Sashe 9
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Adda ta kallemu lokaci daya zuciyarta ta aminta wannan ne mijin Hasiya wad'anda ta aura daga Farko suna cikin Kaddaranta ne.
Cike da kwarin gwiwa tace"Hasiya ki yi hakuri da mijinki ki yi masa biyayya iya karfin ki, ki zauna da shi ki lallaba yanayin da ku ke ciki. Ina miki Fatan samun ingatttaciyar Rayuwar da mahaifiyarki ta ke miki Fata ina kuma rokon Allah ya barki a gidan auran ki sai mutuwa."
Kaina na kasa ban yi mgana ba ina ta wasa da hannuna acikin Hijabina.
Inna talatu ce ta jaddamin na yi addu'a kafin na shiga dakina.
Da kaina na amsa musu Ramatu da su Adda na ta daga mana hannu muka bar kofar gidan Adda Fati.
Tunda muka dauki hanya ba wanda ya yi mgana Tahir ne aka kira a waya ya yi mgana sai da ya gama sannan ya juya ya na kallon Sadiq da ke zaune gefe daya hankalinsa na wajen kallon Hanya nima ina gefe a rabuke.
Karamin tsaki yaja bai yi mgana ba shi ya rika yi ma mai adaidaitan kwatance har gidan.
Daman Ramatu ta sakamin key din gidan a hannuna muna sauka na mikama Sadiq yasa ka hannu ya karba"
SShaf mun manta da kaya sai da mai adaidaitan yace ga kaya sannan ya sauke mana.
Ban tsaya jiran komai ba na sunkunci babban akawatin Tahir shi ya yi gaba ya na bud'e gidan.
Sadiq ya kalleni cikin Duhun anguwan ammh hasken Fatata ta Haske masa fuskarsa.
Cikin sanyinsa ya mika hannu ya Dauki karamin akwatin Lokaci daya ya na fad'in"bani akwatin ta yi miki girma."
A hankali ya fad'a wanda ina da tabbacin Tahir bai jisa ba.
Ba musu na mika masa ya dauka daidai Lokacin da Tahir ya Bude get din gidan
Tahir na gaba ina bin bayansa shi kuma Assadiq na bayanmu.
Wannan karon ma Tahir ne ya Bud'e dakin sai da ya dawo daga baya ni na fara shiga da kafar dama tare da Bismillah.
Sannan Sadiq yabi yo bayana Tahir dai a waje ya tsaya bai shigo ba.
Kamar anguwan ba wuta dakin ya yi duhu sai da ya sauke kayan hannunshi sannan ya yi amfani da Fitilar wayarsa ya haska mana Dakin.
Saman kujeruna tun na auran Abubakar na zauna saboda sai naji duk na gaji.
Sadiq yasan Tahir na jiransa bai Tsaya kallon Dakin ba yace"Zan tafi sai zuwa gobe ko?
Ai sai na ware ido ina kallonsa ina kuma ya ke nufin zai tafi ya barni a wannan gidan ni kadai ko'ina Duhu ga shi bani da waya ballatana Fitilar hannu.
Bai ga razanan da na yi ba ne yasa ya jiya zai fice ya na fad'in"Gobe zan zo in sha Allahu."
Ai bai gama fita ba nayi saurin biyo bayansa bai ankara ba sai ji ya yi kirjina ya bangaji bayansa.
Lokaci d'aya na rirrike masa sagalen hannunsa ina fad'in"Don Allah kada ka tafi ka barni, Ina. Ina jin tsoro bazan iya kwana ni kad'ai ba."
Da dan hasken Fitilar wayarsa ya ke kallon Fuskata, ko'ina na jikinsa na wani amsawa da yadda Hasiya ta rikeshi gam ta na rawan jiki.
*Janafty*
*TMWB2K004*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj
Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641
Da sauri ya matsa baya saboda kaucema rikon da Hasiya ta yi masa.
Cikin yanayinsa yace"Me zai same ki?
Ba komai kada ki damu"
Nayi kwalkwal da ido cikin bayyana tsoro na nace"Wlh ina jin tsoro."
Sai ya yi tsaye kawai ya na kallon Fuskata ta cikin duhun dakin
Tunanin mafita ya ke yi mganar gaskiya bazata iya kwana ita kad'ai ba shima da fari ya yi tunanin haka.
Kuma zaman shi tare da ita baya cikin Tsarinsa.
Gyaran murya ya yi kafin yace"Kin ga ne? Gobe zan zo yau din ma saboda ina da wani uzuri ne yasa bazan kwana anan ba."
Kai tsaye nace"To ka tafi da ni in da zaka kwana don Allah."
Sadiq ya ware ido ya na kallon Hasiya ya na shirin mgana yaji muryan Tahir daga waje na fad'in"Kasan fa mai adaidaita na jiran mu a waje. Ga shi dare ya yi."
Jin haka yasa batare da ya yi magana ya kama hanya zai fice ina ganin haka na yi zaraf na bi bayanshi.
Ya na fita sai yaji ni a bayansa Tahir ko kallon mu ya yi cikin mamaki kafin ya samu zarafin mgana Sadiq ya juya ya na kallona.
Cikin sanyin murya yace"Ba tafiya zan yi ba"
Jikina na rawa nace"Don Allah kada ku tafi barni a gidan nan ni kada'i. Bazan iya zama ba ina jin tsoro."
Na fad'a ina kara kallon wagegen gidan na saba da kwana a daki falle daya tare da Amma da Habiba.
Sannan na saba rayuwa cikin mutane bazan iya kwana a gidan ni kad'ai ba.
Tahir da Sadiq suka kalli juna kafin Sadiq ya sauke numfashi cikin sigan lallashi yace"Kinga Hasiya koma ciki magana zan yi da Tahir."
Sai naji kamar ban yarda da shi ba.
Kada na shiga ciki kuma su tafi su barni na shiga uku.
Kif kif ta idanuwana na rika yi na kasa shiga ciki kamar yadda yace.
Ganin haka yasa Tahir yaja Hannunsa suka koma daga bakin get din ina hangensu.
Sai na samu salama ganin ba tafiyar za su yi ba.
Ammh na kasa komawa cikin dakin tunda akwai Duhu ko Tafin hannunka baka iya gani.
Suna dagachan nesa da ya ke kuma ban kasa kunnuwana ba shiyasa ban jiyo mganganun na su ba.
Kuma dai sun yi kasa da murya kamar wasu munafukai.
Cikin rage sautin murya Tahir yace"Me ye wannan zabiyar matar ta ka ta ke nufi? Bazata iya kwana ita kada'i ba to so ta ke ka taya ta kwanan kenan?
Sadiq ya yi shuru ya na wani nazari akwai hakkin kula da komai na Hasiya a kanshi yanzu aurensa sunan shi aure ko da wani Tunani a ka yi sa.
In ya barta a cikin gidan nan wani abu ya sameta me zai ce ma mahaifiyarta da yan'uwanta?
Har a wajen Ubangiji ma ba shi da abunda zai kare kansa hakkinta zai kamashi.
Shiyasa ya kalli Tahir kafin yace"Tahir ba ni da mafita. kaga dai yanayin anguwan nan sannan ita kadai ce kuma macece akwai hatsari mu tafi mu barta ita kad'ai"
Tahir ya dage hanci kafin yace"I see. to yanzu me ka ke so a yi?
Sadiq yace"Zan tsaya na kwana kai ka tafi sai mu had'u gobe in Allah ya kaimu."
Tahir ya kalli Sadiq a cikin Duhu baya ganinsa sosai ammh ya na ganin Duhun Fuskarsa.
Cikin mamaki yace"Kace me? nan zaka kwana tare da wannan yarinyar?
Tahir ya fad'a ya na nuno Hasiya.
Da Dauri Sadiq ya rike hannunsa ya na fad'in"Ka yi a hankali mana. So ka ke taji abunda mu ke fad'a?
Ya fad'a ya na juyawa ya na kallona sai dai bai fahimci ko naji ko ban ji ba tunda a lokacin Tahir ya daga Sautinsa.
Ni kuma ban ji su ba, na ga dai kamar an nuna ni tunda akwai hasken farin wata da ya raba tsakiya da kwata shiyasa sai duhu ya mamaye hasken farin watan.
Tahir ya rausayar da Murya kafin yace"ammh kasan kwana a tare da yarinyar nan baka saka shi cikin Tsari ba ko?
Sadiq yace"Na sani ba shi cikin Tsarin mu. Ya zama dole ne shiyasa ammh ai daga yau ne zan san abunda zan fad'a mata da zai saka na yi nesa da kwana tare da ita."
Tahir ya yi shuru kamar bazai yi mgana ba. Ganin haka yasa Sadiq ya dafa kafad'ansa ya na fad'in"Da gaske na ke yi maka bazan bari a samu wata matsala ba."
Tahir ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Shikenan bari na tafi."
Sadiq yace"Ok sai da safe kenan?
Tahir ya kallesa kafin yace"Abubakar."
Cikin mamaki Sadiq yace"Na'am Attahir."
Tahir ya had'a hannayensa ya na fad'in"ban da Kusanta, Ban da kusanta Abubakar."
Sadiq ya yi saurin cewa"Kusanta?
Cikin Sigar tambaya.
Tahir yace"Eh kusanta nace kada ta ribace ka tab'ata kasan an ce in namiji da mace su ka keb'e su kadai to shed'an ne a tsakanin su."
Sadiq sai a lokacin ya fahimci in da Tahir ya dosa baki ya hangame kafin ya rike Haba yace"Haba mana Tahir. Me yasa zaka yi irin wannan Tunanin fisabillahi?
Tahir yace"Dole na yi tunda komai naka ya na zuwa ne batare da sanar da ni ba gwara na ja maka kunni yin haka tamkar ka fallasa sirrin da ka ke son Rufewa ne."
Sadiq yace"Na sani ni har ga Allah saboda taimako na auri Hasiya ba domin wani abu daga jikinta ya na Burgeni ko ni sha'awa ba.
Ba bu wannan tunanin kwata kwata a raina."
Tahir yace"Uhm!
Irin ban yarda ba jin haka yasa Sadiq yace"Ko zaka zo mu kwana tare ne sai ka cire shakku a kaina?
Tahir ya juya ya na fad'in"A dakin mata da mijin ne zan kwana?
Sadiq ya yi dariya har sai da tayi sauti.
Shi ya raka Tahir har kofar gida ya na daga jikin Gate din ya shiga adaidaitan suka wuce.
Sannan ya dawo cikin gida da kansa ya sakama get d'in sakata.