← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 75

Sashe 56

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Isha'i. Ya dawo ya iskeni ina ta kuka wurjajan,Sai ya Rud'e Hankalinsa ya tashi daman ina zaune saman gado ne ina masa kukan Tab'ara. Sai ya tarairayoni a jikinsa ya na Tambayata me ya faru? Cikin Jan hanci nace"Ba kai ba ne." Da Sauri yace"Ni kuma Hasiya? me na yi? Cikin Tab'ara nace"To kace zamu fita kuma na Shirya ammh ka yi barcin ka ka kyaleni sannan kuma ma..." Cikin Sanyin murya yace"Kuma me? Ina kallonsa nace"Kuma kana da Damuwa ammh baka fad'amin ba? Cikin bude ido yace"Kamar ya? Wata damuwar? Da Sauri na tashi daga jikinsa ina fadin"Eh mana duk ka sauya sai ka yi ta abu kamar mara lafiya." Shuru ya yi ya kasa mgana ni kuma ganin haka yasa na koma jikinsa na Lafe ina fad'in"Don Allah in wani abu ne ka fad'amin? Saboda ni ne ko? Rumgumeni ya yi sosai a cikin Jikinsa kafin yace"A'a na gayamiki gajiyan zirga zirga ne fa." Na kasa yarda da mganarsa ammh kuma bazan iya masa gaddama ba. Lallashina ya dinga yi da Tattausan kalaman bakinsa har sai da na Dawo ina Dariya. Kallona ya yi kafin yace"Mun fasa fita yau sai Ranar monday kin ji ko? Sai na gyad'a masa kai. Ranar dai mun yi abunda bamu taba yi ba shine kwana a muhalli daya sannan a waje d'aya acikin Rufi daya. Muna manne da juna yanayin da na so ya Dauwama har abada. Ranar asabar da Lahadi bai fita ko'ina ba sai masallaci kawai ya ke zuwa ya na Tare dani muna shan soyayyarmu. Cikin kwanakin biyun nan na saka su cikin Ranaku ma su daraja a cikin ranakun Aurena da Assadiq. Shi kamshi haka din ne a wajensa, har ga Allah yaso ya sauya Tunani ammh acikin kwana Biyun nan ya kara Tabbatar ma kansa ya na Bukatar Hasiya, itama Hasiya ta na Bukatarsa. Shiyasa kawai ya Tsaida Tunaninsa waje daya. A wayarsa ya shiga Goggle ya yi duk Binciken da zai yi, washegari Litini yace na Shirya da wuri zamu fita. Har ga Allah na zata gidan Adda Fati zai kaini, tunda ba mu saba fita da Safe haka ba. Hijabina mai ruwan kasa na Sanya har kasa, shi kuma ya na sanye da wani yadi mai milk dinkin mazan zamani da jakarsa rataye a gefen kafad'arsa Tunda yace zai shiga cikin makaranta. Mamaki ya kamani sanda naga mun zo wani asibit acikin sabon gari. Ni dai ina ta binsa da ido, domin da na tambayesa me muka zo yi a asibiti kai tsaye yace min"Gwajin jini za'a yi mana ni da ke." Sai na kasa gane ma'anar mganarsa zan kara mgana sai ya min alamun da na yi shuru. Asibitin ba wata babba bace daga gani dai irin asibitocin kudin nan ne. Likitan ya nema aka masa iso Office dinsa, ni kuma ya bar ni a waje tare da Nurses yace na jirasa. Ya fi tsawon mintina arba'in da Shiga sannan sai ga shi sun fito tare da Likitan wani d'an gajere. Ya kalleni sannan ya kalli Assadiq ya na fadin"Is she d one? Sai ya gyad'a masa kai, sai naga ya tako mgana ya na fadin"Sannu Madam" Na amsa masa cikin yake, baya ya juya yana yi ma wata Nurse mgana cikin Harshen Turanci. Sannan ya kalleni ya na fadin"Madam ka bi ta" Sai yaga na yi wani fiki fiki da ido ina kallon Assadiq shi kuma ganin haka yasa da Sauri ya iso kusa dani ya na fadin"Kada ki daga Hankalin ki jininki kawai zasu d'iba domin gwaji" Sai ya nuna min damtsen hannunsa inda aka Danne da Auduga ina fadin"Nima kinga har sun dib'i nawa." Jin haka da kuma ganin da na yi shima ya na hannunsa sai naji Hankalina ya kwanta. Sannan a karkashin raina ina da yakini tare da Tabbacin Assadiq bazai taba cutar dani ba. Ya na rike da Hannuna har gaban Nurse din sannan ya sakeni lokaci Daya ya na fadin"Zan jira ki, kin ji ko? Gyada masa kai na yi, Nurse din ta yi gaba ta na fadin na biyo ta. Sanin da na yi Assadiq bazai taba cutar dani ba yasa na saki jiki na sannan na Natsar da zuciyata waje daya.
Chapter 56 · 0% Book details