← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 75

Sashe 7

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan mijinta Nura ya aikomin da Dubu talatin ban rikesu a hannuna ba na mikama su Adda da su suka yi amfani suka siyamin less da material sai Hijabai da takalmi sai dan kunne, tunda kayan nawa duk sun ji jiki.
Salisu bai yi min kaya ba daman da Niyar in muka yi aure zamu je kano da ni da shi na zabi kayan da na ke so.
Bansan ko shi Sadiq din ne ya saka musu rana ba naji suna fad'in Ranar jumma'a za su yi bikin Tariyar nawa ni har mamaki na ke yi su har wani Tunanin yin biki suke a auran da ba su da kyakyawan tabbaci a kan shi.
Inna Talatu ita ta zame mana uwa a lokacin Tunda ba Amma Adda kuma bata zo ba tukunna.
Adda Fati ta kira Baaba Ta lagos suka yi mgana sai tace Baba tanko ya yi mata mganar an d'auramin aure.
Sai kame kame ta ke yi ta na fad'in ta jima bata zo garin ba ne ammh in ta zo zata zo su gaisa da Amma, nan ne ma Adda Fati ke sanar da ita komawar Amma wajen Adda Sai kunya duk ta kama Baaba ta kasa mgana.
to gwara ita ta na yi mana sako in muka kirata mukace ga wani abu ya taso.
Ba wai mganar sako ba dukkansu suna da karfin da bayan rasuwar Baba zasu duba bayanmu ammh ina ba su yi ba wasu ma cikin su sukan manta damu gabadaya.
Irin su Baba Jibril na kaduna shi kila in na ganshi sai naga kamarsa ne da Dangin Babammu kila na ganeshi ammh daga matansa har ya'yansa ban ko san ko d'aya bani da masaniya ko su Adda sun san su barin ma Adda Fati da tafi mu bin su da son zumumci da su.
Goggon kona fa ta na kusa ita da Baba Tanko ammh har ina manta rabon da na gansu da idanuwana ballatana iyalansa har gwara Baba Saminu ya na zuwa duba Amma duk da ba na duban da ya kamata ba ne na zuwa da ganin ya muka kare ne kuma ya gama mganganunsa ya shuru takalminsa ya kara gaba ko sisi bazai iya taimaka mana da shi ba.
Adda Fati da kanta taje gidan Baba Tanko ta kai masa minti bikin Tariyar da ita da Adda Rukayya da Ramatu suka had'a hannu za su yi taron bikin.
Sannan taje har gidan Goggon kona itama ta kaimata ita sai ta fara fad'an Laifin Amma ce itace ta yanke zumumci da su sai anan ma ne Adda ke Sanar da ita Amma bata garin nan ta koma Wajen Adda da zama gabadaya.
Ni in da duk sun yi shawara da ni baza su yi min wannan gayyar ba. gayyar da bata da wani amfani illah ma daga baya ta zame min Tozarci.
Har yan gidanmu da muka taso Adda Fati ta aika Habiba ta kai musu suna ta murna daman sun rasa ina zasu samu cikon Labarin.
Habiba tace ta na zuwa suka Rufeta da Tambayoyin ina angon? Ya na nan lafiya? Sun gama Ammana aure na ba Alheri ba ne ni kaina tun ina sauraran jin ta ina kuma wannan karon kaddaran zata kwankwansamin ammh har lokacin ya gabato ban ji wata mgana sabanin shirin da suke yi ba.
Ranar laraba suka je suka yi min jere sai dare suka dawo Ramatu ce ta isheni da Labarin kyan gidan kai Tsaye na kalleta kafin nace"Me kyan gidan zai kare min acikin rayuwata Ramatu? Haka gidan Abubukar ma kuka ce ya na da kyau na Salisu ma ammh kuma karshen mai ya faru?
Sai ta kasa mgana ni kuma har cikin zuciyata na kalleta nace"To shima haka wannan zai kare a banza. Shiyasa ki ka ga ban tusa kaina ba nayi baya ina ta kallon ku Uhm.! Ku nafi Tsausayi saboda halin da zaku shiga in kuka ga kun kaini cike da Fata na sake dawo muku a karo na uku."
Sai Ramatu ta kasa magana kawai sai ta tsaya ta na kallona cikin mutuwar jiki.
Tayi kokarin kalaman bakinta su yi tasiri sai na dakatar da ita cikin mirnishi nace"Ramatu wannan karon kalaman ki baza su iya tasiri a gareni ba, me jiya ya yi ballatana yau?
Ba bu abunda ya sauya ko da yaushe abu d'aya ya ke faruwa.'
Tunda na fad'amata haka sai bakinta ya mutu ammh duk da haka sai da tamin mganar Kitso da kunshi Tsaraban Harara ta samu.
Sai dai ban tsira ba domin washegari Alhamis Adda ta Dira ganinta ita kadai yasa sai da na tambayeta ina Amma sai ta harareni kafin tace"Daman kin damu da ita ne tunda ta tafi ko a waya baki taba gaisheta ba?
Sai na kasa magana sanin ban kyauta ba, Adda ta gyad'a kai kafin tace"Aisha ba saboda komai ta aikata haka ba sai Saboda Rayuwarki ta inganta Hasiya. Kila yanzu bazaki gane hakan ba sai nan gaba ammh ina miki Fatan ki gane da wuri kafin Lokaci ya kure miki."
Duk sai ta kashemin jiki zuwanta yasa ban kara gaddama ba saboda ta na da Zafi tace sai ta min dukan Tsiya ita ba irin Jari ba ne ballatana ta rika lallabani.
Dole kanwar naki na Tsife kaina Ramatu ta rakani aka yi min wankin kai Kunshi kuma wata makociyar Adda Fari tazo ta min tamin na salatif na kwana da shi wayewar garin juma'a kuma ta yi min baki a hannuna na zane.
Adda tazo min da Gumba wanda za'a sha da madara ban yi musu ba na karba da ta damamin na sha.
Habibu mijin Adda ya yi kokari shi ya bada abincin Sha'anin wanda suka siya kuma sai Adda tace su bar min na gara tunda bazasu kaini haka ba.
Na dauka na gama tara mutane Lokacin aurena ashe na manta cewa wasu ko don tafiya da abunda ya faru suna zuwa.

Duk yadda na so kada na nuna Ina Farinciki da wannan auren su Adda Fati ba su barni ba sai da suka saka na yi wanka na shirya Ramatu ta min kwalliya.
Abun mamaki duka matan Baba Tanko da na Baba Saminu sun zo su gambo da wuri suka iso saboda kada a yi wani sin din basa wajen.
Goggon kona sai da yammah ta zo ammh wasu cikin ya'yanta sun zo da Rana.
Bata ji kunyar yima Adda Mganar Amma ta raba zumunci da su ba ita kuma Adda ta same su ta yi musu wankin babban bargo ta rufe da fad'in"Aisha ta bi ku gajiya ta yi ta kyaleku. kuma har a wajen Allah ba ta da wani laifi ku ne kuka ki ta ku ka k'i ya'yanta duk da su d'in Dolen ku ne. Yau an wayi gari Zumunci ya lalace d'a sai wanda na Haifa ya'yan dan'uwa ba D'a na ba ne, Kwata kwata baku kula da su ba a banzace ku ka bar su suna wahala saboda canfin ku na karya da ba ku da tabbaci."
Kasa mgana suka yi tunda ba su da gaskiya barin ma Goggon kona daman ance gaskiya ai sunanta gaskiya kuma daga kinta sai bata.
Kunya suka ji? Ko kuwa daman suna son ganin abunda zai faru ne yasa suka tsaya har yamma.
Na saka kaya kala uku a ranar ina cirewa gabda mangariba Adda Rukayya ta saka na sake wanka na saka less din da Farin Hijabi naji ana ta mganar ya kamata azo a tafi dani kada dare ya yi.
Nayi ta kallon al'amarin ina mamakin ko motoci goma aka kawo sai sun cika wasu ba su samu waje ba.
Saboda duka matan gidanmu da muka taso sun zo har da makota kuma suma sun ce da su za'a je kai Amarya.
Har sai da nayi sallar mangariba ban ji wata mgana ba ina kan sallaya ina nirmishi ni kad'ai mirmishin da yafi kuka ciwo a cikin raina ina Tunanin kamar na Salisu za'ayi kila ma kafin na kai ga tarewan komai zai iya faruwa.
Wayar Sadiq Adda Fati ta yi ta kira a kashe hankalinsu gabadaya sai da ya tashi sun rasa mafita Kuma bai kamata su je su kaini batare da susan wani Hali Shi mijin nawa ya ke ciki ba.
Mutane nata zaman jira shuru ga Duhu ya shiga Adda Rukayyace ta fita ta na ce musu kowa ya tafi gida Amarya angonta yace zai zo ya Dauketa da kansa sai gwiwa duk ya yi sanyi.
Su gambo dole suka tafi ba'a samu an karisa ganin abunda zai wakana ba matan gidanmu ma ba'a son rai suka tafi ba Ammh sunce daga baya zasu kaimin ziyara.
Zuwa karfe 8 na dare kowa ya watse daga su Adda sai Inna Talatu sai Ramatu har Goggon kona ta kwashi Tsufanta ta kara gaba.
Ni ina ciki ban fito su kuma suna falo suna fama da tararradi.

Ramatu ta kalli Adda Fati da ta ke ta faman kiran wayar Sadiq a kashe cikin mutuwar jiki tace"Har yanzu baki same shi ba?
Adda Fati tace"Wayarsa a kashe."
Adda Ta numfasa kafin tace"Ina sha Allahu lafiya lau. Ku yi tunani ba ku da ko Lambar abokinsa ne?
Sai a Lokacin Adda Fati ta tuna da lambar Tahir da Sauri ta mike ta na fad'in"Na tuna ina da lambar wannan abokin na shi."
Da sauri kowa ya washe baki Inna Talatu tace"Maza ki kirashi."
Da Sauri ko Adda fati ta kira lambar Tahir ta shiga har ta kusa katsewa sannan ya daga kiran.

******
Chapter 7 · 0% Book details