Sashe 66
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ba musu ya matso domin ko karyawa bai yi ba, mahaukaciyar yunwa ya ke ji.
Ya fara cin abincin kenan ta zuba masa ruwa a wani karamin kofin Tangaran ta na Shirin mikewa ya kalleta da Sauri ya na fad'in"Abba fa? Ban gansa ba?
Cikin yanayin maganarta tace"Abba ya fita Tun Safe."
Kai ya jinjina kafin yace"To miye na taro Biyu? Ba gobe ne Daurin auran ba?
Mirmishi ta yi kafin tace"Yaya Sadiq Ya Mubarak fa yace an ana gama Daura aure za'a tafi da Anty Salima"
Sai da ya Cinye abincin bakinsa sannan yace" shine daidai ammh wannan taron duk shirme ne."
Ita dai sai mirmishi ta ke yi baya so ta tafi Saboda kwaliyarta ta yi masa kyau.
Sai ya fara hasaso irin kwaliyar a Fuskar Siya di'nsa.
Har baisan sadda mganar zucci ya Fito Fili ba yace"Wow Beatufull."
Saboda har ya hango kyan da Siya zata yi in da itace ta yi wannan kwaliyar.
Sultana ko ta zata da ita ya ke ta Rufe fuska da tafukan hannayenta ta na Fadin"Thanks Yaya Sadiq."
Sai a lokacin ya fahimci aikin da ya yi sai bai karyata kansa ba ya kalleta ya na fadin"kin yi kyau ya zama dole Abubakar ya biya tukwaicin wannan adon."
Sai jin dad'i ta ke yi ta na masa wani Fari da ido lokaci daya ta na yarfa Hannu.
Bai sallameta ba har ya gama cin abinci sai janta da Hira ya ke yi , anan kuma wajen ya tura mata 5k ta acct dinta yace Tukwaicin gayun da ta yi Sultana zuciyarta kamar Farar Takarda Saboda Haske.
Ba ta bar Falon ba sai da Siyama ta kira wayarsa ya na Dauka bayan sun gaisa tace masa Sultana tazo yan makarantarsu zasu tafi.
Dalilin da yasa ya sallameta kenan, ta koma cikin gida shi kuma saboda mata sun yi yawa bai ko yarda ya Fita ba sai chan da yamma da baki suka fara Raguwa yan gari.
Sannan ya sake wanka ya saka Shadda mai Ruwan kasa, kayan da zasu saka Gobe Farare ne Tahir ne ya matsa masa shi ya Tura ma kudi ya siya musu shaddar tunda yace yasan inda zai kai musu d'inki.
Sannan Abba ma ya dinka musu su biyu, sannan ya dinkamusu har da su Baba Sammani, da sauran yayen su maza matasa har da Baban Sultana Mallam Datti.
Sai Dare Abba ya Dawo gidan a masallaci suka had'u da Sadiq sai bayan sallar Isha'i suka baro masallacin zuwa cikin gida.
Sai lokacin sauran yan'uwansa suka gansa Shashen Innani ya fara Shiga gaida Mutanen Shinkafi.
Da ya ga Innani sai da ya yi Dariya har ya na Rike ciki.
Ga uban Gwagwaro da ta maka a kanta ga gilashi, sai kuma wani Uban mayafi mai kauri mai kama da Bargo da ta yafa sannan ga wata jaka kamar ta wamzamai tace na Tara kudin Biki ne ai ba'a zo a tafi haka ba kuma Hidimar nan dai Sulaimanu ya yi ba Suwaiba da Danginsa ba ahto gwara dai a rika yi ana Tausayama Sulaimanu.
Abba na gayamasa maganar gwagwaro Innani sai da tace in ba'a nad'o mata ba sai ran kowa ya baci sannan Dakyar ya hanata Dauko masu Kidan kwarya ammh tace bikin Sulsana da Magajin gida taga Uban da zai hana makid'a shigowa gidan nan
Abba ba ya son Bid'a su ma walima kad'ai Amarya da kawayenta tare da yan'uwanta suka yi.
A daram Sadiq har shashen Mama ya shiga ya yi mata Allah ya sanya alheri yan'uwanta suka fara zolayansa da Ango gaba tuna shima na shi kamar Gobe ne shi dai baya mgana sai dai ya yi mirmishi.
Shaahen Umma ne yaji daman bai Shiga ba cike da yan'uwansa mata da kawayen Amarya da su Sultana.
Ya na shigowa suka Dau Ihu suna Fadin"Ga angon Sultana Fari mai farin Aniya."
Duk yadda yaso ya zille suka hanasa suka Takura masa sai sun yi Hotuna haka ya tsaya suka yi ta Daukan junansu har da Amarya Salima da ta sha kyau kamar ba ita ba.
Daga karshe Sajida tace"Ku matsa ku bama Magajij gida waje shi da Amarya su sha Hoto."
Hararanta ya yi bai samu zarafin mgana ba suka Turo Sultana gefensa suna Daukansu Hotuna suna Dariya.
Sajida har wani Had'a jikinsu ta ke waje daya ya make hannunta ya na fadin"Sajida."
Dariya ta yi masa har da gwallo sai ya rasa yadda zai yi da ita.
Karshe dai har rike kugun sultana sai da suka saka ya yi da ya gaji ne ya hade rai yace"Kai nagaji."
Surraya tace"Bakomai akwai na gobe mai Hoto na nan zuwa."
Shi dai sulalewa ya yi ya gudu sai a bangaren Abba yaga Umma suka gaisa Hidima ta yi musu yawa.
Sai da Safe ya samu zuwa ya gaisa da Iyayen Sultana wato Matan Mallam Shitu kenan.
Rana bata karya sai dai Uwar Diya taji kunya karfe Sha biyu da Rabi na rana aka Daura auran Salima Sulaiman Abubakar Shinkafi da angonta Mubarak Jibril Mamman.
Akan Sadaki mai Daraja.
A masallacin kusa da su In da Abba ke sallah aka Daura auran.
Daurin auran da ya sami Hallatan manyan baki kama daga abokan kasuwancin Abba yan anguwa, Mutanen Shinkafi dangin Umma da Mama Mazajen ya'yansa da Sauran su
Sai Tawagan Ango daga Kaduna suma gayya Guda bayan Tawagan Uban ango shima sai wanda dai ya gani.
Sadiq daman Shigar Farare suka yi shida Tahir da sai ana gabda ma Daurin auren ya iso garin Sadiq na mamakin Tahir komai yace ba shi da Lokaci kamar majalisan Dinkin Duniya.
Daga nan reception din da Abba ya shirya suka je suka yi, Dagachan angwaye suka rigasu dawowa saboda Daukan Hotuna da Had'a Hadan Tafiya da Amarya.
Hayaniyar gidan ta ishi Sadiq shiyasa yace ma Tahir su zauna a Restaurant din nan su Huta.
Ga shi ya na son Kiran siya ba Dama, Tun jiya da suka yi mgana ta gayamasa sun sauka lafiya.
Basu baro Wajen ba sai da Abba ya kirasa yace yazo gidan yan'uwansa na nemansa za'a tafi da Amarya.
Koda ya zo duk suna haraban gidan ga Motoci ne birjit na tafiya kaduna.
Hotuna suka yi har da su Umma da Abba da Mama da su Baba Sammani.
Har da su Goggo Husai.
Su Mallam shitu da wasu sauran jama'an ana gama Daurin aure kamar Mota Biyu suka koma Shinkafi.
Salima ta sha kuka daman Nasiha tuni Abba sun yi mata sauran yan'uwanta ma ba'a bar su a baya ba.
Da har ance a kaita bangaren Innani sai aka ji ta na masifan a fitar mata daga Shashenta zata kulle ne kaduna garin gwamma zata je kai amarya.
Kuma wlh duk sai da aka fita ta saka wata yarinya kanwar Sultana ta saka mata kwad'o a kofar falonta.
Kuma saboda matam baban Sultanan ne yasa tace zata rufe shashenta.
Tunda suka zo Bikin nan Innani ke bala'i ta na Habaicin wani Hisabin dai sai a lahira.
Sai gata da jakarta Tun na saudiya nan, ta cikata da kaya ta ci Atamfarta ta yinin biki zanin nan a kauri ga uban Daurin da ta Guma a kanta ga gilashi ta na tafiya ta na Dingisa sanda.
Ba wanda bai yi Dariya ba a yi mgana kuma tafara tsine tsine.
Abba da su Umma sun yi sun yi Innani ta yi zamanta kai Amarya tace Uban kuturu ya yi kad'an sai taje gwara taje ta saka ido Bikin jikarta ne.
Sadiq da aka so ya yi mgana wannan karon bai yi ba da kansa ma ya saka Innani a motar amarya yace ta je ta Raka Salima dakinta.
Umma zata yi magana ya kalli su Sakeena ya na fadin"Ku kula da ita in kun isa chan."
Sai kowa ya gyada kai Innani ko sai lekowa ta glass ta ke ta na kwararama Sadiq addu'a.
Daga Siyama, Sultana sai kawayen salima guda biyu a dakin Umma kuma Sadiya da sa'adatu Sai Sajida, Dakin Mama kuma Sakeena da Saliha da Shahida Sai Umma sai Kanwar Mama sai Goggo Husai da matar Baba Sammani, sai matar Baban Sultana da Innani bata ga shigar ta Mota ba da tace tace in taje Allah ya tsine mata.
Sa'ima da Surayya da Suba'atu sai gobe zasu taho da sauran mutane da wasu kayan.
Karfe Biyu da wani abu na Rana Motocin Amare suka Dauki Hanyar kaduna.
Daman Alhaji jibril tun daga Wajen Reception suka wuce.
Suna tafiya ba Dadewa Tahir yace zai tafi sadiq bai damu ba yace a sauka lafiya.
Shima bai ma san tafiyarsa ba bangaransa ya koma ya na kiran wayar siya ammh bata Dauka ba, sai ya yi Tunanin kila ta na cikin Hayaniya ne
******