← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 158

Sashe 35

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Ahmadu na zaune a tsakar gidan akan Kekensa Naziru da physiotherapist da yake dubashi suna tsaye a kansa bayan sun dorashi akan keken dan gama Exercise dinsa kenan suka shiga Addah na Masifa Amirah na kuka gaba daya suka juya suna kallonsu, wuce su Addah tayi bata ko kalli barin da suke ba itama Amiran ta rufa mata baya sallamar me Napep ce ta saka su Nazirun juyawa daga kallon su Addah.

Akwatin Amirah ya dire musu ya kalli Naziru yana cewa “yi musu magana su bani kudina na wuce dan Allah”
“Nawane kudin?” Naziru ya tambaye, bayan ya fada masa ya zaro daga aljihunsa ya bashi.

Me Napep na fita shima Physiotherapist din yayi musu sallama ya tafi dan ya gama aikinsa, kama keken Naziru yayi da niyyar maidashi dakinsa ya dakatar dashi da cewa

“Kaini daki Naziru” Alhaji Amadu ya fada dukda yaso ya zauna a tsakar gidan yasha iska amma zuwan Fatu baze barshi ba, yanzu haka yana jiyo bambaminta daga palour Dadan amma baze kula suba dama ya fada musu ai ayi dai su gani idan Tusa zata hura wuta kuma gashi da alama dai tun ba’aje ko ina ba da sun fara karbar sakamakon abinda suka aikata.

A palour Dada kuwa Addah ce take sababi kamar zata hadiye harshenta,
“Daga abin arziqi se ya zama na tsiya, yar nan naga kuma jikar kuce yanzu ta girma ace cikin yan uwanta kaf itace ba’ayiwa taron suna ba ai setace ba’a qaunarta. Ni kinga tafiyata gata nan ku qarata nima inje naji da masifar nawa mijin dan nasan su Binta munafukai sun kaimasa rahoto tun jiya” Addan ta fada tana kwasar jakarta data watsar tun shigowarsu, bata saurari Dada dake mata magana ba ta fice abinta ranta tana qissima duk abun Bashir be isa yayi a gaban Dadan ba tasan zata ta ka masa burki.

Bayan Fitar Addahne Dada ta mayar da hankalinta kan Amirah dake durqushe har sannan tana kuka,
“Amirah yanzu kina ganin biyewa Addah da kike kuna aikata duk abinda kuka ga dama daidai ne ko? Ke bazakiyi hankaliki zauna a gidan auranki lafiya ba se ki ringa biye mata kina saba umarnin mijinki to ki sani dai shi Allah babu ruwan sa, idan ya tashi ke kadai ze kama da laifin saba umarnin miji banda Addah tun wuri idan zakiyiwa kanki fada ki bi hanyar gaskiya kiyi dan nidai babu ruwana da duk wani shirginki yanzu” tana gama fadan haka ta miqe ta shige dakinta ta bar Amirah na cigaba da share hawaye.

Sosai ranta ya baci da abinda ya faru a gidan Bashir din, ta rasa meyake damun yayarta ta har ji takeyi daman itace gaba da Addah qilan da ta ringa dorata akan hanya ta dena wadannan abubuwan zubda mutunchin da take yi amma ya zatayi sedai tayi ta binta da addua kawai.

Wayar Bashir ta kira bayan ta shiga dakin, lokacin yana tsaye kan Asma’u yana zuba mata ruwan tijara kaman itace Addan ko Amirah. Yanda yake bambamin tasan ransa yakai qololuwar baci yasa bata tankashi ba ta sunkuyar dakai kawai tana jinsa saboda Bashir Miskiline, ko zeyi rashin mutunchi a ruwan sanyi yake dafa mutum. Auran Amirah nema taga yana neman ya mayar dashi mafadaci tunda yanzu yana iya bude baki yai fada idan an masa laifin sabanin da da ko laifi ta masa sedai ya dauki gaba da ita ko yayi ta gasa mata aya a hannu ta ruwan sanyi yanda ko qararsa ta kaiwa wani baza’a yarda ba dan babu shaida.

Sau biyu wayar tana qara amma be kula ba se ana ukun ya zarota da niyyar kashewa dan a lokacin bayajin ze iya magana da kowa sedai ganin suna Dada yasakashi saurin dagawa bayan ya zauna akan kujera dan Uwa ba wasa ba, a magagin mutuwa ne kadai yakejin baze iya amsa kiranta ba amma inda yaji ya kuma gani ko halin yaya ne seya amsa idan yaso ya bata uzuri ya kira daga baya.

Gaisheta yayi ta amsa tana karantar bacin rai a cikin muryarsa, kiran da tayi masa ta so ta tambayeshi ne shiya tura Amirah gida amma yanayinsa yasa ta fasa dan tasan qarshe wani laifin zata jangwalo mata yace ta kai qarar sa danhaka se tace cikin taushin murya

“Bashari idan babu abinda kakeyi kazo gida yanzu mana ina son magana da kai”

“To Dada gani nan zuwa” ya fada yana miqewa dan daman yana da niyyar zuwan a yanzun yaje ya gaya mata abinda Addah da Amiran sukayi dukda yasan ta sani amma dai gara yaje da kansa yaji ko harda sa hannunta a ciki.

“Ku shirya gobe da safe zamu wuce kuma a mota zamu tafi” ya fada yana kallon Asma’u da kanta yake a sunkuye har sannan kafin ta dago harya kai qofa, kallonsa tayi tana zare ido a fili ta furta “kan bala’i Gombe to Lagos a mota” miqewa tayi ta bi bayansa da sauri dan baza’ayi wannan gangancin da ita ba, haka siddan Allah ya rufa musu asiri ya basu yanda zasuyi subi jirgi se yace a mota zasu tafi kamar ma itace tayi masa laifin kenan aikuwa wallahi bazata sabu ba shidai ya tafi su zasu jira Moday din su tafi dan daman already sun siyi tickets ta barsu a bude saboda bata san sanda zasu tafi ba.

Ya kunna motar yana qoqarin bude get ta shige ta zauna, tana jin yanda yake kallonta a jikinta amma taqi daga kai bare su hada ido dan gara aje gaban Dadan itama ta saka baki a wannan al’amari kar goben tayi ma suzo suna wallahi tallahi. Tafiyar kamar ta kurame harsuka isa gidan Dada, ta rigashi shiga gidan dan sanda suka isa daidai ana kiran Magriba shi seya tsaya ya daura alwala ya shiga masallaci ita kuma ta shige gidan.

Amirah na zaune har sannan a palour ta dena kukan dai se ajiyar zuciya take fuskarn nan ta kumbura tayi jajir abinka da Farar fata ansha kuka. Kallon kallo sukayi da Asma’un kafin ko wacce ta dauke kanta gefe Ma’u ta nemi kujera ta zauna tana zaro wayarta daga aljihun Diguwar rigar jikinta ta danna Number qaninta dan karya mayar da yara gida ba kowa da yake suna nan Babban gida tunda safe ta kawo su.

Fitowar Dada da hijabi a hannunta da alama itama alwalar tayo ta kalli Amirah tace “au haryanzu kina zaune a qasa sanyi na shigarki da danyan jiki se ance ki tashi ko? Kiyita zama jikinki ne ai bana wani ba” ta fada tana zura hijabinta inda Abun sallarta yake ta nufa se a sannan ta ankare da Asma’un dake zaune seta sassauta fuskarta tana cewa “Aa Asma’u Yaushe kika shigo”

“Yanzu na shigo Dada ina wuni” Ma’u ta fada tana zamowa daga kan kujerar, seta amsa mata tana cewa
“Ki shiga kiyi sallah bari nima nayi gashi can har an yi raka’a daya” ta tayar da Sallah ita kuma Ma’u ta miqe ta shiga dakin Fainusa dukda ba sallar zatayi ba seta nemi gefen gado ta zauna tana duba wayarta.

Batafi minti uku ba Amirah ta shigo tana jan akwati, kallo daya tayi mata ta ci gaba da dannan wayarta ita kuma ta jingine jakar tana dafe gefan kanta dayake sara mata ga wani jiri jirin yunwa dake son kayar da ita haka ta daddafa ta shige toilet dan wanka take son tayi.

Da ruwan zafi sosai ta gasa jikinta dan yanzu base ance tayi ba tsamin jikin kadai yana sa ta shiga hankalinta ta gargasa jikin gashi taci sa’a jikinta me kyau ne tuni dinkin ya kame in banda ma kata’in da take jefa kanta aida ta fi haka warwarewa.

Sanda ta fito har sannan Ma’u na nan ta sake bararrajewa akan gado da alama waya takeyi, a darare ta ja akwatinta ta ciro duguwar riga da undies ta sake komawa toilet din ta sako kayan ta dauro alwala ta fito daidai sanda Dada ta leqo tana kiran Asma’u, bayan ta idar tana zaune ita ba lazimi ba tayi zuru akan sallayar aka bude qofar.

Dadan ce ta sake dawowa, cikin bacin rai tace mata “wai bazaki tashi kije kici abinci ba Amirah ko kin manta jego kikeyine idan kuma wani kike jira ya kawo miki se ki zauna”.

Yunwa takeji ta gaske dan haka ta miqe salaf salaf ta fito palour inda take jiyo muryar Asma’u da Naziru da alama hira suke, a tsakiyar palour ta tarar dasu, Asma’u nacin tuwo da miyar kuka shi kuma yana mata hira, wuce su tayi ta nufi kitchen tana kaiwa daidai qofar Bashir ya shigo da sallama ciki ciki ai se kawai ta qame a gurin ta kasa gaba ta kasa baya, bata so su hadu ba, a yanda ta tsara in ta shige daki bazata sake fitowa ba abincinma idan an gaji a ringa binta dashi har seya bar garin gashi yanzu tun ba’aje ko ina ba sunyi kicibus.

Shi kuwa Bashir bema lura da ita ba ya nemi guri kusada Asma’u ya zauna, Dada ce ta shigo itama daga Gurin Alhaji tan cewa Naziru yaje Alhajin na kiransa. Kallon Amirah dake tsaye kamar an dasa ta tayi tace

“Ke kuma lafiya kike tsaye kin qi gaba kinqi baya” kidan duma zuciyar Amirah ta shigayi daidai sanda ta waiwayo idanunta suka hadu dana Bashir, wani mugun kallo ya aika mata dashi daya saka hanyar cikin ta kadawa bashiri ta shige kitchen din ta fara matsar kwalla.

“Me yarinyar nan takeyi a gidan Dada oh danace ta tafi shine ta taho gidanmu saboda raini ko tam” ya fada yana sakin qwafa dagani yama rasa me zeyi kawai. Seda Dadan ta zauna tana kallonsa tace

“Dalilin kiran dana maka kenan ai nima ina zaune sukazo ita da Addah sunce kace ta tafi gida”

“Eh nace ta tafi gida Dada wannan yarinyar bata da mutunchi ta raina ni ban isa na bata umarni tabi ba se abinda ta rayawa kanta, seda na gargadeta nace baza’ayi taron sunan nan ba amma saboda ta nuna mun ban isa ba taje tayi”
Chapter 35 · 0% Book details