← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 75

Sashe 37

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakam ta yi ta yi kamar bata ji ba Saboda lamarin gabadaya ya fara bata Haushi me ake jira? Wannan ai sai Allah ya yi fushi da su sun ki cika Umarninsa na had'a sunnar ma'aiki.
Sadiq baisan da mganar Saddiqa na zata samu Abba da mganar ba. Ballatana Maganar Innani abunda yasa bai tanka ba yasan ba wanda ya isa ya yanke masa wani abu acikin Rayuwarsa batare da cewarsa ba.
Ganin da ya yi har su Umma sun fara Zargin wani abu na Damunsa sai ya yanke shawaran tafiya Daura ya kwana Biyu wajen Tahir daman kuma zai je ya Duba Hajja tun ciwon da ta yi kwanaki bai je ya gaisheta ba.
Sai ya fara shirin tafiya batare da ya fad'a ma kowa ba, Da Tahir kad'ai suka yi mgana duk da bai saka masa ranar da zai zo ba.
Saddiqa ta dad'e bata zo gusai ba shiyasa zata d'an kwana Biyu a gida, Maganar da tace zata yi ma Abba basu samu zama ba sai dai sun yi magana da Surayya tace ta bari ta shigo gidan sai su yi mgana su san me za su fad'ama Abba in sun je gabansa.
Shiyasa sai ta dakata da yi ma Abba mganar Ita kuma Innani ta Samu abunda ta ke so ta dinga mganar Daman ta fad'a ammh aka ki jin mganarta ga shi nan Magajin gida zai lalace a tsaye.
Ita surayya ita ta kira sauran yan'uwan duk ta sanar da su, su daman sun ce Sultana su ke ji ganin ta yi kankanta da yawa ammh tunda abun ya zama haka sai ayi auran sai su reni juna a tare.
Ana gobe Sadiq zai je Daura Daddare ya kira wayar Mama yace ta turo masa Siyama yanzu zuwa bangaransa.
Siyama na jin haka ta ruga da gudu ta san kiran Yaya Sadiq samu ne yawanci.
Tana zuwa yace taje ta kira masa Sultana su zo tare, Da sauri ta je Shashen Umma ta kira Sultana bakinta washe Allah yasa wayar ce aka siya musu.
Tare suka dawo ya na zaune acikin Falonsa ga kwalayen wayoyi nan a gabansa na Samsumg guda Biyu.
Suna shigowa Siyama ta kyalla ido taga wayoyi sai ta washe baki jikinta na rawa da bakinta.
Dukawa suka yi a kasan cafet suka gaisheshi ya amsa kai tsaye kafin ya kallesu gabad'ayan su.
Cikin kaushin murya yace"Kun san meyasa na kira ku?
A tare suka girgiza kai, kwalin wayar ya Dauka guda d'aya ya mikama Sultana ta saka Hannu ta karba itama Siyama ya bata nata ta karb'a bakinta na rawa tace"Namu ne Yaya Sadiq?
Kai ya gyad'a mata kafin yace"Naku ne Abba yace a siya muku."
Siyama ta saka Ihu ta Rumgume wayar ta na fad'in"Thank u Yaya Sadiq mungode sosai."
Kai ya jinjina kafin yace"Ku yi ma Abba addu'an Gamawa da duniya lafiya."
A tare suka ce"Allah yasa Abba ya gama da duniya lafiya."
Ya amsa da Ameen.
Kafin ya cigaba da fadin"kowacce akwai layi acikin wayarta. Ba an siya muku wannan wayar ba ne domin shashanci saboda ta taimake ku akan karatun ku ne kun ji ko? A tare suka toh za su kiyaye.
Kai Tsaye ya sallame su suka mike suna Murna suka fice ya bisu da kallo.
Ranar gidan nan ya cika da Murnan Siyama karad'inta kad'ai ake ji.
Bayan sun yi chaji haka kiran sauran yan'uwansu ta na fadin Siyama ce sun yi waya ita da Sultana.
Salima na kallonta ta tabe baki ta na fadin"Siyama gaskiya ke yar kauye ce ji fa abunda ki ke yi?
Siyama ta tura baki ta na fadin"Eh d'in naji."
Sultana kuma ta na chaza wayarta abu d'aya ta fara yi Lambar Sadiq ta fara sakawa daman kuma ta Hadaceta a kanta, Kuma da ya ke an saka musu 2k katin waya shi ta fara kira.
Shi dai yaga bakuwar lamba ta kirasa ya na Dauka kawai yaji Muryan Sultana ta na fadin"Yaya Sadiq ni ce Sultana ce."
Cikin mamaki yace"Sultana.."?
Mirmishi ta yi masa ta cikin wayar kafin tace"Eh ka yi Saving din lambata."
Sai ya jinjinamata kai kamar ta na ganinsa, sannan suka yanke kiran a tare.
Mamaki ya cika shi sai dai kuma ya share mamakin nasa ya yi Saving din lambar nata kamar yadda ta bukata da sunanta wato SULTANA.
Sai da asuba suna hanyar dawowa masallaci ya fad'a ma Abba zai je Daura.
Abba yace ga Direba sai ya kaisa, Sadiq yace baya bukata saboda ba yau zai dawo ba sai ya kwana Biyu.
Abba ba shi da yarda zai yi Tunda yasan Halin Abunda ya Haifa.
Sai da ya gama shirinsa ya fito da karamar Jakarsa ta baya sannan ya shiga ya yi ma Umma sallama itama sai ta rika masa Fad'an meyasa bai gayamata da wuri ba.
Kansa na kasa yace"Umma ki yi hakuri."
Umma ta kallesa kafin ta kira sunansa"Abubakar.."
Cikin mamaki Sadiq ya Dago ya na kallon Umma kafin yace"Na'am".
Cikin mamaki saboda bai taba jin Umma ta kira sunansa kai tsaye haka ba, ko ba ta ce Auta ba sai dai tace Saddiqu.
Cikin idanuwansa ta kallesa tace"Me ke damunka ne kwana biyu nan?
Cikin Sauri yace"Umma me ki ka gani?
Hararansa ta yi kafin tace"Bansani ba! Ji yarda duk ka wani susuce ina maka mgana kana ce min me na gani."
Sai ya yi shuru kawai ya sunkuyar da kansa na wani Lokaci kafin ya Dago ya na fadin"Umma ni fa ba abunda ke damuna"
Umma ta kura masa ido shi kuma sai ya kauce ma kallonta saboda kada ta Fahimci ba shi da gaskiya daga cikin kwayan idanuwansa.
Umma sai kawai ta kad'a kai bata kara mgana ba.
Bata da komai da zata ba shi ya kai ma Kakar Tahir sai cikin Atamfofin da Saddiqa ta zo mata da shi ta dauko guda daya sai ta hado mata da sabon Hijabin cikin wad'anda ta dinka ma Sultana sai turaren wuta na Rushi da na Tsinke, har da na fesawa.
Ta kawo ma Sadiq tace ya kai ma Hajja kakar Tahir tunda shi tafiyarsa da zuwansa ba ma wanda ya isa ya sani
Kansa na kasa yace"Ki yi hakuri Umma."
Bata kara mgana ba ta koma ta zauna ta na latsa wayarta sai da ya mike yace"Umma sai na dawo"
Kai Tsaye tace"Allah ya tsare ka gaishe su."
Har ya fice ta na kallonsa Idanuwan Umma ya ciko da kwallah a fili ta Furta"Me ke damun Auta na ne?
Bata da wannan amsar ammh in dai maganar Innani gaskiya ne to zata ba da goyon bayan auran nan yanzu saboda ya samu natsuwa sannan kowa ma ya Huta.

Bangaren Mama yaje itama ya yi mata sallama itama sai da ta yi masa Korafin tafiya ba sanarwa haka Sadiq? Itama Hakuri ya bata, ta ce bakomai itama ba ta da abunda zata ba shi shiyasa ta Dauko masa Dan kunne da Sarka da abun Hannu sai Sabulun wanka mai kamshi ta had'a masa ta ce ya kai ma Kakar Tahir, Saboda Itama Hajja na da kokari Tahir baya zuwa hannu Rabbana abubuwanan na Mutanen chan duk ta na ba shi yazo mu su da shi.
Bangaren Innani ne karshen shiga chan ya iske Saddiqa suna Hira.
Saddiqa kam sai da tace"Kai kam Sadiq baka da Dabi'a. In zaka yi tafiya ba sanarwa ba kyau fa irin wannan."
Kallonta kawai ya yi bai yi mgana ba Innani kuma sai kawai ta mike tace bari ta shirya su tafi tare itama taje ta gaida Kakar Attahirun.
Sadiq ya kalleta a karkace kafin yace"Ki je ina? Innani ba inda zan je da ke Wlh."
Innani ta saki baki ta na kallonsa kafin tace"Magajin gida..!"
Kai ya jinjina kafin ya juya ya na fad'in"Sai na dawo."
Sai kawai Innani ta saka kuka ta na fadin"Shikenan ai Allah ya tsare ni dai kace Kakar Attahiru ta aikomin da aya ina jin dadinta."
Dariya ta kusa kamashi sai da ya fita sannan ya yi dariyansa.
Kai Innani ke baki ba hakori a  baki ammh kina ba da sallahun a zo miki da wani abu.
Daman Abba ya sallamesa tun safen da kudi duk da yace masa ya na da kudi a hannunsa Abba ya kallesa kafin yace"Ko me ka zama a wannan Rayuwar Abubakar ni ne mahaifinka kuma har in koma ga Allah bazan daina maka Hidima ba."
Kalaman Abba suka toshe masa baki ya kasa yi masa gaddama.
Tasha yaje ya hau mota zuwa katsina daga chan ya samu na Daura.
Tahir na wajen taron siyasan d'an majalisan su da ya fara bi Sadiq ya kirasa yace masa ya na ina ne?
Kai tsaye yace ya na wajen Taron Siyasa.
Sadiq yace"To ya zaka yi dani? Ga ni a dakin Hajja."
Tahir yasan ba karya Sadiq ya ke yi ba sanin Halinsa.
Da sauri ya baro wajen ya na zuwa ko yaga Sadiq zaune dakin Hajja suna ta Hira shi kuma ya na shan Fura.
Tsaye ya yi rike da kugu kafin yace"Kai ammh banza ne ka kira kace yau zaka zo shine ya gagare ka.?
Kai Tsaye Sadiq yace"Bani da kudi ne a waya."
Da Sauri Tahir yace"Karya ka ke yi wlh."
Hajja ta dago ta na wurga masa maficin Hannunta Lokaci daya ta na fadin"Tafi chan mara tunani ya taso tundaga gari mai nisa saboda kai ammh kana kiransa makaryaci kai dai Dahiru Allah ya shirya ka."
Tahir ya bata rai ya na fadin"Hajja sunana Tahir. Tahir sunana."
Hajja tace"Nace Dahiru Dahiru ko zaka Tsireni ne?
Sai Tahir ya kasa mgana Sadiq kuma na shan Fura ya na Dariya.
Chapter 37 · 0% Book details