← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 158

Sashe 115

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai da Fata Mama da Abba suka dage se Khalil ya saki Umaimah da tunda tasha marin Abba ta durqushe bata sake dagowa ba saboda wani Azababben ciwon mara da kai da suka dirar mata lokaci daya.

“Shikenan, taje na saketa saki daya” Khalil ya fada kamar wanda ze fashe da kuka.

“Uku zaka mata ka yanke duk wata alaqa da take tsakanin ku yanzun nan” Mama ta sake fada,

“Hajiya dayan ma yayi ba se ya qara ba” Hajiyar su Khalil ta fada

“Wallahi se ya qara Hajiya ko beyi uku ba se ya mata biyu” Mama ta sake kafewa dole Khalil ya sake qarawa Umaimah da tayi mutuwar zaune jin wannan Drama da ake tsarawa.

“Durun uwar nan, ka sake ni Khalil a maimakon ka saki wannan Yar iskar daka auro? To wallahi dani da kai da ita sedai duk ayi biyu babu” Umaimah ta fada tana miqewa kafin kowa ya ankara ta finciki wani flower vase da yake kusa da ita ta saukewa Khalil a daidai Mazantakarsa, ihu daya ya kwalla ya fadi wanwar a gurin.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 52

ENGINEER BASHIR

Watanni ukun da suka shude Bashir yayi su ne cikin wata rayuwa me cike da qunci da rashin sukunin zuciya. Ya sake zama shiru shiru duk da daman shi ba me yawan magana bane amma a yanzu kana kallonsa zaka san shirun sa yana da nasa ba da tarin damuwa da yake ciki.

Abun ne ya hadar masa goma da Ashirin, kewar Ma'unsa tana neman zauta shi ga rashin kula da rashin abinci me kyau da baya samu a gidansa kullum se tashin hankali da hayaniya idan ya fita har baya so lokacin tashi aiki ya dawo gida.

Gaba daya a yanzu idan ka ganshi se ya baka tausayi yanda gaba daya ya fige ya fita hayyacinsa, hidimomi sun sako shi a gaba, wata daya da rabuwarsa da Asma'u gaba daya ya kasa gane kan cefanen gidansa.

Be taba sanin cewa Neman da Asma'u takeyi rufin asirinsa bane se ranar daya dawo daga aiki ya tarar da Amirah ta dafa masa farar shinkafa ta soya manja da yaji ta ajiye masa a ranar Azumi yayi, kuma kafin ya fita da safe ya gaya mata azumin yakeyi be shigo gida ba seda yayi sallar magriba dan haka yana shiga kan Dining ya wuce kai tsaye dan ya ci abinci.

Yana budewa yayi arba da abinda ta ajiye masa gaba daya se ya gagara bude baki ma yayi mata magana, mai da yaji a gidansa abinda rabon dako a ido ya ganta tun zamanin da yana Jami'a shine yau aka dafa masa a matsayin abin shan ruwa.

Yar gasken kuwa daya tambayeta dalili kai tsaye ta gaya masa cewar kayan miya sun qare kuma ita bata da kati a wayarta bare ta kirashi ta sanar masa shiyasa taga daya dawo bata girka komai ba tunda tana da yaji gara ko fara da mai dince tayi masa.

Yanzu shine ajiye buhun huna, shine cefane, dai da Maggi se ya siyo ya ajiye mata sannan in dai bashi ya duba ya sake siyowa ba babu ruwanta abinda yake da akwai shi zata sarrafa tayi abincin da kusan kullum Asarar sa akeyi dan yaran basa ci shi kuma bashida nutsuwa da kwnaciyar hankalin da zeci da yawa, da ya zauna cin abinci in sha Allahu seta qirqiro abinda zata bata masa rai ya tashi daga gurin.

Ya rasa wace irin macece Amirah da bata taba tashi kawo qorafi da mita se a lokacin da za'aci abinci ko lokacin kwanciya wadannan abubuwa suka taru suka sake dagula masa lissafi.

Be qara shiga uku ba seda Amirah ta fara laulayi. A iya saninsa bayan haihuwar da tayi an saka mata Implant a Asibiti saboda ta huta jikinta ya dawo daidai amma se gashi ba'a rufa shekara ba ta samu wani cikin.

Lokacin da yayi mata magana akan ya haka ta faru kai tsaye tace masa cirewa tayi sanda zata taho saboda itama tana so ta tara Yaya a dena mata gadara dasu, be ja ba ya barta tunda ai jikinta ne ta sani idan dadi taji idan ma wuya ce duk tafi kowa sani shidai tunda ta fara Amaye Amaye da wasu abubuwa ya tattarata ta koma dakinta dan wata muguwar qazanta ta farayi abin dai ba'a cewa komai.

A bangaren matsalar Ma'u kuwa yankewa kansa shawara yayi akan ze saka mata ido ne yaga iya gudun ruwanta, ze jira daga nan har shekara har zuwa sanda zata huce ta saurare shi a sannan baze sha wahalar shawo kanta ba su komawa auransu amma babu qarya yayi kewar Asma'u koma yace yana kan kewarta, fuskarta, muryarta, qamshin ta da gayunta daddadan girkinta ga murmushinta me saka shi manta kowa da komai kai wallahi dole ya maido da Asma'u rayuwarsa dan kuwa tabbas rasata babbar Asarace a gareshi.

Yanzu haka tun daya rabi da ita baya iya bacci saboda tunanin ta, idan kuwa har bacci yayi nasarar sace shi me nauyi to cike yake da mafarkin Asma'un.

Abu dayane yake dan kwnatar masa da hankali yanzu da be sake ganin wannan mutumin yazo gurinta ba, tun waccen ranar ma babu wani Namiji da ya sake gani tare da ita idan ba Yemi ba wanda ya bincika ya tabbatar abokin aikinta ne kawai babu wata alaqa a tsakaninau bayan ta aiki.

Sedai kuma  guiwar sa tana yin sanyi irin yanda yaga gaba daya ta ci gaba da rayuwarta babu wata alama da take nuna tana da damuwa ko tunawa da shi dan yanzu ko sun hadu a hanya gaisawa sukeyi kamar wasu maqota, yanda zata gaisa da sauran mutanen da suke cikin layinsu shima irin wannan gaisuwar take yi masa babu wani abu da yake nuna sun taba hada wata alaqa ta soyayya bare har aje ga batun aure amma kuma baze sare ba, zeyi ta binta a hankali har zuwa sanda ita da kanta zata sakko ta neme shi.

A ranar Lahadin yana kwance a dakinsa kamar yanda yanzu ya mayar da hakan dabi'arsa zaman daki kamar wata sabuwar Amarya. Amirah ce ta shiga dakin fuskar nan qozai qozai da ita kana ganinta kaga me yaron ciki duk ta firgice ta saka doguwar rigar bacci cotton ta daura zani akai kanta ko dankwali babu ga gashinta me laushi duk ya tashi.

Kan gadon ta nufa ta zauna daidai kansa se yayi saurin miqewa zaune ya matsa can gefe yana hade fuska, Amirah da abin ya mugun bata mata rai, bakinta cike da yawun da yake yawan taruwan mata tace

"Wai wane irin wulaqanci ne haka se kace wata kashi daga nazo kusada kai zaka tashi sannan ka dena cin abincina gaba daya mun zama kaman wasu yan haya a gidan nan kowa sabgar gabansa yake yi"

"Malama ki wuce kije kiyi wanka kuma karki sake zuwa kina mun magana da yawu a bakinki. Sannan na miki magana akan ki ringa suturta jikinki kin qi ko? Shikenan" Bashir ya fada yana miqewa ya shige bandaki ya barta tana banbamin fadab bazatayi wankan ba ai jikinta ne ba nasa ba.

Sanda ya fito bata dakin, shiryawa ya shigayi, yasan tunda ta fara wannan neman rigimar to idan ya zauna gidan dole se ta saka shi yayi hayagaga shi kuwa yanzu ciwon kan da yake fama dashi kullum ma ya ishe shi ba se ya qara wani ba.

Yana tsaye yana warming mota kamar ance ya kalli qofar gidan Ma'u yaga wasu lafiyayyun motoci guda biyu a ajiye ga Bouncers hudu majiya qarfi se fareti suke a qofar gidan.

A farko tunaninsa Alkasim ne yazo, yayan au Ma'u ne babban dan sandan farin kaya ne yasha shine me yawo da wadan nan mutanen ko a Gombe idan yana gida haka Zasuyita zagaye unguwar.

Harya shiga motarsa ze tafi ta mudubi ya hango ana fito da kwanukan abinci, cike da mamaki ya dakata ai kuwa idonsa sukayi mummunan gani da mutumin daya fi tsana a Yanzu ya fito daga gidan yana zuba murmushi kamar wanda akayiwa Albishir da Aljanna.

Be gama cika da mamaki ba seda yaga Ana ta fitowa da yara akwatuna suna dauka, yana nan tsaye suka wuce shi kamar da gayya ma har wani quuu suka taka motar suka fice da gidu Bashir ya bisu da ido zuciyarsa na tafasa saboda bacin rai.

Kashe motarsa yayi ya nufi gidan, a bakin qofa suka hadu da Aliyu daya fito fuskar nan kinini kamar wanda aka daka sukayi wa juna kallon kallo kamar wasu zakaru kafin Aliyun ya rabe shi ze wuce se yayi saurin ruqoshi yana cewa

"Waye ya fita daga gidan nan yanzu?"

"Saurayin Mami ne, Uncle Yusuf" Aliyun ya bashi amsa kai tsaye kafin ya janye hannunsa ya yayi gaba.

Seda Bashir ya dage bango kafin ya iya tsayawa da qafarsa. "Saurayin Ma'u?" Ya maimaita maganar a fili yana bin bayan Aliyu da ya tafi ya barshi da kallo.

Dagaske Ma'u ta bawa wani damar shiga rayuwarta bayan shi? Wannan irin kata'i ne yake taso masa daga qirji yana shaqe masa wuya kalamar saurayi da Aliyu ya gaya masa tayi masa zafin da gara ace wuta ya fi masa sauqi akan jin wannan mummunar maganar.

Fasa shiga gidan yayi ya juya dan tsoro yakeji, idan ya shiga ya samu tabbacin maganar da Aliyu ya gaya masa daga bakin Ma'u ya tabbatar zuciyarsa kawai bugawa zatayi a take ya mutu dan baze iya dauka.

Yana dafe da qirjinsa dakyar ya iya kwasar qafarsa ya koma jikin motarsa yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudun 10KM. Gaba daya jinsa yake shi ba a sama ba ba a qasa ba, qafafunsa kansu rawa sukeyi beyi aune ba se ganinsa yayi dirshen ya zauna akan kwaltar da take qofar gidan kawai se ya mayar da kansa ya hade da guiwa yana jan numfashi.

"Lafiya Engineer kake zaune a qasa meya faru?"yaji muryar da be tantance ko ta waye akan sa ba, dakyar ya dago yana nuna masa kansa da qirjinsa daga nan be sake sanin abinda ya faru ba se farkawa yayi ya ganshi kwance a gadon Asibiti.
Chapter 115 · 0% Book details