← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 75

Sashe 26

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Umma ta ja Hajiya Murjanatu bangaranta suka yi sallah bayan Abba da Alhaji jibril tare da Mubarak da kamal sun fita zuwa masallaci.
Siyama da Sultana su ka ja Zahara'u da Fatima batul duk da ba sa'ar su ba ce sai dai salima in ma bata girme mata ba ammh halin Salima sai ita shiyasa suka ja Zahra'un a jiki, a nan Shashen Innani suka yi na su sallar.
Su Anty surayya kuma suna bangaran Mama tare da Fathihatu.
Sai da Su Abba suka dawo daga masallaci sannan aka zauna zaman cin abinci.
Sultana da Siyama har da Salima suka Shimfid'a babbar Darduma a tsakiyar Falon Innani aka jera komai a samanta
Sannan suka zagayeta kamar cin abincin Larabawa.
Innani ce kusa da Abba da Alhaji Jibril sai Mubarak da kamal sai Umma da Mama da Hajiya Murjanatu.
Sai su Anty surayya sannan su Siyama ne a karshe.
Salima ce chan kusa da Innani ta Hannun Hagu, suna kuma Facing din juna ita da Mubarak duk sanda kuma ta Dago kanta sai sun had'a ido.
Shiyasa sai ta kasa sakewa ta ci abinci sosai Sarver ur self ne kowa da kanshi ya sama ma kansa abunda ya ke so
Innani ce Alhaji Jbiril ya zuba mata ta na ta saka masa albarka.
Ba innani kad'ai ba batta su Abba sun ji dadin ganin irin yadda Alhaji Jibril ke kula da Innani tun zuwan su.
Abba ya kallesa ya na fadin"Nagode Alhaji Jibril."
Sai kawai ya kad'a kai kafin yace"Haba bakomai mahaifiyata ta rasu da jimawa ina kallon Innani kamar uwa ce a wajena."
Sai Abba ya jinjina kai cikin kara ganin kirki da Dattakon Alhaji Jibril.
Suna cin abinci sama sama suna d'an Taba Hira har suka gama.
Wannan karon manyan suka kwashe koma zuwa bangaran Umma.
Suka kuma ja Fathihatu tare da su, Siyama da Sultana suka gyara wajen sannan suka ce Zahra'u ta zo su tafi, sai suka koma Shashen Mama suka zauna.
Salima kuma Dakinsu ta shige abunta bata ko zauna  a falon ba, inda su Siyama ke zaune suna taba hira ba.
Mubarak kad'ai aka bari da su Abba afalon sai su Umma da ke chan gefe suna ta hira da Hajiya Murjanatu.
Innani gyangad'i ta fara ta na zaune sai Alhaji Jibril yace ko zata shiga ciki ne ta kwanta.
Innani na jin haka sai tace bakomai ba barci take yi ba kuma da gasken barci take ji ammh kada ta tashi a yi wata mgana bata sani ba ne.
Kamar ko ta sani taji Alhaji Jibril na Tambayan Abba cewa bai ga Abubakar sadiq ba ko baya nan ne?
Kafin ma Abba ya ba da amsa Innani ta yi zaraf tace"Magajin gida ai ya na chan wani gari ne ma Salamatu?
Ta fad'a ta na kallon Umma wacce sai alokacin ma taji mganar.
Cikin alamun tambaya tace"Waye Innani?
Innani tace"Wai magajin gida ya ke tamnbaya nace ya ma wani gari ne?
Umma ta yi mirmishi kafin tace"Ya na chan Zariya ya na Hidimar kasa Innani."
Innani ta washe baki ta na fadin"An yi ko haka ya na chan zariya abun shi gidan sai ya yi ba dad'i da bayanan ka san shi ai na Innani ne in dai yana gidan ne to bai da wata uwa da ta wuceni nan ne wajen zamansa barci kawai ke kaisa bangaransa."
Alhaji Jibril yace"Allah Sarki."
A ransa ya na mamaki kamar Alhaji Sulaiman ace dansa ma ba'a waje ya yi karatu ba? Kuma wai ya na zariya ya na Hidimar kasa sai abun ya yi masa wani iri.
Sai dai bai yi mgana ba kamar an tambayi innani ta tsinke da labarin cewa Magajin gida zai auri Sultana an kusa bikin ma.
Abba ya kalleta cikin mamaki ba Halin ya yi mgana.
Alhaji Jibril kuma da mamaki ya kalli Abba na neman karin bayani.
Sai Abba ya gyara zama ya na fad'in"Sultana diyar kanwata ce da ta rasu nan ta ke wajena ita ce mu ke so mu had'a auran su da Magajin gida in sha Allahu."
Alhaji Jibril ya had'iye wani miyau mai daci ya kasa mgana ita ko Innani fad'i take yi wata yarinya nan mai kokari da suke ta kai da kawo ita da yar uwar ta? Wata mara kaurin jiki doguwa haka ita adole sai Alhaji Jibril ya ganeta.
Sai ya yi mata yake ya na fadin"Ma sha Allah wannan tunani ne mai kyau Alhaji Allah yasa muna raye."
Innani da karfi tace"In sha Allahu ma muna raye za'ayi auran magajin gida da Sulsana."
Alhaji Jibril ya Dukar da kai ya kasa mgana Umma ce ta juya ta na ma Hajiya Murjanatu bayanin had'in Auran Sultana da Magajin gida da ke chan zariya ya na Hidimar kasa ammh ya kusa gamawa ya Dawo gida.
Abba kuma ya na ta ma Alhaji Jibril magana sau yaga kamar ya d'an Shiga damuwa.
Cikin mamaki yace"Alhaji nace ko lafiya?
Alhaji Jibril ya sauke Numfashi cikin Damuwar da ta bayanna har saman fuskarsa.
Cikin wani irin sauti yace"Shikenan kawai Alhaji."
Abba yace"Shikenan me ya faru? Ka fad'amin mana?
Alhaji Jibril ya kara sauke Numfashi kafin yace"Alhaji mganar bata da amfani mu bar ta kawai."
Shi kuma Abba ya Dage sai ya gayamasa ko wata mgana ce.
Jin ja'in jansu yasa hankalin su Umma ya dawo kansu.
Har da Innani wacce tace"Fad'i damuaarka Jibrilu kamar yadda ka Daukeni uwa haka nima na Dauke ka d'a kamar Sulaimanu."
Alhaji Jirbril ya kalli Matarsa Hajiya Murjanatu itama sai ta kallesa cikin mamaki Saboda ta kasa gane ma'anar kallon na shi.
Sai kuma ya koma ya sunkuyar da kansa kafin yace"Had'uwar kasuwanci ne ya had'amu da Alhaji Sulaiman ammh jinsa na ke yi kamar Dan'uwa na jini Shiyasa na yi Tunanin na kara karfafa alaqar mu ta hanya aurattaya a tsakanin ya'yan mu."
Innani ta washe baki ta na fadin"To miye abun damuwa? Ga mu nan da yaran mata a gida sai shi dan wajen naka ya duba ga Salima da Siyama ni da zai ji shawara sai ya zabi Siyama Domin tafi yayar Hankali da natsuwa kunga shikenan ma sai a had'a bikin su rana d'aya da na magajin gida da Sulsana."
Kallonta kowa ya yi ya na mamakin ko gama mgana Alhaji Jibril bai yi ba har Innani ta yanke mgana.
Shi kuma Mubarak da yaji komai har ransa yaji dadi daman kuma kila Rabon auran shi da Salima ne ya had'a Abba da Baba suka san juna.
Chapter 26 · 0% Book details