← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 75

Sashe 22

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

dauki Lokaci ba ko? Da Sauri nace masa In sha Allahu. Kad'a kai ya yi kafin yace"Ok." Sai da na tabbatar da ya fita sannan na Daka Tsalle. Sauri sauri na tsane shinkafar sannan na had'a miyar naje na yi wanka. Ina cikin salla ya dawo sai da na Idar sannan na saka kaya ko mai ban Tsaya shafawa ba. Ina fitowa daga ciki yace"ke nake jira kada dare ya yi na rasa abun hawa. Sannan garin kamar da Hadari." Ni kuma kai tsaye nace masa"Da wuya fa ayi ruwa kasan farkon damina." Bai ce min komai ba na shiga kitchen daman bayan na fito wanka na zo na Duba miyan naga ta yi sai na kashe gas din Daman tuni na wanke salat dina had'a masa na yi miyan daman nama na saka masa saboda yace baya son kifi ni kuma bazan saka masa abunda baya so ba. Ban dauka ba zai ci abincin da yawa ba sai naga kuma yaci ba laifi da ya tambayani ni bai ga na zubo nawa ba? Sai na ce masa ba yanzu zan ciba sai anjima. Ruwan gora na Dauko masa Tunda ya siyomin da lemun Fanta kanta d'aya kowanne. Kamar wasa sai iskan Hadari ya taso yana jin haka ya mike yace zai tafi sai me? Ba sai ga Ruwa ma su karfi ba dole ya dakata da Tafiya tun ya na zaton ruwa zai Dauke har ya Sare. Sallar isha'i ma shi ya jamu jam'i Saboda Ruwa bai samu fita ba. Kamar ranar da farko ni yace na kwana aciki shi kuma zai kwanta afalo.
Chapter 22 · 0% Book details