiye mata bazata tsallake ba.

Be damu da kwashe kayan ma da tayi ba, sema guri daya samu a palour ya dora kafa daya kan daya, a cikin kudin da yayi niyyar biya musu umara shida itan ya yi order sabon gadon da za’a saka a dakin da ta cire nata da kuma labulaye kai kujerun ma chanza su ze kawai idan yaso kayan Kitchen in Amirah tazo se ta siyo da kanta tunda shi be san abinda ake buqata ba.

Koda ya shiga dakinsa ma yaga kaya a watse be wani damu ba yasan duk cikin haushin sakin ne yasa tayi haka, se kawai ya tattare ya watsa su kan gado yayi shigewarsa Toilet yayi wanka kafin yayi shirin bacci ya zauna akan kujera da wayarsa a hannu.

Cikin sa da yayi qara ne ya tuna masa da yau fa be ci komai ba, se ya miqe ya fito palour kai tsaye ya wuce gurin Dining sedai kafin ma ya qarasa ya hango shi wayam daga teburi se kujeru, yar Show gilas din kwanukan da ta qawata gurin ma an dauke bare yasa ran samun wani guntun abinci.

Dolensa ya sake fita ya siyo abincin a waje a ransa yana cewa “Dole yarinyar nan ta dawo a satin nan dan bazan iya sintirin zuwa siyen abinci ba, yana gama ci ya ahige daki yayi kwanciyarsa abinsa.

ASMA’U
Qarfe 11 na dare ina zaune akan abin sallah tun bayan da nayi sallar Isha ban tashi ba, gaba daya hankali na yayi nisa da inda nake na yi nutso a cikin kogin tunanin abubuwan da suka faru dani tun daga haduwata da Bashir har zuwa yau daya yanke alaqar da take tsakanin mu.

Tiryen tiryen komai ya ringa dawo mun lokutan da suka kasan ce masu dadi a cikin rayuwar mu da wadanda suke aka sin haka, haduwar mu ta farko da Bashir wadda har muka qulla soyayya a tsakanin mu nake tunawa.

ASMA’U ABDULLAHI TUKUR shine cikakken sunana. Baffan mu Alhaji Abdullahi haifaffen Kumo ne ta Jahar Gombe.

Yana da matan aure guda hudu Hajia Babba da Hajia Umma rana daya aka saka musu lalle se Hajia Anjim kafin ya auro Goggon mu Maryam daga qarshe.

Ita Goggon mu yar Asalin Numan ce kuma Babanta shine limamin garin a lokacin. A yanda aka gaya mana asali ba Baffan mu Goggon zata aura ba, Baffa Sama’ila Amininsa ne saurayinta wanda har an saka musu rana cikin tsautsayi a ranar da za’a daura auran ya gamu da mummunan hatsari akan hanyar su ta zuwa Numan daga Yola wanda yayi sanadiyyar tabuwar lakar bayansa dalilin da yake kwance kenan har yau yana jinya.

A lokacin su Baffan mu sun riga su isa garin, bayan da aka samu wannan mummunan labari hankalin kowa ya tashi har aka watse daga taron daurin aure seda Baffa Sama’ila ya bar wasiyyar akan Baffan mu ya auri Maryam dan beyi zaton ze tashi ba, haka kuwa akayi se kawai gani sauran matansa sukayi yazo da Maryam da suka je bikin Amininsa a matsayin kishiyarsu babu kuma wata jayayya ko tashin hankali suka karbeta tamkar yar uwa.

Zaman gidan mu zama ne me tsafta tsakanin matan guda hudu wanda suke kishi gurin kyautatawa mijinsu da qoqarin ganin ko wacce ta zama ta gaban go shi bata hanyar cutar da yar uwarta ko tashin hankali ba.

Allah ya azurta Alhaji Abdullahi ta kowanne bangare domin ya masa arziqin Dukiya, mata da kuma Yaya saboda seda ya haifi Yara 42 inda biyu suka mutu tun kafin a haife ni yanzu haka mu 40 cif muna raye Maza 24 mata 16.
Mu 8 ne a dakin mu, maza uku mata biyar.

Zan iya cewa kusan nice mafi soyuwar ya a gurin mahaifina kodan ina da sunan mahaifiyar sane amma dai kowa ya shaida nidin yar gata ce ta gaske, Baffan mu yayi matuqar qoqari gurin bamu tarbiyya tareda hada kanmu dan bamu san wani abu wai shi yan ubanci a gidan mu ba mun tashi tamkar tsintsiya baka taba banbance yan wannan daki dan kowa inda yake so yake warkajamin sa.

Dukda kasancewar Baffa beyi boko ba amma yayansa ya bamu damar yin ilimi iya yanda kaso kuma mata da mazan mu, baya tsawwalawa, dukda anayiwa mata auran wuri a lokacin sam shi babu ruwansa idan yayyen mu mata sun gama secondary school yana basu zabin aure ko makaranta wanda kika dauka shi zakiyi dan tun duniya na kwance Baffa yake fitar da yayansa mata qasashen waje suyi karatu, idan ma kuma kina karatun kika fitar da miji dukka ze miki auranki.

Nice ya ta Ashirin da bakwai a gidan mu, Ma’u kwalisa shine laqabin da akeyi mun a makaranta saboda yanda Allah yayi ni dason gayu abin ya hade mun da irin qirar halittar da nake da ita dan haka nake bawa gayu haqqinsa yanda ya kamata.

Tun muna SS1 na qudurce a raina nifa dana gama secondary aure zanyi duk kuwa da yanda nake da qoqari sosai a makaranta nidai kawai aure nake so abinda ze baku dariya shine ko saurayin bani dashi dan bana kulasu, ni a lokacin ma duk wanda yace yana sona tofa ya zama abokin gaba ta har tsokanata yan gidan mu sukeyi indai kana so muyi rigima dakai to ka nuna wani kace saurayi nane.

Ranar da muka fara haduwa da Bashir wata rana ce mun taso daga islamiyya da yamma, muna hanya wani da Ake kira Ibbah saurayine dan layin mu daya nace shi ala dole sona yake yi mun taho a hanya kawai ya tare mu.

Ibbah girman Ingila ne acan aka haife su dan basufi shekara biyar da dawowa Nigeria ba dan haka gaba daya dabi’unsa na turawa ne abinda yasa nake qara tsanarsa kenan muna tafe muna hirar mu se ganin sa kawai mukayi a gaban mu ya kalleni yana murmushi yace “Hey pretty yau na kamaki bazaki gudu ba, tsaki nayi masa na murguda baki kafin na kauce ina cewa

“Aikin banza mutum kamar maye yayi ta bin mutane, se kayi tayi ai dan wahala” nayi gaba abina se ji nayi caraf ya riqomun hannu banyi wata wata ba kuwa na kwashe shi da mari kafin na hau zazzaga masa tsiwa ina zaginsa.

Tahowar da Yaya Abubakar din gidan mu da Abokanan sa uku yasa na dakata ina hararar Ibbah dayayi mutuwar tsaye yana kallona, Yayan ne ya tambayi meya faru Alawiyya tayi caraf tace masa “Ma’uce ta Mari Ibbah saurayinta” tun kafin ta gama na juya kanta da masifa ina cewa

“Ta ina ya zama saurayina wallahi karki sake hadani dashi niba saurayina bane” kawai na saka kuka kawai se suka samun dariya dan yanda nayi abun seka rantse wani mugun abu aka jinginani dashi.

Daya daga cikin Abokan Yaya Abubakar wanda ban sanshi ba, cikin taushin murya yace mun “waya gaya miki mekyau tana yin kuka rabu dasu ba saurayin ki bane ki share hawayenki”.

Haka kawai naji ya burgeni, na saka hannuna na goge fuskata tsaf kuwa fuu nayi gaba na barsu suna ci gaba da yi mun dariyar ina jin Yaya Abubakar na bawa Ibban haquri kafin ya taso su Alawiyya a gaba suka biyo bayana.

“Ma’u danja Ma’u rigima daga ance mutum saurayinki kawai ki kama kuka ke wai baki san kin girma ba” Bala daya daga cikin Abokan nasu ya shiga taokana tun kafin ma na bude baki Yaya Aliyu da duk yafi sauran abokan su kirki ya tareshi da cewa

“Zaka fara ko Bala, Ma’u kyaleshi yi shigewar ki gida” seda n harari Bala na murguda masa baki kafin na shige dan sam bana son Balan nan saboda yana shan Taba nasha ganinsa yanayi ni ban ma san me yasa su Yaya suke kula shi ba.

Da Daddare muna zaune a palour Baffa muna hira yanda muka saba nake bashi labarin abun da ya faru
“Wani sabon abokin Yaya Abubakar ne yace na dena kuka amma su da duk se dariya ma sukeyi mun” na fada cikin shagwabar da idan ina gaban Baffana jina nakeyi kamar wata yar jaririya zuba tabara nake son raina idan akayi sa’a Goggo na kusa ta make ni.

“Banda dai tsiwa irin ta Mamana ya zaki mari mutum kawai dan yace yana sonki, ki kiyaye kar a sake kuma gobe kuje har gida dasu Alawiyya ki bawa Ibrahim din haquri kinji ko” Baffan ya fada. Sena marairai ce nace “toh Baffa bazan kuma ba.

Washe Gari Alhamis kuwa bayan mun taso boko da yamma babu Islamiyya mukaje har gidan su Ibbah na bashi haquri, da yake yana da sauqin kai yace shi harya manta ma Maman sa se nan nan take dani wai yarinya me kyau da hausarta wata iri ta hado mana kayan dadi muka tafi muna gulmarta wai su a dole turawa.
Chapter 60 · 0% Book details