Sashe 25
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Suna shigowa Haraban gidan Abba ya kira wayar Umma yace su fito su tarbi baki ga su nan a haraban gida.
Umma ta shaida ma Mama da Sauram yaran suka Dumguma gabadaya.
Har da Innani da ta mike ta na Faman Dogara sandarta.
Salima ta kalleta lokaci d'aya ta na fad'in"Innani ke kuma ina zaki je kina tafiya Dakyar?
Innani ta kalleta kafin tace"Gidan uwarki zani. Ka ji min yarinya mara kunya? Ina ce baki nan na Sulaimanu ne ba bakin Suwaiba ba ko?
Umma ce ta katse fad'an Innani da Riko Sandarta ta na Fadin"Kyaleta Innani muje ke ya kamata Daman ki Fara musu maraba."
Innani na jin haka sai ta washe baki ta na fad'in"Yauwa salamatu yar albarka."
Sauran gaba su ka yi Mama daman ta na jin Innani ta fara ambaton sunanta ta bata rai ta na Hararan Salima domin tasan ita ta ja mata zagi wajen Innani da daman bata taba fari a wajen wannan Tsohuwar ba.
Umma ce ta tsaya ta na taimaka ma Innani suka fito tare.
Duk suna Haraban gidan Abba ne sun Sarke Hannu da Alhaji Jibril suna gaisawa kowanne fuskarsa cikin Annuri da Farimciki.
Dukkansu kuma suna Sanye da Manyan riguna kamar wad'anda za su je wani waje Daurin aure.
Su Mama kuma Hajiya Murjanatu suka nufa cikin Sakin fuska suna yi mata maraba da zuwa.
Siyama ne da Sultana suka tarbi su Fathihatu da Zahra'u Salima kuma na gefe ta na faman Danna wayarta sai dai ta na wani kare ma mutane kallo cikin irin takun ta.
Mubarak na gefe shima ganin ba shi da aboki namiji a wajen.
Sanye yake cikin shigar shadda Fara dinkin zamani kafarsa cikin bakin Takalmi na Fata mai kyau.
Kansa kuma cikin Hula kube kalan aikin shaddar jikinsa mai baki baki.
Muryan Innani ne ta karad'e wajen da Muryanta sanda suke karisowa ita da Umma.
Cikin muryanta na Tsufa tace"To gani na iso ina shi abokin Sulaimanun ina so na ganshi da idona."
Jin haka yasa aka bata Hanya Abba ya kalli Alhaji Jibril ya na yar Dariya yace"Ga mahaifiyata da na ke yawan baka Labarinta."
Innani ga Alhaji Jibril abokin kasuwancina ne shekaru biyar da suka gabata."
Innani ta washe baki ta na Fad'in"Ma sha Allah sannu Jibrulu sannu kaji? Ai sulaimanu akwai kirki ga mutumci da son jan mutane ajiki sannun ku da zuwa Allah ya yi muku albarka."
Alhaji jibril cikin Ladabi ya ke amsawa da Ameen Ameem kafin ya Zube a kasa ya na gaida Innani.
Ita kuma sai amsawa ta ke yi cikin waahe baki taji dad'in ganin yadda ya bata girma.
Alhaji jibril ya gabatar da iyalansa ga Abba shima Abba ya gabatar da na shi iyalan a wajen Alhaji Jibril.
Sai faman saka albarka ya ke yi Alhaji Jibril ya Dafa kafad'ar Mubarak da ke gefensa cikin mirmishi yace"Ga babban yaro na Mubarak."
Abba ya ba ma Mubarak hannu suka yi musaba yana tambayansa karatu yace ai ya gama yanzu aiki ya ke yi.
Innani ce taga ana ta tsayuwa ga shi ta gaji sai ta yamutsa fuska kafin tace"Wai nikam a tsaye zamu yi zumuncin? Haba ni na gaji tunda ba Dije soja sunana ba."
Gabadaya sai da aka yi Dariya Alhaji Jibril da sauri ya rike Sandar Hannun Innani ya na fad'in"Mu je Innani na yi miki jagora."
Innani ta washe baki ta na fadin"Allah ya yi albarka kaji Allah ya raya zuru'a."
Ya na ta amswa da Ameen Ameen.
Umma da Mama suna tare da Hajiya Murjanatu su ke bin bayan su Abba zuwa Bangaran Innani.
Su Surayya kuma suna tare da Fathihatu wacce ke Dauke da Danta karami namiji sai Siyama da su Sultana da ke tare da Zahra da Fatima Batul.
Kamal kuma daman ya na tare da Babansa ne.
Salima ce ke baya ta na tafe ta na taku d'aya bayan d'aya wayace a hannunta hankalinta ma baya kan in da take takawa.
Har sai da ta kusa cin Tuntube ta fad'i Mubarak da ke bayanta kamar ya na kirga takunta ya yi gaggawan tareta ta hannun hagu shi ya taimaketa daga Fad'uwa.
Ido cikin ido suka kalli juna kafin Salima ta yi saurin janyen kallonta Daga gareshi ta na fad'in"Thanks."
Kai ya gyad'a mata batare da ya yi mgana ba.
Sai dai ya nuna mata hanya da hannunsa ta fara yin gaba sannan shi yabi bayanta.
Ya na tafe ya na kallonta ya na mirmishi daga ganinta a ransa yace ta na da aji da isa.
Afalon Innani a ka yada Zango Abba da Alhaji Jibril duk suna zaune a kasan Cafet ne gaban innani haka su Umma da Sauran yaran
Salima ce ta zauna kan kujera ta na mai Dora kafa d'aya kan d'aya.
Hankalinta na kan wayar hannunta.
Gaisawa aka sake yi cikin mutumtata juna.
Da kuma tambayan Hanya da Mutanen gida.
Ruwa Umma ta ce su siyama su fara kawowa tare da Lemu saboda su fara sha su jika makoshi.
Siyama da Sultana suka rika wannan Zirga zirgan salima na zaune bata ta shi ba, daman ita yar iyayi ce bata son aiki sosai sai ya zama Dole.
Mubarak na gefe ya na kallon Salima ammh cikin takun da ba ta sani ba
Haka kurum ya ke jin yarinyar zata yi daidai da Zabinsa sannan da Ra'ayinsa.
Sultana ta kawo masa Ruwa mai sanyi har gabansa ya karb'a ya na fad'in"Thanks."
Mirmishi ta yi masa shima sai ya maida mata da martanin mirmishin nata.
Bayan sun sha ruwa sun natsa Abba ya duba agogon hannunsa yaa na fad'in Lolacin sallah ya yi su fara gabatar sallah tukunnah.