← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 158

Sashe 92

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin da yayi wa Ma’u y sake hasalashi, tayi qara fari tayi kyau abinta a yanda ta fitan nan babu me mata kallo matar aure ma bare har a hasaso mata yaya shida dole itama yaja mata kunne gaskiya tunda dai haryanzu ai da auransa akanta. Haka ya wuni ranar a gurin aiki cikin quncin dashi kamsa be san na menene ba, sanda ya tashi ya tsaya ya siyi fruits da kaza kafin ya wuce gida.

ASMA’U
Hankali kwance na ringa tuqina harna isa ma’aikatar mu, muka gaisa da abokanan aikina cikin mutun taka suna yimun sannun rashin lafiyar danayi qaryarta har na zauna ranar aka bani tukuicin saki nidai se yaqe nake ina amsa musu dan a yanzu bana son wani abu da ze ringa tunamun da wancan Al’amari.

Se da muka fita break din rana Olivia wata abokiyar aikina ta same ni ina cin abincin da se a sannan na samu na siya.

Cikin harshen turanci take cewa
“Asma’u Juliet tana gaya mun wata magana ranar amma ban yarda ba wai dagaske ne kun rabu da me gidanki baku tare yanzu?”

Sak nayi ina kalllon Olivia, daman Olivia irin mutanen nan ce maso shegen gulmar bala’i duk wani abu na ma’aikatar nan kaji shi a bakinta ka rasa ta inda ma take samun labarai akan mutane kuma idan taji daman ka qaddara kamar anyi yekuwa ne dan kowaanne ma’aikaci se labarin nan ya isar masa.

Dagaske yanzu dai mutane sun dena kiwon akuya sun koma mutum tabbas, Juliet din da take magana qawarta ce ni kuma a estate dinmu take budurwar wani abokin aikin su Bashir ce a gidan sa take da zama bama fa layin mu daya ba suna can qasan mune amma ace har labari ya kai musu ashe dai ba a arewa kadai mata suka iya gulma da sa ido ba harda suma a nan kudu.

Bude baki nayi da niyyar bata amsa Maman Islaha qawata ta gurin aiki ta qaraso wurin, cikin fada fada tace da Olivia din

“Wannan wane irin rainin wayo ne zaki ajiyeta kina mata wannan tambayar ina ruwanki da auranta da kike tambaya akai ita wadda ta baki labarin meya hana ki tsayawa kiji inganjinsa a gurinta? Dallah malama bar gurin nan tunda baki da aiki se soka baki a rayuwar mutane da shegiyar gulma kawai” sosai ta balbaleta da fada dan Maman Islaha irin yarabawan nan ne da basa daga qafa.

Olivia kuwa simi simi ta bar gurin tana waiwayena, mayar da kai nayi ina juya abincin dan gaba daya ya fita a raina Maman Islaha ta dafa ni tana cewa

“Ki manta da ita kici abincinki ni wallahi mamaki kika bani ma da baki dauke ta da mari ba ace kina zaune tazo tana miki irin wannan maganar se kace ubanta ne ya kashe miki auran, idan kuma mijinki take so tun wuri se ki san me ake ciki...” seta dakata ganin ina hawayen da ni kaina bansan sanda suka fara zuba ba.

“Maman Faridah lafiya meya faru?” Ta fada a rude tana ruqoni, sena saki kukan gaba daya ina cewa

“Yanzu dan aurena ya mutu shikenan har na zama abin gulma ana yayatani a duniya kenan?”

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un auranki ya mutu Maman Faridah dagaske? yaushe? Kardai yarinyar nan son mijinki takeyi din da gaske kiyi mun magana” ta jero mun tambayar daga ganinta kasan hankalin ta ya tashi da jin maganata.

Seda na tsagaita kukan dan har hankalin masu cin abinci ya fara dawowa kanmu kafin nayi mata bayanin komai cikin sanyi tun kafin na kai qarshe ta qundumo wata ashar me maiqo da yarbaci ta aunawa Bashir ta qara lailayo wata ta watsa mun kafin cikin fushi tace mun

“Amma kin bani mamaki Maman Faridah yo se me shi ya tafka asara fa ba ke ba dan wallahi harya mutu baze taba maida kamar ki ba shine har zaki tsaya kina kuka wani ana yayata ki a duniya an dade ba’a fada ba tunda ba kanki faru ba sakin aure har a sakeki akan kishiya kintaya kina wani zubda hawaye mtsw,

Kansa ya cuta in sha Allahu se kin samu me sonki wanda yasan darajar ki kuma akan idonsa zega yanda za’a ringa tarairayarki sedai ya hadiyi zuciya ya mutu, Allah ya kaimu ki gana iddah ni kaina ina da Candidates se wanda kika zaba kika darje”.

Haka Maman Islaha taci gaba da gaya mun maganganu da suka sake bani kwarin guiwar yakice Bashir daga rayuwata, har tana ce mun se na chanza shiga tunda yanzu bani da aure na dena zumbula wadannan Dogayen rigunan da suke boye dirina se nayi dariya nace mata

“Maman Islaha ko da aure ko babu dole in rufe jikina in kare mutunchin kaina, bafa yarinya ce ni ba sannan ga yara ina dasu nan da kika ganni ma babu lissafin sake aure a gabana zan ci gaba kawai da neman kudina na kula da yarana shikenan”.

A ranar bamu tashi da wuri ba saboda mitin din gaggawa da mukayi, abin takaici ina zuwa na kunna motata taqi tashi bayan nasan lafiya qalau take ba’a ko yi sati uku ba da a ka kaita a dubata a sannan dinma ba abinda ya sameta shine yanzu zata mun halin qarfen nasara.

Ina tsaye ina ta faman zabga tsaki, David daya daga cikin yaran da suke kula da gurin pakin ya qaraso yana tambayata lafiya nagaya masa abinda ya faru shine ya bude gaban motar yana duddubawa duk ya gama yan dabarunsa amma taqi tashi, haka na kwashe kayana daga ciki na kulleta, ga Magriba tayi gashi duk yan arear mu sun wuce haka dai na kira uber dukda bana son hawa da daddare.

Ina tsaye a daga can gaban get ina jiran me uber wata dalleliyar mota Marsandi qirar shekarar da muke ciki baqa wuluk se qyalli ta wuceni, da ido na bita a raina ina yaba motar aga quginta kadai zaka san ba qaramar mota bace a raina nace

“Allah kayi mana arziqi muci me kyau mu saka me kyau mu hau mota me kyau” ina cikin haka se ganin motar nayi tana dawowa da baya. Matsawa nayi daga inda nake ina waiwaya wa bayana dan naga tazarar gurij da cikin ma’aikatar mu idan ta kama da abin gudu in fece kar inje masu satar mutane ne se gani nayi motar ta sake biyo ni ai kuwa na daga qafa na fara sauri, sunana danaji na ciki ya ambata ya saka na juya da sauri na kalle shi.

“Asma’u” ya sake ambata yana kallona, nima kallonsa nakeyi ina so na tuna ko na sanshi amma banga alamar hakan ba.

Baqi ne amma ba irin wukuk din nan ba fatarsa a goge take alamar hutu da jin dadi sun ratsata a kallo daya zaka tabbatar da kyakykyawa ne irin kyau na maza me cike da kamala. A zaunen da yake na tabbatar da dogone irinsu Bashir sannan yana da cikar halitta bashida qiba amma jikinsa a murde yake alamar yana daga qarfe daga damtsen hannunsa da yake a bude ma zaka tabbatar da hakan.

Gaba daya a abinda be wuce second talatin ba na qare masa kallon, nayi guntun tsaki dan ban gano wata alama da take nuna na taba sanin ko me kama dashi ba a rayuwa qila irin samarin nan ne ya canki suna akayi sa’a ya fada daidai se kawai na juya na fara tafiya a raina ina mitar abinda ya tsayar da me Uber kusan minti talatin shiru bayan a map naga yana dab da inda nake. Maganar da saurayin ya sakeyi ce ta sakani juyawa a sukwane ina kallonsa

“Ma’u danja wutar baya Ma’un lelen Baffanta” ya fada yana sakin wani murmushi daya saka gabana yankewa ya fadi.

“Yusuf” na fadi sunan a rarrabe ina qare masa kallo dan ya fito daga cikin motar ya jingina shima yana kallona. Murmushinsa me kyau ya sake yi mun kafin yace

“Har kin tuna ni kenan da yake kinji kirarin naki ko, daman na fada miki ko kin manta fuskata a rayuwa na barmiki abinda bazaki taba mantawa ba gashi kuwa ina fada har kin gano ni, me kikeyi a gurin nan ga duhu ya yi haka?”

Jinsa kawai nakeyi ina kuma qare masa kallo dason tabbatar da dagaske Yusuf din ne dai ko kuwa wani ne daya san tsokanar da yakeyi mun ada, se kuma dana nutsu na gane shidin ne amma canjin daya samu a rayuwa tabbas ya zarta ace ka gane shi a kallo daya yanda kasan wanda aka saka a inji akayi masa qare qaren abubuwa, Babban abinda yafi bani mamaki ma yarintar da ke tattare dashi.

A sanda nasan Yusuf ma a qallah ya haura shekara talatin kenan yanzu yana hararo hamsin ne amma nake ganinsa kamar yanzu ne yake talatin din da yan kai.

“Ki dena kallona haka karna komawa matata a rabi ina tambayarki me kikeyi a nan baki amsa ba” ya sake fada cikin sigar tsokana ya baro jikij motar zuwa inda nake tsaye, se naji kunya na sunkuyar da kai ya gane kallon qurillar da nake masa.

Ma’aikatar mu na nuna masa ina cewa “Daga gurin aiki nake motata ta lalace tana ciki shine na fito ina jiran Uber da nayi order”.

“Anan kike aiki Masha Allah Ma’u shiyasa mana seda nayi dagaske na iya gano ki, idan ba damuwa muje sena ajiye ki shiga motar haya da daren nan babu dadi.

Ban musa masa ba, muka qarasa ya bude mun gaban motar wani sanyi da qamshi suka bugoni har seda na lumshe ido ina shiga naji na wani lume a cikin kujera kai jama’a kudi dai yayi a rayuwa.

“Wace unguwa mukayi” ya fada yana kallona, se na gaya masa ya kunna motar muka fara tafiya shiru, Yusuf ne ya katse mana shiruj yana cewa

“Yaushe kuka dawo lagos da zama nasan dai a Gombe kikayi aure koh?”

“Eh Gombe nake bamufi shekara shida da dawowa nan din ba ai bayan daya samu chanjin aiki” na fada ba tareda na kalle shi ba.
Chapter 92 · 0% Book details