← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 75

Sashe 24

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yau asabar din karshen mako ne. Gidan Alhaji Sulaiman Shinkafi kamar yau d'in sun ta shi da Hidima ne sosai saboda za su yi baki daga Jahar kaduna.
Abokin kasuwancin Abba ne zai zo tare da iyalansa gabadaya.
Shima a gidan Alhaji Sulaiman su Umma sun yi ma yaran na su waya, suma duk za su zo wad'anda ke cikin garin kenan na nesa kuma ban da su.
Tun safe Umma da Mama ke kitchen a shaahen Umma suna ta dorawa suna Saukewa, tare da taimakon ya'yan su Salima da siyama sai Sultana.
Abinci kala kala su ka yi musu sai kuma lemuka kayan Snkas kuma Anty Surayya tace zata zo da shi.
Anty Sa'in kuma tace zata yo pepe Chicken ta zo da shi.
Ita kuma Sajida tace za ta yi Dambun Nama itama ta zo da shi.
Tun misalin karfe takwas da wani abu na Safe Abba yace bakin sun taso suna kan hanya.
Shiyasa suka fara aikin da wuri kada Bakin su iso kuma ba su gama ba.
Bayan sun gama girkin daman Tuwon Shinkafa ne miyar agushi suka yi musu sai Farar shinkafa da miyar Naman rago.
Sai jallof d'in Couscous da ta ji hanta da kayan lambu.
Sai lemun kankana, sai kunin gyada da Kunin aya.
Da farko Abba yace bakin a shashen Umma za'a sauke su ita kuma Umma taga ga bangaran Innani bai kamata a sauki baki a na ta Shiyar ba.
Sai tace a kai komai bangaran Innani a jera a nan bakin za su sauka.
Abba bai ce komai ba Mama ce ma taso ta yi mgana sai kuma ta fasa.
Siyama da Sultana ne ma su kai abincin zuwa Shashen Innani da daman Tun safe Sultana ta gyara Bangaran sai tashin kamshin Turare ya ke na daki.
Innani na zaune a kasan cafet a cikin Falonta sai faman kankaran Rake ta ke yi da wata karamar wuka, ta na sawa a baki tana mamula da hakoranta na roba.
Ta ci uban Dauri ta Rufe kanta Ruf har kunnuwanta ga gilashinta da ya cika rabin Fuskarta.
Atamfarta mai kyau ce super ce mai tsada, dinkin Riga da zani na su na Tsoffi.
Ta na jin sanda suka shigo ta dago ta na kallon su ba'a a falon suka jera komai ba ciki suka shiga da shi.
Innani ta gaji da shige da ficen su ta dago ta na kallonsu cikin takaici kafin tace"Nace lafiya ku kuma ku ke ta min Faman sintiri a shashena da Uban Safiyan nan?
Siyama ce tace"Kai Innani Abinci fa muke shigowa da shi."
Innani ta ce"Abinci kuma? Na waye?
Siyama na Tura baki tace"Na baki ne."
Innani tace"Bak'i kuma? In ji uban wa ya ce a kawo abinci nan?
Sultana ce da ke bakin kofa tace"Innani Umma tace mu kawo nan."
Sai Innani ta yi shuru kafin tace"Oho na zata kinibibin Suwaiba ne. Bakin sun iso ne?
Sulatana ce ta tsaya ba ta amsa ba Siyama ficewa ta yi ta na kunkuni.
Innani ta rakata da fad'in"Uwarki kika yi ma kunkuni ja'ira."
Ita dai Sultana ta fice ta bar Innani na ta masifa ta na faman cewa Sulaimanu ya auro dangin Jaraba sun zo suna neman hanata zaman lafiya ita da gidan d'anta.
Daman in dai wad'anan kalaman ne kusan duk wamda ke gidan nan ya Haddacesu daga bakin Innani.
Kowacce bangaransu ta wuce domin su yi wanka su shirya.
Salima daman ita suka bari zata gyara kitchen din Umma.
Masu aikin su daman basa zuwa Weekend saboda suna gida sai ranakun Litini zuwa jumma'a da basa gida.
Abba kuma ya fita ammh yace zai Dawo ba jimawa zai yi ba.
Ko kafin sha biyun rana ta yi kowa ya shirya Umma wani less dinta ta saka mai Tsada dinkin Doguwar riga ita kuma Mama sai ta saka Shadda ita mai Dinkin Doguwar riga.
Siyama kuma da Sultana shigar Maryam Epytian Abaya su ka yi.https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V

kuma duka iri d'aya suka saka kalan pick ma su kyau da Tsari sun kuma yane kansu da mayafin Abaya.
Ita kuma Salima daman iyayen iyayine wani material ta saka Dinkin Riga da sikat ne sun mata kyau sosai kamar wata black American
Kuma daman Salima ta na da kyau sosai suna kuma D'iban kama daman da Sadiq.
Zuwa kuma lokacin su Surayya duk sun iso suma tare da ya'yan su suma sun yi shigar alfarma kana ganinsu kasan ya'yam manya ne sannan kuma suna auran manyan mutane ma su Rufin asiri.
Gabadayansu Bangaran Innani suka yada Zango tunda nan bakin za su fara sauka, Innani sai washe baki ta ke yi ballatana kowacce da yar ledanta na Innani ka na bata zata fara washe baki ta na zuba mu su albarka sannan har taja ya'yanka a jikinta.
In kuma baka zo ka bata komai ba ta Dinga Hararanka kenan, in kaci sa'a ka tafi salin alim ba'a bika da gori ba.
Sadiya Kaza guda ta soya ma Innani suyan da ta ke so, Innani ta saka mata albarka kamar me.
Sa'ima Miya ta yi mata mai Naman sa, Sai ga Innani na fad'in ya'yan Suwaiba duka ya'yan albarka ne ya'yan mutumci.
Siyama ta kalleta ta na mamaki, Dazu da Safe ta gama cewa ya'yan Suwaiba ya'yan Jaraba ne ammh shine Saboda abun duniya har ta sauya mganarta.
Ai Innani in dai kana son Siye bakinta to toshe shi da abun duniya shikenan sai ka samu lafiya.
Sha biyu da rabi da wani abu baki suka iso tare da Abba suka iso daman sanda Alhaji Jibril ya kirasa ya fito daga inda yaje zuwa gida shine kawai yace Direba ya tsaya a hanya su taho tare da su zai fi da kwatance.
Chapter 24 · 0% Book details